Skip to content

Chapter 89

Chapter 89

Nakasa Ba Kasawa Bace Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

dama agajiye suke, hakan yasa sukayi masa saida safe, koda Hayatuddeen ya buƙaci ganin Hamman nashi cewa dashi Dr.Adnan yayi yayi bacci sannan ba aso atasheshi, dole haka Hayatuddeen ya haƙura yabi Ahmad suka koma masauƙinsu. Koda Dr.Adnan ya koma cikin ɗakin nan ya iske Saifuddeen kamar yanda yafita ya barshi wato idanunsa alumshe tamkar wanda yake bacci, shi kuwa Saifuddeen ba bacci yake ba, yayi nisa ne akan tunanin Zaliha, kyakkyawar fuskarta ne keyi masa gizo acikin ƙwayan idanunsa da zuciyarshi, tuno da yanda ta rungumesa ta baya tana me jansa akan su gudu alokacin da yaran Dalla suka kusa cimmasa yasanya tsikar jikinsa tashi, lokaci guda ya tuno da taushin hannuwanta da kuma yanda daddaɗan ƙamshin turarenta ya zautar dashi, yanayin da yakejin kansa aciki, ya sanya shi jin tamkar alokacin abun ke faruwa, sake lumshe idanunsa yayi alokacin da ya tuna da yanda bakinta ke motsawa alokacin da take cewa yazo su gudu kada su cutar dashi, wani irin yawu ya haɗiya wanda tuntuni ya tsaya masa amaƙoshi, gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi wani iri, yayinda yakejin wani irin sassanyan yanayi shauƙin sha'awa na musamman suka rufeshi dangane da ita. "Saifuddeen!". Dr Adnan yaƙira sunanshi yana me kamo hannunshi, tayanda zaiji ya buɗe ido, jin sauƙan hannu akan nasa hannun yasanyashi buɗe idanunsa ahankali, murmushi Dr Adnan yayi masa tare da cewa. "Tashi kaci abinci, danajika shiru na ɗauka ma ai bacci kakeyi". Ɗan murmusawa kawai Saifuddeen yayi, inda shi kuma Dr Adnan yaɗan ɗago saman gadon da Saifuddeen ɗin yake yayi sama, shida kansa ya gyara masa kwanciya inda yayi kamar azaune yake saidai kuma bayansa yana jingine ne da gadon, abinci Dr Adnan ya miƙo masa kana ya koma gefe shima ya soma cin nasa, cikin nutsuwa haka Saifuddeen ya shiga cin abincin ahankali yake ɗan lumshe kyawawan idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali, haryanzu tunaninta ne kwance aƙasan zuciyarsa, ahaka dai har ya ɗanci abincin kaɗan ya ture sauran gefe, don shi ba mutum bane me yawan cin abinci sosai... Gombe Nigeria Dawowarta daga wajen aiki kenan, aɗan gajiye ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin nata, jakar dake hannunta ta aje gefe tare da soma rage kayan jikinta, saida ta cire komai na jikinta sannan ta sanya wata kekyawar rigan wanka baby pink colour, dogon gashinta ta ɗaure da ribbom sannan ta wuce kai tsaye zuwa toilet, wanka tayi da sabulunta me daɗin ƙamshi kana ta ɗauro alwala, kasancewar ankusa ƙiran sallan Magriba, zama tayi agaban tangamemen dressing mirror'n ta wanda gabansa ke cike maƙil da kayan shafa masu kyau da tsada, body lotion ɗinta tashafa wanda gaba ɗaya sanyin ƙamshinsa ya game ɗakin, yanayin yanda takejin kanta agajiye yasanyata miƙewa tsaye, ahankali ta ƙarasa gaban drawer ɗinta wanda cikinsa ke shaƙe tam da kayan sawanta masu kyau da tsada, wanda ita kanta batasan iyaka yawan suturun sawanta ba, wata ƴar doguwar riga marar nauyi ta zaro wanda yake daga ɓangaren kayanta marassa nauyi, rigar irin mai taushin nanne wanda takebin jikin mutum ta lafe, da fararen stones aka ƙawata wuya da hannayen rigan, wanda hakan kuma ba ƙaramin ƙarawa rigan kyau yayi ba, sosai rigan ta amshi jikinta ta lafe, hakan yasa kyakkyawan body structure ɗinta bayyana, wanda da ace lafiyayyen Namiji zai gani to fa tabbas dasai ya rasa nutsuwarsa, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasanyata zura wani dogon hijab ajikinta tare da shumfuɗa sallaya, koda ta idar da sallan magriba bata tashi akan sallayan ba har saida ta sallame sallan Isha, bayan ta tarin addu'ointa wanda mafi yawansu akan Saifuddeen ne, cikin sanyin jiki ta tashi daga kan sallayan tare da cire hijab ɗin ta ninkesa, kana tayi taku uku zuwa biyar ta isa bakin gadonta kwanciya tayi akan lallausan gadonda tare da jawo pillow ta matse a ƙirjinta, rumtse idanunta tayi da tsananin k'arfi tare da fesar da wani zazzafan numfashi me ɗan karen zafi yayinda takejin wasu zazzafan hawaye sun tsastsafo mata cikin jijiyoyin idanunta, cusa kanta tayi cikin hannayenta tanajin akowani bugu na zuciyarta da tunaninsa yake wanzuwa, ina yake!? a ina zan ganshi? wani hali yake ciki? sun kasheshi ko yana da rai? tana da buƙatar sanin waƴannan amsan fiye da komai ayanzu, gyara kwanciyarta tayi tare da buɗe idanunta, kan zanen pop'n dake mamaye saman ɗakin ta tsaida idanunta sun kad'a sunyi jazir cikin raunin murya take cewa. "Ya Allah kasa ako ina yake yana cikin ƙoshin lafiya, in kuwa sun mishi rauni ya Allah ka bashi lfy!". tafaɗi haka aɗan raunane, ahankali hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa suka biyo ta gefen kumatunta, haƙiƙa zuciyarta cike take da son jin wani abu daga garesa, yayinda idanuwanta kuwa ke ɗokin sake ganinsa, tunaninsa ya matuƙar tsaya mata azuciya babu dare ba rana ko yaushe bata da sukuni bata fahimtar komai domin duk nazarinta da tunaninta a kanshi yake k'arewa, sake muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta akaro na biyu, kana ta lumshe idanunta da har yanzu suke ɗigan hawaye, da sauri ta buɗe idanunta tare da dafe ƙirjinta dake wani irin bugawa sakamakon tunowa datayi yanda Yaran Dalla suka caka masa wuƙa abayansa, da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da sakin kuka me cin zuciya cikin yanayi mai kama da sambatu tace. "Ya Allah Kasa ba mutuwa yayi ba, Ya Allah ko sau ɗayane ka ƙara nunamin shi, ya taimakeni alokacin danafi kowa buƙatar taimako, Ya Allah kasa yana cikin halin nutsuwa aduk inda yake ya Allah ka kaddara saduwa ta dashi koda godiya in mishi!!". Da sauri ta d'ago kanta jin k'anwarta Zahira na cewa. "Dan Allah Anty Zaleeha, ki bar irin wannan kukan, kici gaba da yimishi addu'a insha Allah addu'arki zata riskeshi." cikin kuka ta kife kanta bisa cinyar k'anwar tata wacce ita kad'aine tasan da batun. Cikin kukan take cewa. "Bai sanniba, bai tab'a ganinaba cikin taron maza dake wurin kab babu wanda ya kula da ni bare ya taimaka min dan tsoron Dalla da sukeyi, sai shi d'aya ya zame min Garkuwata, kuma sun mishi illa gashi ban san ina zan sake ganinshi ba." shafa kanta Zahira tayi tayi tare da kwantar mata da hankalin. A haka tacigaba dayin kuka ƙasa-ƙasa tana me fidda shashsheƙa da haka har bacci ɓarawo ya ɗauketa. *** A gidansu Saifuddeen kuwa. Ummi ce zaune afalo tayi jigum yayinda tunanin ɗanta kuma farin cikinta Saifuddeen ke kwance acikin ranta, dare da rana bata da wani addu'a sai na nema masa lafiya awajen mai duka, Raliya ce da Adda Rahma da tazo musu tunda safe, sune suka tafito daga cikin kitchine, hannun Adda Rahma ɗauke da goran ruwa me ɗan sanyi, jingina bayanta tayi da jikin ƙofar kitchine ɗin tare da kafe Ummin nasu da ido, wani irin tausayin kansune ke ƙara ɗarsuwa acikin ranta a kullum, haƙiƙa SAIFUDDEEEN shine komai nasu, Allah Ne gatansu amma Saifuddeen babban jigone agaresu wanda kuma shine gaba ɗaya farin cikinsu. Raliya kuwa da sauri ta k'araso gefen Ummi ta zauna, ita kuwa Adda Rahma cikin sanyin jiki ta fara d'aga k'afafunda da suka kumbura sabida tsufan cikin jikinta da kyar take tafiya bisa dukkan alamu cikin ya cika wata bakwai ya shiga na takwas a hankali ta ƙaraso cikin falon tare da sanya hannu taɗan taɓa Ummi wanda

Table of Contents

Chapters

148 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148