Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Zulfa Book One Complete Hausa Novels 1,216 words 0 views Progress saved
Download Book

"Kaci abinci??" Ta tambaye shi tareda kafe shi da ido Gyada kanshi yayi alaman erh, murmushin takaici tayi tace"har ka iya cin abinci??" Kallon ta kawai yakeyi ga zuciyarshi na wani iri sakamakon hawayen da har yanzu basu daina zuba" kidaina zubarda hawayen ki am really sorry" "Ka iya cin abinci shine kace karna ci najiraka?? Ba damuwa nagode"tafada tareda barin wajen tana tafiya tana hada hanya Dasauri ya tareta yace "kiyi hakuri Zulynah bansan zai bata miki rai bah" Murmushi tayi tace" shi neh nace ba damuwa nagode" Tafiya tadinga yi har ta shige side dinsu dasauri yakarasa binta tareda tsayawa abakin kofa "Yar Umma yadai baki ganshi bane??" Hawayen da take kokarin rikewa neh ya gangaro mata sharewa tayi takwanta akan kujera tace" naganshi" "Toh Madalla barina kawo miki abincin toh" "Bazan ci bah" "Taya za'ayi kice bazaki ci bah bayan rabon ki da abinci tin jiya da safe" Zama Umma tayi agefenta tace"miye faru" "Umma nah ashe shikam ma mantawa dani yayi yaci abincin shi bayan yace min karna ci nawa zai dawo muci tare" tafada cikin kuka "Kiyi mishi uzuri mana" "Toh Umma kawo min abincin toh" Sosai jikin shi yayi sanyi yaji bai kyauta bah kwata kwata shifa ma a wasa yafada mata amma ta dauka dagaske soboda bai dauka zata dauki abin serious bah. Sallama yayi inda Umma ta amsa lokacin tana kokarin shiga cikin kitchen din part din ta. Gaishe ta yayi ta amsa a dakile cos itama bataji dadin abinda yayi bah. Hadiye masifarta tayi tace"ka kyauta shine kasa min y'a tajiraka bayan kasan bazaka dawo bah gashi yarinya har tafara ramewa" "Amin afuwa wlhy gabadaya ba acikin gari na wuni bah naso shigowa amma dare yayi sosai shiyasa ban shigo bah amma Wlhy tana raina" Haka kawai ta samu kanta da yarda da abinda yafada tace"aww hakane?? Toh kadawo lfy??" "Lafiya, danAllah kitayani bata hakuri" Tin kafin Umma tayi magana tace" ai nace babu komai koh??" "Erh kinfadi hakan" "Kawai dai banji dadi bane shiyasa"tafada cikin nuna rashin jin dadi shigewa Umma tayi yayi saurin matsowa wajenta tareda rike hannunta "Sorry once again" yafada tareda pecking din kumatun ta "Ai dai kasan banjin turanci koh??" Tafada cikin shagwaba "Toh kiyi hakuri" Murmushi tayi tace"amma zaka koya min turanci koh??" "Sosai mah har yawo zaki kaini kafin nabar garin nan" "Zaka bar garin nan fa kace??" "Erh mana aiki na yana jira na achan da nah zauna" "Yanzu zaka tafi ka barni nadaina ganin ka kenan??" "Toh da bazai koma inda yafito bane?? Umma ta yakatse su Abinci ta ajiye agaban su cikin tray, bude cooler din tayi wani kamshin dadi ya kaiwa hancin su farmaki. Wani sabon yunwa taji yakamata ba bata lokaci tadauki plates biyu tareda saka cokali daddaya. Zuba daidai wanda tasan zata iya ci tayi acikin plate, zata zuba mai ya rike hannunta tareda girgiza mata kai yace. "Basai kin deba min bah muci tare" cikeda rashin damuwa tamiyar da spoon nashi cikin plate dinta tareda Zuba juice acikin cups biyu. Duk abinda sukeyi Umma na kallonsu girgiza kai tayi tareda basu waje domin su sake dakyau. Cin abinci sukeyi babu wanda yace uffan acikin su harsuka karar basu sani bah. Mourad ji yayi kaman baitaba cin abincin da yakai wannan dadi bah tinda yake arayuwar shi. Juice din ta dauka tasha juice tana ajiye wa ya dauki nata yaushe"zan iya sha" Da murmushi takalle shi tace" duk abinda yake nawa daga yau kaima sun zamo naka" Cikin Jin dadi yace"dagaske??" "Erh" daidai saitin da janbakin ta ya taba ya kafa bakin shi idonsu a sarke acikin kowannen su. "Nagode koma miye na mallaka kema naki neh" murmushi kawai tayi har suka gama cin abinci. Wayan shi dake kara ya dauko ganin sunan dake yawo a screen din yasashi fadin "Ya Subhanallah"cos gabadaya ya gama mantawa da yabar wasu suna jiranshi. Hankalin ta tamiyar gareshi tana jiran yayi magana. Daukan wayan yayi yace" I will be there in the next 5mins" "Miye faru??" "Ashe na tsayar da wasu, barina je nasame su" yafada tareda mikewa "Nima zan bika" batareda second thought yace muje. Umma ta kwala wa Kira tace saisun dawo. Hannunta acikin nashi suka jera suna tafiya gwanin ban sha'awa, koina suka wuce sai an nuna su cos they look so perfect. Shiga sukayi cikin gurin inda baturai sunkai 10 awajen. Cikin turanci wani bature yace " it's like we are missing something in this drawing" Kallon hoton takeyi tace" Yay Mou dina wannan hoton baiyi bah" Kallon ta yakeyi da mamaki cos sai architects neh kawai zasu iya concluding cewan baiyi bah gashi ba turanci takeji bah da yace don taji anfada neh. Karasawa tayi wajen board din tayi ta dauki duster ta hau gogewa. Zaro Ido sukayi ganin tana goge wahalan da sukeyi. "Bari na zana muku wanda yake kaina" tafada cikin murmushi Tambayan shi sukayi abinda tace shikuma ya fassara musu , har zai hanata wani bature wanda alamu suka nuna shine oga yace yabarta(kun dai san turawa basu underestimating din mutum). Zanawa tafara cikeda kwarewa kaman wanda tasaba yi daman, baki da hanci suka sake suna kallonta. Juyowa tayi tace" ya kuka gani" Tafi aka fara acikin wajen inda cikin ransu cike yake fal da mamakinta, ware mata hannu yayi alaman tazo gareshi. Cikin sauri ta karasa ya Rungumeta tsam tareda daga ta sama yashiga juyi daita. Itakuwa dariya duk ya cikata wai akan dan wannan abin suke ta murna. Ajiye ta yayi baturan suka fara takowa wajen ta kowa na Mika mata hannu suyi handshake. Wani irin dadi taji kawai ta washe hakwara tareda Mika musu hannunta itama. "Yay Mou dina duk wannan murnan na miye haka?" "Kinsan nawa neh kudin da aka sa a abinda kikayi kuwa?" "Dan wannan abin??" Ta tambaya da mamaki Zaro Ido yayi wani farinciki na shigar shi soboda tunanin dasuka shiga kaikawo acikin kwakwalwar shi. "Muje" yafada tareda yin gaba da ita "Ina zamuje??" "Wajen babanki!!" "Babana kuma?"da mamaki Tsayawa yayi yace"erh mana babanki sarkin garin nan" Fizge hannunta tayi tace... *Vote,comment&share* *Mhizzphydo* [21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA* @MHIZZPHYDO A Sweet and pitious Romantic love story *Bismillahir Rahmanir Rahim* *Page 35* Fizge hannunta tayi tace "ni kadaina kiranshi da babana " "Why?" "Barina koma gida" Ganin bata gane abinda yace bane yace"Nace miyesa??" "Ohhh toh ai ba baba na bane" "Miye sa kika ce hakan??" "Toh ai kowa yaji sunana zaisan bashi ya haifeni bah" Numfasawa yayi cikin basarda shirmen ta yace "toh muje wajen shi" "A'a kaje in kadawo ina wajen Umma nah"bata jira cewan shi bah ta ruga aguje abinta... Da kallo ya bita sannan ya girgiza kanshi tareda bin bayan wa'inan baturen zuwa cikin fada... ```cikin fada``` "Kuna nufin kuce Zulfa ce tayi wannan zanen??" Maimartaba yatambaye su cikin turanci ga mamaki kwance asamar fuskanshi "Erh" "Daman in bazaka damu bah inason natafi daita USA zan nema mata makarantan Architects soboda gaskiya bai kamata ace wannan basirar tata yatafi abanza bah" Mourad yafada cikeda neman alfarma Numfasawa Mai martaba Malam yayi yace" kabari zanyi tunani akai" Toh yafada yana adduan samun nasara azuciyarshi sannan suka mishi bayanin kudin da daman aka sa akan zanen. Mamaki sosai Mai martaba Malam yayi ganin

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138