Chapter 98
Chapter 98
ka yi ne?" Duk da k'arancin shekaruna amma na fahimci shirun da na yi masa ba k'aramin dafa shi take yi ba. Ba abin da yake so irin na yarda mun yi magana ko da rashin kunya ne na yi masa. Amma ban yi hakan ba. Ni a karan kaina so nake na yi kuka, na caccaba masa maganganun da zasu gasa masa zuciya tamkar yadda ya yi dalilin da tawa zuciyar take gasuwa, amma na kasa. Tsawon sati guda muna cikin wannan matsanancin halin, daga ni har shi mun zama wasu iri. Gidanmu ya koma tamkar na zaman makokin mutuwar uwa mahaifiya. Sannan na k'i yin k'unshi har lokacin. Al'amarin da ya sake damalmala mana komai. Shi kam kawai k'arfin halin da aka san maza da shi ne. Amma kana kallonsa kasan yana dandanar kudarsa da shiruna. Yadda bana cin abinci haka shi ma baya ci. Gara ma ni da daddare na kan yi barci, amma shi duk juyin da zan yi zan gan shi kan sallaya ko yana zaune ko kuma yana sallah. Da asuba ya dawo ya tarar har na koma na kwanta. Ya zauna a bakin gadon. A sanyaye ya ce "Yabi wai a haka zamu rayu ne? Bazan iya wannan rayuwar ba. Ki yiwa Allah da ma'aiki ki bu'de baki ki fa'di duk abin da kike so. Na ro'ke ki ba dan ni ba, da Allah nake ha'da ki." Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa. Ya tsananta da magiya. Sai kawai ji na yi cak ya dauke ni ya yi nufin d'ora ni kan cinyoyinsa. Ai gaba'daya wani irin k'arfi mai tattare da matsanancin fishi ya taso mini. Da dukkan zuciyata na fisge na ingiza shi ya fadi k'asa warwas. Na dinga huci mai zafi, amma na kasa bu'de baki na yi magana. K'irjina sai harbawa yake yi da tsananin gaske. Ya mik'e ya kafe ni da ido, cikin kad'uwa da tashin hankali. Ya ce "Dan Allah bu'de baki ki yi magana. Fadi me zaki ce, idan kuma na zauna ki mini duka zai fi mini akan irin halin da nake ganin ki, ki yafe wa mijinki, ki yafe wa masoyinki, ki yafe mini, kaddara ce ta hau kaina Asiya". Na juya na kwanta ba tare da na ce uffan ba. Kukan kuma bai zo ba. Ya kasa hakuri ya sake biyo ni inda nake kwance ya hau lalubata, ban hana shi ba, ban kuma yi wani yun'kurin da zan tankwabar da shi ba. Ya yi abin da zai yi. Yana gamawa na lalubi zanina na daura na fice. Wanka na yi, sannan na dawo na kwanta. Bayan na mulke jina da hadadden man oriflame. Wanda jakadiyar kamfani ce ta za'ba mini shi fa kanta, q cewarta shi zai fi dace wa ta tarar fatata. *Kunsan dai Aisha Lame make up artist din Guduyo ce. Yanzu ma bata bata bar fatar Yabi babu gyara ba*. *Kun tandadi fame wash din nan kuwa da na yi ta jaddada muku muhimmancinsa a wajenku?* *Ku tuntu'be ta a wannan lambar dan samun sabbin kayanta masu kyau da farashi mai sau'ki da ya zarta na saura*. *07036662633*. Shi kuma yana kwance sai fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ke yi da k'arfi. Yau duk jarumtar sa kasa yin ayyukan gidan ya yi. Dan haka na yi abuna. Na yi abin karyawa har na gama yana kwance. Na d'aga labule na ce "Ka zo mu karya." Yana daga kwancen ya ce "Ko na zo d'in ma ai ba ci muke yi ba. Ki yafici abin da zaki ya fita ki rufe". Wasa wasa yana kwance har azahar, ko wanka bai fito ya yi ba. Abin da ban ta'ba ganin ya yi ba, zama da janaba. Komin dare baya kwanciya sai ya yi wanka. Ko da kuwa zai yi second round. Amma yau safiyar Allah kuma ba barci ba, amma yana nad'e ya kasa tashi bare ko ruwan shayi ya kurb'a. Na sani fishin nawa ne ya fara k'ure malejin jarumtar sa. Ina zaune ina tunanin al'amurar rayuwa sai na ga fitowar sa, d'aure da tawul da k'yar yake daga k'afafuwansa rauni gaba'daya ya bayyana a jikinsa. Da ya tashi dawo wa daga masallaci sai ga shi da Malam liman da Malam mai Tafsiri. Ganin dattawa kuma manyan Malamai na shiga marabatarsu da girmama wa. Shi da kansa ya yi musu jagoranci zuwa falonmu. Na zuba ruwa a k'aramin tray na ajye a gabansu. Na gaishe su cikin ladabi. Suka amsa suna saka mini albarka. Na yun'kura zan tashi na basu waje dan a tunanina wajensa suka zo. Sai kawai na ji sun ce "Ina zaki kuma, ai zuwan na ki ne". Gabana ya yanke ya fa'di to me ya kawosu waje na ni kuwa?" Malam liman ya yi gyaran murya ya yi addu'ar bude taro, ya nemi tsari daga sharrin shaidan da rundunarsa. Sannan ya ro'ki Ubangiji ya sanya albarka a abin da za'a tattauna. Aka amsa da ameen. Ya zarce da cewa "Asiya mijinki ya same mu, ya kawo k'arar kansa da kansa gabanmu. Da bakinsa ya ce ya yi miki laifi da ya amsa sunan laifi. Amma yana ro'kon mu zo mu baki ha'kuri a madadinsa". Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba. Domin ba k'aramin nauyi na ji ya kama ni ba. Akan me zai dauko mini manyan mutane irin haka? Malam liman ya zarce da cewa "falalar hakuri yawa ne da shi Asiya. Mijinki ya yi nadama, irin wacce ake so mumini ya yi. A wannan zamanin idan mutum ya yi kuskure ya yarda ya yin ma, har yake bada ha'kuri ba k'aramin mutumin kirki ba ne. Abin da yasa na yarda na zo kenan da bakinsa ya ce ya yi miki k'aton laifi. Sannan na ga rauni mai yawa a tare da shi, wanda idan ba'a ba shi dauki ba zai iya kwantar da shi. Ki gode wa Allah da ya baki miji mai kiyaye sallah. Sama da shekara da zuwansa unguwar nan ban ta'ba fashin ganinsa a sahun gaba na sallar isha da asubahi ba. Annabin Rahma ya ce wadannan sallolin munafukai basa kiyaye ta. Ki yi hakuri da inda ya gaza mutumin kirki ne, na shaida hakan". Sai lokacin kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, irin kukan da yake ki'dima duk mai sauraronsa, kuka mai dafa zuciya mai sawa a shid'e. Kowa ya yi shiru, illah Tijjani da yake fa'din "Alhamdulillah! Alhamdulillah cikin wani irin yanayi. Domin ya sani rashin kukan da ban samu na yi ba. Da rashin furzar da maganganu. Ya sanya na taurare nake dafa shi ta hanyar zuru. Malam mai Tafsiri da yafi kusa da ni, kuma yafi tsufa, domin ya tsufa ainun, na tabbatar ya haifi kamar Babanmu. Ya d'ora hannunsa a kaina yana shafa mini, cikin muryarsa ta girma ya ce "Yi hakuri jikata. Kara hakuri, Innallaha ma-assabirin. Ki daina irin wannan kukan zai janyo miki ciwo. Yi salati ki samu nutsuwa. Tsawon lokaci yana shafar kaina tare da maganganu masu taushi har na samu nutsuwar. Hannunsa na kaina ya ce "Shin Asiya ta huce ta ha'kura, ta yafe wa mijinta?" Da rawar murya na ce "Akan me zai dauko mini ku? Ni bai mini komai ba, kuma nima ban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161