Skip to content

Chapter 103

Chapter 103

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

Yabi ya yi tsananin da ka ce ya dawo da ita gida. Sai ya ro'ki na zo na zauna masa da ita. Ni kaina hankalina ba kwanciya zai yi ba idan ba zuwa na yi na ganta ba." Baba ya numfasa ya ce "Ai shi Tijjani bai gamsu zan kular masa da iyali dan karan kansa ba, sai ya zargi na yi masa fin k'arfi saboda y'ata ce?". Ta diriri ce ta ce "Haba Yaya ni Wallahi har kasa na ji babu da'di." Ya ce "To ki ji mana. Ban da dai ke ma kin banbanta ta ya ya zaki zo ki ce mini "Zaki dauki matar Tijjani a gaba na?" ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Ta shiga ba shi ha'kuri, shi kuma ya dinga yi mata sababi. Yana fa'din "Da kam nan da kwana biyu na yanke zata koma zan ha'da ta Mamarsu ta je ta zauna da ita ko na sati ne kafin jikinta ya yi k'wari. Amma yanzu na fasa ba zata koma ba. Ki fa'da masa na ri'ke ta, sai ta haihu tunda ba shi da kunya, ya banbanta, ya nuna uwarsa ce ka'dai zata yi wa iyalinsa hidima. Ai kuwa Babah ta dinga ba shi hakuri, ta lallaba ta zame kanta ta bar Tijjani tsundum cikin maganar. Ta shigo d'aki ta duba ni. Ta bani leda mai d'auke da soyayyun kaji. Da kuma soyayyar awara da ta sha yaji mai da'di fal leda (K'ara'i). Na fahimci duk yadda Babah bata shiga al'amarin Bulkachuwa Amma bata dauki abin da ya shafe ni da sau'ki ba. Samuwar cikin jikina kuwa sai na fahimci k'arfin soyayyar da take yi masa. Domin farin cikin da take ciki duk wanda ya rab'e ta sai ya gane hakan. Kusan kullum sai na amsa k'iran abokan arzik'inta. Suna mini sannu da jiki. Daga samuwar cikin zuwa yanzu na manta adadin da ta zo duba ni. A dakin Gwaggo ta shigo ta same ta suka hau cakar juna, tunda k'anwar miji ce. Gwaggo ta ce "Oh ni Asma'u ina ganin kananci a wajen Hauwa. Kina zazzame wa akan sha'anin yara. Amma tunda kika ji zaki yi jika sai b'are b'are kike yi da sintiri a hanya tamkar a kanki za'a fara yin jika". Ta ce "kya yi kya gama. Y'ay'ana nawa ne suka haihu? Yanzu ina ce duk sa'anin aurenta sun haihu dama wandanda suka riga ta auren. Duk ba jikokina ba ne?" Gwaggo ta ce "wace ni na ce ba jikokin ki ba ne. Gani na yi Ummi yar hutun ki ma baki ta'ba zuwa dubiya idan tana laulayi ba, sai idan haihuwa ta yi. Amma Yabi kin zo ganin ta, sau ba adadi sabo..". Ai bata jira saboda me Gwaggo zata ce ba. Ta sunkuci jakarta ta fice tana wani irin murmushin farin-ciki. Tare da ce wa "sai ki yi da wata ai. Ke da ake ganin shirunki da hak'urinki, nan kuwa ba'kinki fal zan ce da bita da k'ulli ne". Washagari ta shiga mota ta juya ba tare da ta ce wa Tijjani komai ba. Ai kuwa kwanaki biyu ya dinga wata irin zarya a cikin gidanmu ta ban mamaki. Baban Marina ya share shi. Rannan da daddare ya murje kunyar sa ya ce "Baba gobe zan zo na d'auki Asiya." Baban ya gyara zama ya ce "Ai haba?" Ya yi wani irin tare da sunkuyar da kansa k'asa ya kasa amsawa. Baba ya numfasa ya ce "Ai k'ure rashin kunyar ka zan yi Tijjani. Wai kai magidanci kada a ga gazawar ka. Shine ka turo mini uwarka dan ka nuna mini ita ce zata maka hidima kai tsaye ko?" Ya yi k'asa da kansa tare da ce wa "Ba haka ba ne Baba". Ya ce "Ya ya ne? Fada mini ina jin ka". Tsawon lokaci bai tanka ba. Baban ya ga ji da shirun sa ya ce "To uwar taka ma da soyayyarka ta rude ta, ta zo zata mini rashin kunya na fatattake ta, bare kuma kai karamin alhaki. Ai tunda ka nuna mini da wajena da wajen Hauwa da banbanci, ni kuma zan nuna maka da kai da Salisu d'aya ne a waje na. Bazan baka Asiya ba sai ta haihu ta yi arba'in". Ya kalli Baban ya ce "Idan na baka hakuri fa Baba, zaka ha'kura ka bani ita?" Kai-tsaye ya ce "Bazan hakura ba." Tijjani ya ce "To ka yi ha'kurin kuskuren da na yi". Ya ce "To na ha'kura Allah ya yafe mana. Ku daina banbanta iyaye. Dukkanmu d'aya ne." Ya ce "To Baba zan kiyaye." Suka yi shiru. Can Tijjani ya ce "Baba ko zaka yi hakuri ka janye zancen sai ta haihu, nan gaba a k'ara wata biyar fa, kafin ma ta haihun". Ya ce "To na ha'kura Tijjani. Allah ya yi muku albarka. Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku. Ya kuma hore maka ikon kula da iyalinka". Ya amw.sa da "Ameen Baba". Washagari da yamma ya zo muka tafi, ni kuma sai fishi nake yi. Muna isa gida ya rungume ni sosai yana ta sakin ajiyar zuciya. Ni kuma na sha mur, na kawar da fuskata gefe guda. Ya ce "Tunda mun dawo ai sai ki huce. Yau kwana uku ko hudu kina mini fishi. Gidan fa gaba'daya zafi ya yi mini da ba kya nan." Nan ma ban kula shi ba. Sai da ya dinga rarrashi da ban baki sannan na bu'de baki na ce "Ai dan ka ga na damu da kai ne shi ne kake musguna mini ta hanyar ce wa dan baka da abin duniya ne nake yi maka wani abu. Tunda haka zaka dinga yi mini kawai ka k'yale ni, kowa ya yi harkarsa". Ya dinga fa'din "ki yi ha'kuri na daina, dan Allah ki huce haka nan". Ya shafa cikina da ya fara tasa wa. Ya ce "Ya bebinmu?" Kawai sai kunya ta kama ni na ture hannunsa na rufe fuskata da hannuwana. Ya sani a jikinsa ya ce "Asiya ina son ki, ina son kasance wa tare da ke muddin rai. Jikina ya yi sanyi na kasa ce wa komai. Amma kalaman sun yi matu'kar tasiri a zuciya da gangar jikina gaba'daya. Ban samu kaina ba sai da cikin ya shiga wata biyar. A lokacin kuma ya fito sosai tamkar ba cikin fari ba. A kan dole nake yin k'unshin, amma sai muka tak'aita iya mutum uku kawai nake yiwa a rana. Amma ina yiwa masu son bak'i da tunda shi babu durk'ushe sosai. Sannan ina yin kitso. Ana kuma siyan lalle. Dai-dai lokacin kuma Tijjani ya fara zuwa Bauchi cikin kasuwar Muda lawal. Ya samu Alhaji Auta aminin mahaifinsa tare ma suke kasuwancin. Kawai dai da tafiyar ta yi nisa sai bai cigaba da bibiyar iyalin marigayin ba. Amma hatta katon fiilin da ya fito a gadon Tijjani a jere suka siye su. A yanzu hakan ma

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161