Skip to content

Chapter 116

Chapter 116

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ya ce ",Yauwa Ummilolo, na gode, hanzarta dan Allah". Ta ce "Zan sallami mutanan gidan da abin karyawa tukun". Akan dole ya ce "To." A hanzarce ta gama dumame ta sallami kowa. Kusan da sanda ta shiga gidan Nazira domin ta tabbatar mijinta baya nan. Amma bata ga wata alama mai kama da rashin gaskiya ba. Suka gaisa ta tambayi yara. Ta ce "Daga ina Yaya Ummi?" Ta ce "Mafarkin ki na yi Nazira shi ne na taho dan na ganki, na ga lafiyarki". Da'di ya kama Nazira. Ta ce "Madallah da Yaya Ummi. Kin kuma tarar da ni lafiya, har na karya na yi hidimar gida". Ta mike tana fa'din "Alhamdulillah! Tunda na ganki lafiya bari na tafi". Ta hanzari Nazira ta yi kicin dinta ta juyo mata dafadukan macaroni mai dan dama a madaidaicin filas. Ta ce ga shi ki kaiwa yaran nawa. Na maigidan ne bai tsaya karyawa ba. Ana ta jiransa zasu je Lame. Ya dai sha kunu a tsaitsaye." Ta karba da godiya ta tafi. Maimakon ta zarce gidan ta, gidan Marina ta yiwa tsinke. Duk wani bin kwakkwafinta bata ga ko ganin wata alama da take nuna sun san Yabi bata gidanta ba. Dan haka suma ta yi musu sallama ta tafi ba tare da ta bu'de musu komai ba. Sai da ta isa gidanta sannan ta kira Bulkachuwa ta tabbatar masa Yabi bata zo Toro ba. Ya lalube ta anan Bauchin. A rikice ya ce "Yanzu Ummi abin da Asiya ta yi mini dai-dai ne?" Kai tsaye ta ce "To ai bansan me ya faru ba Yaya Bulkachuwa". Ya ce tsaya ki ji, ki fa'da mini inda nake da laifi, ki kuma fa'di shin ta kyauta mini kenan?" Ta ce "To zan fa'di gaskiya tsakanina da Allah kuwa". Ya numfasa ya shiga koro mata bayani tiryan tiryan na gaskiya. Bata katse shi ba sai da ya gama tsaf ya ce "kin ji abin da ya faru". Ta numfasa ta ce "Ka yarda gaskiyar magana zan fa'da?" Da sauri ya ce na gasgata ki Ummi. Komin tasirin jini na sani zaki yi adalci domin ke din mai kauna ta ce na shaida." Ta ce "Na gode sosai. Amma gaskiyar magana kai ne baka kyauta ba. Kasan Yabi tasan akwai tsohuwar soyayya tsakaninka da Nasiba. Yanzu Kuma bata da aure. Akan wanne dalilin zaka dauke ta da kanka ka kai ta gidanka da sunan ta zauna, ba zama irin na bakunta ba.? Me yasa da Yabi ta ce bakuntar kwanaki uku ta amince ta yi muku baka yarda kun fahimci juna ba? Me yasa ka ankarata ta hanyar ce wa Nasiba tana da darajar da ba zaka kore ta a gidan ka ba?. Tsakanina da Allah wannan maganar ta yi nauyi a zuciya. Ai da sai ka ce mata ita ta kore ta, shi kenan magana ta k'are." A sanyaye ya ce "Na gode na kuma yarda na yi kuskure. Amma me yasa ta zarge ni?" Kai-tsaye Ummi ta ce "Kai ka bada k'ofar. Me yasa dan Nasiba zata zo gidanka sai ta hannunka zata biyo? Ba Yabi ce matar gidan ba? Me yasa sai da kanka zaka kai ta? Me yasa ka kausasa harshen ka akan zamanta?" Ya ce "Yanzu dai Ummilolo Yabi ta yi dai-dai da ta fice ta bar gidan babu izinina?" Ta numfasa sannan ta ce "A fuskar shari'a bata kyauta ba. Amma tunda ni mace ce nasan yadda take jin zafi a zuciyarta bata yi laifi ba, tunda ka nuna wacce bata zama dolen ka ba sai ta zauna mata a gidan ko tana so, ko bata so, ba tare da rarrashi ba". Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Na gode sosai Ummi. Na kuma gamsu da wannan gaskiyar ta ki babu son kai a cikinta. Kuma yanzu hakan tun jiya na saka Nasiba a mota ta dawo Toro. Na sallame ta a kurarerren lokaci ko?" Nan ma Ummi ta ce "Eh, baka girmama ra'ayin matarka ba, sai da ka bari ta yi maka tutsu, hakan kuma zai haifar muku da tazara da tsatsar zuciya mai yawa". Cikin karaya ya ce "Na gode bari na shirya yaran nan, mu fita nemanta, ki taya ni addu'a, gaba'daya yarinyar nan ta gigita ni. Wato Yabi jidalinta mai girma ne." Ummi ta kwashe da dariya ta ce ni fa ban ga laifinta ba Yaya Bulkachuwa. Haka kawai za'a lallaba a yi mata kutse mai dafa zuciya, da saka jinya a gangar jiki". Ya numfasa ya ce "Allah ya sauwake, ni Wallahi babu tunanin komai a zuciyata akan hakan". Ta ce "Kai kasan hakan, mu ina muka san zuciyar ka?" Ya ce "Shi kenan bari na saka d'ambar neman ta." Suka yi sallama, ya kashe wayar tare da zurfafa a tunanin ta inda zai fara nemanta. A daddafe ya yi wanka saboda azabar kukan Hamim. Domin a bakin band'akin ya zauna yake kuka na tashin hankali. Hanif kuma sai ri'ke shi yake alamun wai ya yi shiru. Dan haka ko da ya fito a rikice ya shirya, ya dauki yaran da yake ta gunjin kuka. Yasan kukan neman Amminsu yake yi. Allah ya zuba masa k'ulafacin uwa. Ya gama shawo kan Hamim ya yi shiru, sai kawai Hanif ya fa'di ya dan bugu a goshinsa. Ya fara kuka shi ma. Hamim da dama kukan ba daina shi ya yi gaba'daya ba, sai kawai ya bu'de baki yana taya Hanif. Suka rikice masa ainun. Ya jima kafin ya samu su tsagaita. Shi da kansa ya fahimci d'a sai uwarsa. Duk da yadda ya iya raino. Amma rashin Yabi a tare da su sai komai ya k'wace musu daga shi har y'ay'an sa. Har suka bar gidan bai yanke shawarar inda zai dosa ba. Amma yana hawa titi zuciyarsa ta fi rinjayar masa ya je Bulkachuwa. Dan haka gidan mai ya shiga ya sha mai. Ya siya wa yaran yoghurt da cake. Sannan suka dau hanya. Yana yi yana daukar fasinja dan ya samu sau'kin tsadar mai. Da walwala Babah ta karb'e su. Tana ta tambayar ya aka yi suka baro Yabi a gida ita kad'ai? Ya dan diririce, bayan ya ga rashin wasa a fuskarta. Murya babu karsashi ya ce "Bata jin da'di ne shi yasa bamu taho tare ba, nima kayan miya na kawo nan Dambam". Ta ce "Ayyah me ya same ta? Ko zazzabin damina ne da ko ina yinsa ake yi". A sanyaye ya ce "zazzabin cizon sauro ne, amma da sau'ki rashin k'warin jiki ne kawai." "To Ubangiji ya bata lafiya". Ya amsa da Amin cikin damuwar to ina Yabi ta fantsama kenan? Ya kasa ko da shan ruwan da yake gabansa bare kuma abinci. Yara dai suna ta cin abincinsu. Ta zauna tana fa'da masa sati mai zuwa Aliyu zai je Ibadan yin jarabawar zama likita, tunda karatun likitanci yake yi a jami'ar Jos. A gajarce ya yi murna da fatan alheri. Ta fahimci rudun da ya shiga amma ta matse ta yi kamar bata gane ba. Ya sassauta murya ya ce "Tafiya zan yi, zan bar yaran a nan, zuwa jibi zan dawo". Cikin nutsuwa ta ce "Haka kawai ka dauko su babu shirin zasu zauna ka bar mini su? Uwarsu ba zata ji dadi ba". Ya basar ya

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161