Chapter 120
Chapter 120
a fuskarsa ya kai intaha. Tsawon lokaci mun yi shiru. Yaran kuwa duk sun yi barci. Ya munfasa ya ce "Ki yi hakuri. Na baki hakuri. Tashi mu tafi, na yafe miki". Na sake hade rai na ce "Ba na son ka yafe mini, domin ban maka komai ba. Ban zalunce ka ba. Kai ne ka ke shirin zalunta ta. Shi yasa na saukaka maka hanyar rabuwa da ni. Kawai ka sallame ni, ba zan iya zaman zullimi da fargaba ba. Tunda ka fara samun kudi ka ke canjawa. Nan gaba bansan yadda zamu kwashe ba. Gara tun wuri na barka tun baka gama barina ba ". Murya babu amo ya ce "me nake yi miki Asiya?" Baka yi mini komai. Son ka ne ba na yi! Ko dole ne?" Ya mik'e tsaye ya ce "Babu dole, to ba ni yarana". Na rungume Hamim da yake ta barci yana sakin ajiyar zuciya. Na ce "Ba zan bayar ba, dauki Hanif shi kenan an raba." Nan da nan ya hau rantsuwar ba zai bar shi ba. Ba zai raba su ba. Na dage tamkar har cikin zuciyata da gaske nake yi. Sosai muke yin takaddama. Sai da na gama famfa shi. Ya sakankan ce bazan iya yarda ya tafi da su ba. Sai kawai na ce "Dauke su ku tafi, Allah ya shiga al-amarinsu." Nan da nan ya yi turus. Jikinsa ya yi sanyi ainun. Ya zuba mini ido tsawon lokaci, ni kuma na yi kamar ban ga ni ba. Ya koma ya zauna a maimakon mikewar da ya yi, yana kumfar bakin sai na ba shi y'aya'nsa. Ya sassauta murya ya ce "Na baki hak'uri fa little. Ki mini uzziri mana". Murya na rawa na ce "Sau nawa ka ke yi mini laifi ina share wa?" Da sauri ya ce "Da yawa. Ina kuma gode miki. Na kuma dha fad'a miki kina da alfarmomi masu yawa a waje na. Yanzu ki mini hakuri dan Allah. Bazan sake yin hakan ba." Na hirgiza kai tabbacin ban karbi ban bakinsa ba. Ya marairaice ya ce "Haba mana my little angel. Ki huce, kin san fishin ki kassara ni yake yi". Sai lokacin na ji kuka ya zo mini. Na dinga yinsa bilhakki. Tsawon lokaci sannan na daina. Ya saki gauron numfashi ya ce "very sorry little. Nasan kin huce, tashi mu tafi dan Allah". Na girgiza kai na ce "Ni kam bazan koma ba fa. Ai tunda har waya ka ke yi da ita, nasan akwai abin da zai biyo baya. Dan haka ka je na bar mata kawai." Ya diririce ainun. Ya fara musun basa waya. Na zuba masa ido na ce "Waye ya ce mini Nasiba ta ce da Dada za'a zo ganin gida?" Ya ce "Ni ne". "Me yasa ni bata fada mini a wayar ba? Me yasa kullum sai ta kira ka? Me yasa sai kai Tijjani? Tunda bata kirana, bata kiran Yaya Salisu da ragowar. Na tsani rashin kame wa". Ya kasa magana tsawon lokaci. A sanyaye ya ce "Ba ni da bakin magana , am speechless. Abin da zan iya ce wa biyu ne. Ki mini uzziri, ki yi hakuri." Na yi shiru. Cikin rarrashin ya ce "Wallahi duk hasashen da kuke yi ni ban tab'a d'arsa shi a raina ba. Amma na gamsu kin fini gaskiya. Idan kika yarda muka tafi yanzu kuma. Na miki alkawarin har kasa ta rufe idona babu magana mai tsayi a tsakanina da ita bare soyayya ko aure, In sha Allah ". Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba, amma kuma k'ullin zuciyata ya hau warware wa". Ganin rarrashin ya fara tasiri. Ya sake tausasa harshe ya ce "Ai ni na dauka babu abin da zan yi miki, ki yi mini yaji. Tunda baki kai hakan ba ma, na miki babban laifi, kika rufa mini asiri kika yafe mini. Amma yanzu kuma a kan zato da zargi kika tozarta ni. Me yasa zaki munana zato a kaina? Me yasa kika zabi ki janyo mini fishin Babah?" Yana rufe baki na ce "saboda ka fahimci ban dauki alamarin da wasa ba, ka kuma gane yanzu hankali ya fara ratsa ni. Ba komai zan lamunta ba". "A karo na ba adadi ina sake baki hakuri. Allah ya huci zuciyar ki. Dan Allah mu rufe wannan matsalar. Wallahi bazan sake yi miki hakan ba, babu ruwana da ita, ko kallon inda take bazan sake yi ba. Ko na ganta a wajen Dada idan ta gaishe ni, zan amsa ne ba tare da na kalle ta ba, bare na gane me take ciki". Na yi shiru. Ban tanka ba. Ya ce "Haba mana Little"! Na cuna baki na ce "To kuma wayar da kuke yi fa?" Da hanzari ya miko mini wayar yana fad'in duba ki ga ni. Na share lambarta. Na kuma jefe lambar a black list ta yadda ita ma ba zata same ni ba". Na yi shiru ya ce "please mana Little ki ce kin huce, ki ce komai ya wuce". Na dauke kai na ce "To kuma iyakar da ka nuna mini fa? Da ka ce gidan ka ne ba nawa ba?" Da rawar murya ya ce "Kinsan An nadamu ala ma fata? To hakan maganar ta ke. To ni me ma zan yi da gidan da babu ke a cikinsa? Idan wannan maganar ne ta sake b'ata miki rai to ki huce. Na baki gidan ma gabadaya. Ki yi yadda ki ke so a cikinsa. Shi kenan?" Na ce shi kenan, amma bazan koma yau ba". Da hanzari ya ce "A a kada mu yi hakan, yanzu zamu tafi idan ba so kike hankalina yafi hakan tashi ba." A hankali na ce "To kawai sai Babah ta ga zamu tafi? Ka bari idan na fada mata jibi sai ka dawo mu tafi". Da azama ya ce "Wallahi bazan iya ba, kada ki zalunce ni, kin sani bazan iya ba. Tunda mun shirya ina ruwanta da mu?" Ya mik'e yana ce wa "bari na je na fada mata zamu tafi". Na bi bayan sa da kallo. Ina jin fishin da na yi da shi yana warware wa. Na zuba wa yaran ido. Ina rasa ga ne wa nafi so a cikinsu. Dukkansu Abu guda nake ji a kansu. Amma na fi jin tausayin Hamim haka siddan duk da shine fitinanne kuma marar hak'uri. A fili na furta "Allah ka rayamu tare da yaranmu, ka tsare mana su, ka yiwa rayuwarsu albarka". Ina kallon Hanif da yake barcinsa akan gado illah kansa da yake jikina. Ina ayyana mutane masu karamci da sadaukarwa tun suna kananu ake fahimtarsu. Yana wahalar gaske ya ture d'an-uwansa a jikina. Ko abu ya dauka da Hamim ya fara kuka zai ba shi. Haka nan baya damuwa idan na goyi Hamim shi na rik'e hannunsa. A raina sai nake ganin shine yafi dace wa ya amsa sunan Baban Marina. Ko da yake bansan ko Baban Bulkachuwan shi ma haka yake mai hak'urin gaske ne. Na shafa kansa ina ce wa "Allah yasa ka zarce da hak'uri da yakanar ka. Allah ya saukaka muku rayuwarku gabadaya". Na yi shiru ina jin wani irin abu na tsirga mini da bansan ko mene ne ba. A hakan Babah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161