Skip to content

Chapter 141

Chapter 141

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

sassauci sai a samu masalaha a duniya, a kuma samu rabauta a duniya. Zan yi iyakar kokarina na fita a harkar mijinki, na yarda Yaya Bulkachuwa ba mijina ba ne, ba kuma zai zama ba. Kada ki ce maganganun da ya yi cin fuska ya yi mini, zahirin gaskiya ya amayar". Na rik'e hannunta murya na rawa na ce "Ban kullece ki ba. Amma idan na ce ban ji ciwon abin da ya faru ba na yi karya. Har abada ba zan iya auren mijin ki ba Nasiba. Amma na hak'ura na barwa Allah ya yi mini zabi akan lamarinku. Tunda ai ba haramun ba ne. Shi yasa na hak'ura na barwa Allah komai". Dukkanmu kowa zuciya ta narke, muka dinga kuka. Ubaid da yake gaban motar ya yi tsaki ya ce "Sai ku yi ai. Amma ai mu kam mun kudire matukar ya aure ta sai ya sako mana ke ko da kuwa a gaban alkali ne". Na daskare da maganar sa. Na tuna na ba shi watanni shida. Gabadaya ma shekarunsa ashirin da uku ne. Amma ya yi magana kamar wani babban wanmu. Sai kuma hawayena ya sake zuba a dalilin yadda maganar auren Nasiba da Bulkachuwa ta zama silar samar da soyayya a tsakanin ahalin Baban Marina. Yan ubancin da manyanmu suke gwada mana ya yi matukar zangwanye wa. Na yarda mafi yawan kalubale ya kan zo da wata nasarar komin kankatarta sai dai idan ba a kula ba, ko an bari hankali ya kwace an yi fishin da ya shallake hankali. ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Washagari duku duku Baba Maryo ta zo. Domin na je gaida Dada na juyo muryarta tana ce wa "Ai ko baki bijire mini ba gabad'aya ba zai aure ki ba, wane shi. Ashe dama arzikin da ake ga ni a tare da shi kazami ne? To ba zata sabu ba. Aure kam tabbas ya fasu fas. Dama ai ba so kike ba, tunda kin ringa kin tsorata da iblishiyar mata tasa. To ta je ta samu sai ta tabbata a matar d'an safarar kwaya ita kad'ai. Mutane babu Allah a ransu. Ka dinga neman arziki yaki haram yaki halal. Dama so na yi na nuna wa uwarta da ita Yaya Hauwa iyakarsu. To tunda bai shiryu ba, huta toro an bar musu shi. Watak'ila ma daurin rai da rai za'a yi masa. Ai da a sau'udiyya aka kama shi fille wa d'an banza mai yiwa iyayensa kallon raini za'a yi". A sanyaye Dada ta ce "Ai kuwa mai sunan manya ya yi hankali da girmamawa yake gaida kowa kamar ba shi ba. Kawai dai yana nuna son kai ne, ya fi nan nan da k'ofar Alhaji. To wannan kuma dariyar matarsa yake so, ya za'a yi tunda ya jarabtu akan ta.!" Baba Maryo ta ce "Ban da ni din, ni ce ai ko gaishe ni ba zai yi ba, ya kullace ni ainun. Tunda ake fad'in labarin wadatar da yake ciki, ashana bata tab'a had'a mu ba. Kai ya taka ya je gidana bai san wannan ba. Idan ya gan ni tamkar zai doke ni. Amma yanzu da yake ba shi da kunya har zarya yake yi mini. To na fasa ba shi Nasibar. Ba zai yiwu ba, ya je dai ya k'arata da afiruwar matarsa mai izgili. Kai ahalin Tijjani da Yabi za'a yi majununai, biyu ta had'u y'aya'n iska marasa albarka". Na sake jin cikin rauni Dada ta ce "Yanzu fa sun yi hankali suna girmama kowa. Yabi da kanta jiya ta zo har nan ta tafi da Nasiba wajen mai sunan manya. Kin san idan Yabin da ce ba za'a yi hakan da ita ba". Ta saki tsaki ta ce "Yo tunda ya rikice mata ai dole ta kai ta. Amma daga yau zan yanke komai." Dada ta kame bakin ta. Ita kuwa ta ci gaba da sakin maganganu masu nuni da dama ba Tijjanin take so ya zama surikinta ba. Wadatar da ake kallon ya samu ne ake son su lasa. A yanzu da ya hadu da ibtila'i kuma an janye saboda dama ba da zuciya d'aya aka yi abin da aka yi ba. Na shiga daga bakin kofa na gaida Dada, duk da tana ce wa "iso mana, ina tagwaye ko basu farka ba?" "Eh suna barci Dada". Na gaida Baba Maryo a gajarce. Ta amsa fuska babu walwala. Har na juya sai ce wa ta yi "Yabi ashe haka ya faru da Tijjani?" Na ce "Eh! Sai ji na yi ta ce "To wadannan kadarorin da suke yatsun ki da kunnawan ki sai ki hanzarta kad'ar da su dan ki dauka masa lauya domin dai a gindinki da na iyayen ki ya k'are. Gyatumar sa ma yar amshin shata aka mayar da ita. Watak'ila hakkin ta ne ya sanya yake gani a k'waryarsa. Na juya da nufin bata amsa sai na tuna kanwar mahaifina ce. Ba zai yiwu na yi fad'a da ita a yanzu da hankali ya ratsa ni ba. Nasan kuma dole ni ce a ciki tunda shi da kansa Baban Marina zai ce ai kanwarsa ce ta shiga rigarsa mana. Dan haka sai na hadiye na ce "To Baba Maryo zan yi hakan". Ta tunbatsa domin ta washi mu fad'i sunan ta. *** *BAUCHI* Kotun ta cika makil domin sharioi za'a yi masu daukar hankali. A kuma wannan ranar za'a yanke wa Tijjani hukunci. Da wuri muka iso. Da ni, da Yaya Salisu da Baban Marina da kuma Yaya Salamatu. Sai ko Yaya Ammar da yake Bauchi. Karfe shadaya aka fara shari'arsa. Babu wata hujja da zata wanke Tijjani. Domin lambar da ya ce an k'ira shi da ita kwata kwata bata shiga. Sannan an tambaye shi me yasa da aka ba shi kaya bai bude ya duba ba? Tunda ya dauki delivery a matsayin sana'a. Me yasa ba ya nazarin kauce wa dukkan wata matsala da zata taso. Wajibi ne idan zaka karbi sako, ka duba ka ga mene ne a ciki tunda idan aka kama ka ai kai ne a ciki. Sannan me yasa bai binciki ainihin inda mutumin yake ba?" Lauyan da k'aninsa Aliyu ya daukar masa, ya kasa

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161