Chapter 46
Chapter 46
kawo kofarmu. Hatta Babanmu sai da Inna ta bu'de masa kayan ya ga ni, ya yi addu'ar alheri tare da fa'din "Oh haka suka yi wahala mai yawa?" Ni kuwa ko kallon kayan ban yi ba, bare na ga mene ne a ciki. Da yamma ina zaune ina k'ulla wa Gwaggo siga. Sai ga Anas ya shigo ya kalle ni ya ce "Dada ta ce ki je yanzu". Na bata rai na kasa amsawa domin na tsani na je kofarta saboda dalilai masu dama. Na farko haushinta nake ji. Sannan bana son ganin mawuyacin halin da nake ganin Nasiba a ciki. Domin sosai ta mak'ala wa zuciyarta son Bulkachuwa. Kishina sai ya galgalata yake yi, duk da bata bu'de baki ta mini maganar ba, sai ma murnar da ta yi mini na samun miji irinsa wacce na ji tamkar ta caka mini wuk'a ne. Wannan shine daidan wani, karkataccen wani. Sannan kuma ina sake k'in shiga wajen Dada ne saboda kada na ga Tijjani. Shi yasa ma bana zuwa gaishe ta sai hantsi ya yi sosai. Gwaggo ta ce "Je ka ce tana zuwa". Ya ce "To" ya tafi. Akan dole na dauki mayafi na nufi shashin Dada. Ina hasashen menene dalilin kiran? A zauren Dada na tarar da shi a tsaye. Zuciyata ta tsinke sosai. Na yi kamar ban gan shi ba. Na wuce da nufin shiga cikin gidan. Ya bu'de baki ya ce "Ni ne mai kiran na ki ai". Na tsaya cak. Ba tare da na iya ce wa kanzil ba. Ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Ga ni na yi abu ya matso kusa sosai amma babu fahimta a tsakaninmu bare nasan abubuwan da kike bu'kata". Na ja tsaki na ce "auren so ake yiwa irin wannan tagomashin". Fuskarsa ta yamutse kadan. Ya ce "To na biyayya fa?" Nan da nan idona ya ciko da hawayen takaici. Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai. Murya babu amo ya ce "Abokina da muka yi karatu a Gad'au gobe zai zo. Ya dame ni akan na ba shi lambar amarya ko na kawarta dan ya ji irin yadda ake sallamar amarya da kwayenta a nan, da kuma abubuwan da kike bu'kata". Na ja tsaki tare da ce wa "Komai zai fito ta hannun ka ko ta sanadin ka bana sonsa ba kuma zan kalle shi ba." Ya zuba mini ido sosai cikin damuwa mai yawa. Cikin wani irin yanayi ya ce "Asiya Toro alfarma d'aya nake so ki mini, ko da kuwa ita ka'dai ce alherin da zaki yi mini. Ki taimake ni kada ki tsinka ni, ki yi mini wannan arzikin dan Allah". Ban san ya aka yi ba, jikina ya yi sanyi, mussaman yadda na ga ya yi kalar tausayi tamkar ba Bulkachuwa ba. Na yi shiru amma fuskata a cukune sosai. Ya sake ce wa "ki bani lambar wacce zai yi magana da ita Asiya. Sannan idan sun zo mini ranar daurin aure kada ki wula'kanta ni a gabansu. Na yarda bayan sun tafi ko menene ki yi mini, zan jure". Na sake gallah masa harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Tare da ce wa ban iya Yaudara ba, ba kuma zan fara yanzu ba. Ai na sha jin kana fa'dawa abokan naka ba macen da zaka aureta alhalin kasan bata sonka. Ba ayi macen da zata ce baka yi mata ba, sannan ka nace sai ka aure ta, duk wanda ya sanka yasan wannan alwashin na ka. To me yasa yanzu ka yarda zaka aure ni alhalin kasan bana son ka, bana farin-ciki da al'amarinka gaba'daya?" Kuka ya k'wace mini sosai. Murya babu amo ya ce"Kaddara ta ce a hakan Asiya! Ni kaina na kasa gane kaina. Wata'kila cika bakin da na yi ta yi ne, ya sanya aka jarrabe ni da son auren wacce ta washe ni, wata'kila kuma Ubangiji ne zai mini wani alherin ta sanadin ki shiyasa ya jingina mini sonki mai yawa." Na sake jan tsaki na ce "Ba wani alheri domin da zan ga sadda zai tunkare ka zan karkatar da shi na bawa wanda suka fika mutunci da so na". Ya girgiza kai ya kasa magana domin ransa ya baci idanuwansa har canja wa suka yi. Tsawon sakwanni bai iya ce wa uffan ba. Ni kuma sai fama nake da kuncin zuciya. Sannan sai yanayinsa ya sanya na ji babu da'di, domin duk yadda na tsane shi. Sai na ji ya d'an ba ni tausayi ka'dan. Muna haka Baban Marina ya dawo, ya zo wuce wa ta babban zaure ya hango mu a zauren Dada. Ina kallon yadda yake murmushi yana amsa gaisuwar Bulkachuwa da walwala. Ni kaina a wannan lokacin ya sace da fishin da yake yi mini. Domin da murmushi a fuskarsa ya amsa barka da zuwan da na yi masa. Har yana fa'din "Sannunku Yabi" Kunya ta saka na yi nufin shige wa wajen Dada. Sai ce wa ya yi "Dawo ku cigaba da tattaunawarku. Allah ya yi muku albarka. Allah ya sa ku zamo abin alfahari, Allah ya shiga al'amarinku". A hankali Tijjani yake amsa wa yayin da ni kuma ban amsa ba ko da a zuci ne. Yana shige wa ya kalle ni a sanyaye ya ce "Asiya Toro Baban Marina bai dauki auren nan namu da wasa ba fa. Mu ha'da kanmu, kada mu ba shi kunya dan Allah". Na ja tsaki tare da ce wa "Ni Malam na gaji tafiya zan yi". A sanyaye ya mik'o mini wayarsa ya ce "Saka mini lambar" A tunzure na ce "Ba ni da k'awa". Da sigar lallashi ya ce "Yanzu duk ro'kon da na yi miki? Farin cikin da Baban Marina ya yi a dalilin ganinmu bai sa zuciyarki ta rusuna ba?" Na murguda baki na ce "To ai dai kasan ba ni da k'awaye, Adda Nazira ce kuma ta yi aure, sai kuwa Nasiba ita ma kuma ai auren ta za'a yi ko?" Ya girgiza kai ya ce "Hakane! To Ina wannan fara mai dan jikin nan da yanzu kuke dawowa daga boko tare? Sannan tare nake ganinku a wajen koyon kwalliya". Na zuba masa harara na ce "Tsabar sawa mata ido har ka gane halittar ta? Har abada ba zaka burge ni ba Tijjani. Ba kuma zan baka lambar ba, domin dai da bakin ka ka tabbatar mini nema cikin nema haramun ne. Bari na shaida maka tuni an kai ku'din aurenta. Dan nasan kana iya lallabawa wajen ta". Ya yi sororo sai kuma b'acin ran fuskarsa ya ragu. Ya ce "Bana ma son lambar, na fasa, zan ba shi lambarki sai ki fa'da masa ta yadda zai turo miki ku'din kunshi da na kitso, ya damu akan a sallame ki ke da kawayen ki ne". Na yi shiru ban ce komai ba. A hankali ya ce "ya yi miki hakan?" Na sake yi masa banza. Ya sassauta ya ce "please mana Asiya Toro". Na harzuka na ce "Gaskiyar magana baka yi mini adalci, idan ina kaunar yadda kake gatsa sunana ha'de da na garina Allah ya tsine mini!. Ya dan murmusa ya ce "Da sannnu idan kin kwantar da hankalinki zan daina fa'da, na samo miki sunaye masu da'di da tsuma zuciya". Ba'kin ciki ya sake turknike
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161