Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

amma biyansa hakkin wai sai ya zama bashi, abin kaicon ma idan an yi masa aikar a bayar da ku'din nan, sai ya zama laifi. Mace ma'aikaciya sai ta bari ku'din mai wanki, ko markade, ko kuma mai dakan hannu ya taru a kanta. Ba tare da yarjejeniyar sai k'arshen wata zata biya ba. Anya kuwa muna son ganin dai-dai jama'a? Wannan wahalar data taru ta yi mana k'awanya ya sanya na mayar kitsona na ku'di. Domin tun daga alhamis idan na fara k'itso har lahadi, amma ba wanda zai cire ko da sisi ya bani a cikin matan gidanmu da duk kusan sati nake yi musu kitson su da y'ay'ansu. Kuma na sani hakan baya hana su karbin ku'din kitson a wajen mazajensu, ko iyayensu. Bisa shawarar Nazira na daina yiwa kowa kitso sai ta biya. Iya y'an k'ofarmu kawai nake yiwa kitso kyauta. Mama kuwa bata yarda ta ba ni kanta dama. Amma ina yiwa Inna da Gwaggonmu. Da kuma yan'uwana na k'ofarmu. Ai wannan bijirewar da na yi akan sai an bani ku'din kitso ya sake jefa tsana a tsakaninmu, domin duk inda Mama ta zauna sai ta ce "Uwarta ce ta kitsa mata, me za'a yi da irin wannan haihuwar a ce ba zaka bari aci arzikinka ba?" Iyayenmu maza da suka san suna biya basu dauki al'amarin a wani abu ba. Domin suna k'yashin a ce mu d'in muna da mamorar da zamu yi musu alfarma. Domin fa'di suke yi "Idan ku'di ne ku bata kudinta daidai da yadda na waje zasu biya ta, ko kuma daidai da wanda idan kun je wajen bare zaku bayar. Ita ce bata gaji arziki ba". Yayin da muka k'udire a ranmu ni da Nazira ba wanda zai sa na yiwa yaransa ko matarsa kitso akan dole domin suma basu taimake mu ba, dai-dai da ku'din islamiya da bai taka kara ya karya ba, basu ta'ba ha'da mu da y'ay'ansu sun biya ba. An sha koro mu da sauran k'annenmu, akan ku'din islamiya. Yayin da sauran yaransu basu da wannan matsalar. Idan zamu yi wata a zaune, Mahaifinmu ko iyayenmu mata basu samu sukunin biya ba, ba wanda zai dube mu. Dada kuma ba zata ce wane biya wa yaran nan ba. Ita kanta ta manta irin da'din da Babanmu ya jiyar da ita. A yanzu kam ta mayar da shi da dukkan ahalinsa tamkar wasu barori a cikin ahalinta. Tarin Baban kasuwa ya fi maganar Babanmu sau dubu. Tunda shine yafi kowa rufin asiri, sai Baban tsakiya. A batun soyayya kuwa kowa shaida ne Dada bata ha'da lamarin Yaya Anwar, da Tijjani da kuma Nasiba da kowa. Sun fi kowa lasisi a gidan, gasu dai ba y'an gidan ba ne tunda iyayensu mata ta haifa. Amma sun fimu gata da gadara a gidan. Yanzun nan Dada zata hau ihu matu'kar aka ta'ba guda a cikinsu. Sai yaran Baban kasuwa, sai na Baban tsakiya. Hakan dai hawa hawa abin yake. Canjin da nake samu a kitso ba k'aramin taimakona yake yi ba. Haka Gwaggo tana yin kokon safe, muna samu mu sha a ciki, har watarana a aikawa Yaya Ummi. Asusu na siya nake tura dan wani abu, domin ina matu'kar jin haushin yadda mu da gwaggonmu muke koma baya a gidan. Yaranta maza an d'ora musu nauyi mai yawa. Yaya Salisu ne kawai ya yi aure, shima ba wai wadatar ne da shi ba, aikin gini yake yi duk da ya yi karatu amma aiki ya yi wuyar samuwa tunda babu hanya. Su Yaya Rabi'u kuwa koami na gidan sune, Mama fa'di take ai sune maza, sune zasu taimaki ubansu, ga karatunsu su suke daukar nauyin kansu. Dan haka Gwaggonmu bata samun komai, amma idan an nutsu za'a fahimci kowa a kofarmu yana cin arzikin yaranta. Duk yan dakinmu ni ce mai tsiwa, ban dauko sanyin halin uwarmu ba. A tsaye nake kan kafafuna cak, haka zuciyata bata daukar raini. Sai dai kuma bani da kullaci, ina da saurin afuwa. A duk sadda na kalli Gwaggonmu da Yaya Ummi sai na tsinci kaina da yiwa kaina da Iklima addu'a samun miji na gari mai wadata, ko muma ma shiga sahun masu mutunci. Tun kafin hakan kuma sai Ubangiji ya hore mini iya yarfa kitso. Duk wata matashiya yar kwalisa a yankin nan ni ce mai yi mata kitso. A hankali sai na fara gwada lalle. Nan da nan sai Ubangiji ya sake haska mini. Layi ake yi mini na kunshi da kitso duk satin duniya. Muka fara dan warware wa, domin muna samun yan kuda'den yin bu'katar yau da kullum. Hatta Yaya Ummi ta d'an samu sau'kin matsatsacin da take ciki. Domin duk sati sai na cire mata wani abu. Da ku'din asusuna ya yi auki na fasa na siya mana kayan kwalliya masu sau'kin ku'di ni da Ikilima da Nazira, har ma da Ubaidan Innah. Sai kuma na sake siyan wani na k'udire niyyar dinki zan yi mana idan kudi ya taru. Tsawon dauki lokaci ina zubi, kafin na samu na yi mana y'an suturu ni da Iki. Ai Mama tana ankara da y'ar nutsuwar da muka fara samun kanmu a ciki, sai ta tayar da ballin sai na bar kitso, domin gashi yana yawa a gidan, ba dama ta zubo abinci, zata yi ta ganin gashi. Ko ina gashi ne, ta gaji da wannan k'azantar. A wannan karon Babanmu ya yi jarumtar cewar ba zai hana ni yin sana'a ba, tunda shi da kansa ya sani ba k'aramin rufa masa asiri sana'ar take yi ba. Kusan kullum sai na ba shi naira dari hud'u. Maganar maganina kuwa idan ba ni da lafiya, na dauke wa kowa. Dan haka sai muka fara saje wa da su Maijida. Tunda muma yanzu muna samun yan suturu babu laifi, duk da bai kai nasu daraja ba. Idan akwai abin da ya yiwa Mama tarnaki rashin kintsuwar Yaya Musa ne. Gashi dai shi ne babba, amma gaba'daya ya lalace, ya zama d'an iska, hakan kuma yak'i ya zame mata izna, a kullum cikin aibata yaran da ba nata ba take. Ta kuma gasgata hannu aka sawa d'anta, da kuma bakin mahassada. Ta kasa fahimtar rayuwa har yanzu. Tsabar kyashinta ta hana ya'yanta mata su tallafawa Babanmu da d'an abin da zasu iya . Kullum fa'di take ai hidima ta y'ay'a maza ce. Dan haka komai yaranta mata zasu kawo gidan to nata ne, sai ko idan dafaffe ne sai ta samma wadanda take so, wadanda bata so kuwa ko ta yi babu. Sai nake mamakin idan tana habaicin ku'din kitson da nake kar'ba, wai Gwaggo ta kasa bari a mori haihuwarta, ko ita wa ta bari ya mori tata haihuwar? Ko Babanmu da ya yi mata hidimar yaran ba dai tasa su kawo masa wani abu na tallafin gida ba tunda yana da k'ananun yara. Idan ma sun yi hankalin kawo wa to fa ita ce a hakku a kan kayan, ta dinga gadara kenan duk ba wasu kaya masu yawa ba ne, tunda dai ba wai ku'din ne da su ba, rufin asiri ne kawai. Sai nake mamakin wai mene ne manufarta ne? Da na kasa gane wa sai na ha'kura, amma hakan ya ja hankalina har nake sha'awar yin

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161