Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

Iki. Amma amincin da yake tsakaninsu sai Allah. Saboda Ubaida, Iki ta nace boarding ita ma zata tafi, duk da dai ta fara day ajin ta d'aya a sakandire su d'in kamar karatunsu ba zai yi sauri irin namu ba. Tunda a yanzu haka har Dada ta fara maganar auren Ubaida, a dalilin tana da garin jiki, kuma tana shirin shiga shekaru sha biyar ne. Cikin farin-ciki muke hutunmu, na saje a tsakanin Ikilima da Ubaida tunda ni din ba ni da auki. Ba abin da yake damuna sai bibiya da nacin yaya J. Matu'kar kuma na yi saken da muka ha'du yini nake yi babu sukunin a dalilin fama da tsallen badake da zuciyata take yi. Da yake aurena ba kwatsam ya zo kamar na Nazira ba, Baba ya samu damar siyan dimemiyar katifa mai nagarta. Ya tanadi labulaye da kafet, da ledar tsakar daki da kuma bargo. Irin dai kayan da aka yiwa Nazira. Ya ce idan ya samu dama ko a ranar da za'a kai ni ne idan ku'din gado da kujeru sun samu sai a siya tunda gasu nan a bakin titi ko ina, idan kuma bai samu ba to a hakan zai kai ni arzikin gidan miji yafi na uba. Ban damu da rashin kayan katako ba, na sani in sha Allah yan'uwana zasu yi mini irin na Nazira. Sai dai bani da garanti akan manyanmu yan dakin Mama. Domin sun yi nisa a cikin *BAK'AR TA'ADAR* Y'an ubanci. Su Yaya Salisu ne kawai zasu tsaya mini tunda sun fara daukar albashi duk da dai ba mai wani nauyi ba ne amma dai sunfi da . Ranar asabar mun dawo daga Islamiya. Yammaci ne sosai muna tafe da yan ajinmu. Mun zo daidai wani gida da bai kammala ba, muka ga Bulkachuwa da wata yarinya wacce nafi zaton ita ce Bilkin da na ji yana fa'da a waya kwanaki, sun fito daga cikinsa. Gajeriya ce, amma fara ce sai dai ko kusa bata kai ni ba. Sannan ita din yar duma duma ce tamkar su Nasiba. Kirjinta a cike yake, jikinta irin rugu-rugu ne. Nan da nan shaidan ya kawo wa zuciyata caffa domin take sai na yi aiki da zato, na zarge su da al'amarin da shaidarsa yana da tsananin tsauri. Na kalli Nasiba na ga hankalinta na kansu, tausayinta ya kama ni, domin sai yanzu na gane ba son Nasiba yake yi ba, domin ko ka'dan bai yi mata uzziri irin wanda ya yiwa Bilki ba. Ko da yake maganganun da mahaifiyarta ta yi wa uwarsa ne suka yi masa ciwo ba ka'dan ba. A zuciyata na ce shi kuma Bulkachuwa yana son lukataye masu manyan nonuwa. Na sake kallonsu na gan shi kamar kullum ba wani wadatatcen wanka, yana cikin yanayin babu yabo babu fallasa. Amma ni kam duk saurayin da ya zo mini a haka ina da tabbacin ba zan saurare shi ba. Domin an sanya mini son namijin d'an wanka, haka nan na k'yamaci marar gyara irin Tijjani. Amma a hakan yake murza zuciyoyin yan mata kintsatssu da watsatssu. Na sani kuma kyaunsa da zubin k'arfin da yake da shi yake rudarsu. Gaba'daya a murde yake dukkan physiques dinsa sun bayyana alamun yana motsa jiki yadda ya kamata. Na ja tsaki muka wuce, yayin da ya yi kamar bai hango mu ba. Ba zato na ji Nasiba ta barke da kuka mai sauti. Wani har tsayar da mu ya yi yana tambayar ba'asin kukanta, domin dai ya dauka ta samu labarin rasuwar uwa ko ubanta ne. Kukan nan na Nasiba ya yi matu'kar dukan zuciyata, domin na san pain din da ake ji na kubuce war masoyi domim ni din katuwar victim ce. Muna tafe, tana kukan bata fasa ba, duk yadda nake bata ha'kuri da kalamai masu nutsar da zuciya. Kukan nata sai ya zama sanadin tabarbare war sassaucin da na yi akan al'amarin Bulkachuwa. Domin na dauke shi a mai son kansa, mai fifita bare akan jininsa. Sannan fitowar da suka yi daga kongon gidan da babu kowa a ciki ya sanya na sake k'yamarsa da dukkan zuciyata, domin kowa ya shaida shi din mai BAK'AR TA'ADAH ne. Da k'yar na shawo kanta ta yi shiru. Amma a k'asan raina haushin makauniyar soyayyar da take yi masa nake yi. Gaba'daya ta lalace, ta zube bata farin-ciki ko ka'dan da auren da za'a yi mata. Uwarta kuwa ta ja ta dake akan sai dai ta canja uwa matu'kar ta ce ba zata yi wa mahaifinta biyayya ta so d'an-uwanta da ya za'ba mata ba. Duk da k'arancin shekaruna na fahimci Tijjani ne kawai mahaifiyarta bata so, domin kuwa mahaifin su Nasiba bai cancanci ya yi irin wannan ikon ba, tunda gaba'daya fita ya yi daga hidimarsu, ba wanda ya taba ganin an kawo musu wani abu daga mahaifinsu, ko danginsa, duk wahalarsu uwarsu ce da danginta. Amma an zo batun aure ya nuna ikonsa na uba, ita kuma duk ba'kin cikin da ya k'unsa musu daga ita har Dada sun manta. Abin da nake tambayar kaina shine shi wanda Baba Maryon ta fifita akan dan yar'uwarta tana da tabbacin nagari ne? Ko dan kawai ma'aikacine, ya kuma gina gidansa? Na yi imani da ace Bulkachuwa yana da ku'di to ko yafi haka lalace wa za'a ba shi, duk wani na'kasunsa sai an yi masa kwaskwarima ya zama abin uzziri. Amma da yake bashi da ko sisi, sai take ta akilon y'arta ta nisan ce shi, ta so d'an-uwanta na dangin ubanta, na d'an yar'uwarta kuma ya tabbata a lalace. Muna isa gida Dada ta hau tambayar makusidin kukanta. Kai tsaye na shiga rattaba mata dalilin. Ta yi tsaki ta ce "Kare ya cinye miki zuciya Nasiba. Ina ce jiya a gabana ya tsaya yana miki kashedi akan ki sakar masa kurwarsa? Bakaken maganganun da ya cusa miki, ai masu cizo ne da kina da hankali. Domin bai ji kunyar idona ba ya ce miki komin k'wadayin ki shi yafi k'arfin ko dandana shi ki yi, bare kuma ki mallake shi a matsayin miji. Amma dan lalace wa har ki zauna kina kuka dan kin gan shi da wata? Bayan Allah ya baki mai son ki, nutsatssatse ba irinsa ba. Bayan hakan kuma mai abun hannune ta ko ina ya yiwa mai sunan manya fintikau. Ban da ma darajar jini me zai sa ki so shi haka? Ko an yi auren ma wahala zaki sha tunda ba sonki yake ba, ga kuma talauci da takaicinsa." Jikina ya sake mutuwa ina ayyana duk soyayyar da take tsakanin Dada da Bulkachuwa amma take iya fa'din hakan a kansa saboda Nasiba? To wai wa take so ke nan a tsakaninsu? Take na yanke hukuncin Nasiba take so. Na tsinci kaina da jin haushin yadda bai san ciwon kansa ba. Kullum a fa'din ya daina mugayen dabi'aunsa yake, ashe ba hakan ba ne. Ina tsaye tamkar gun ki aka fara kiraye kiraye sallar maghariba. Murya a dashe na ce "sai anjima Dada". Na tafi na barta tana ta kumfar baki da dan mulmulallen bakinta. Muna idar da sallar na kalli Gwaggo na hau rattaba mata bayani. Ina fa'din "Gwaggo ashe har yau Bulkachuwa yana yin iskanci? Dazun na gan shi da wata sun fito

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161