Chapter 77
Chapter 77
"Da nasan zaki kalli idona ki yi mini irin wannan tayin na raini Billahillazi da dazu ban yarda na karbi ban hakurin ki ba. Amma shike nan. Daga yau din nan bana bu'katar ayi mini lalle da kitso a gidan nan gaba'daya ma". Ina jin hakan na takarkare na ce "Bilhiillazi ba zai yiwu ba, komai kake ji da shi Tijjani, baka isa ka hana ni sana'ar da ka gan ni da ita ba! Duk masifar ka kuwa". Ya murmusa ya ce "Lokacin da aka dauke ki aka ba ni babu shawarata ai ba a ce mini mata zasu dinga yi mini zarya a gida ba. Dan haka yanzu da na ga bazan iya d'auka ba, na dakatar da su". Na sake hassala na ce "To wai dole aka yi maka ka zauna da ni? Na ce ba na sonka, kai ma baka sona, to mu rabu mana. Mugunta ce kawai ta sanya ka ri'ke ni, kake musguna mini." Ya ce "Shike nan bar shi a muguntar ne kawai. Sai dai ki sani na riga na samo wa kaina mafita. Ki saurari abin da zai biyo ba. Ban karbi auren ki ba sai da na kudire wa zuciyata komin rintsi bazan bari mugun halinki ya sanya na kunyata Baban Marina da Babah ba. Ki je ki karaci diban albarkar ki. Ai Ubangijin adalci ya riga ya samar mini mafita a cikin wula'kanta ni da kike yi tun kafin a halicce ni". Daga haka ya fice. Gaba'daya na kasa gane manufar maganganunsa. To wacce manufar ya samo? Na kwana ina tauna maganganun Tijjani. Zuciyata ta yi nauyi a wajen son na fahimci inda ya dosa. Ko dokar da ya sanya mini ta hana ni sana'ata bata tokare mini wuya ba. Irin son na gane mafitar da ya samo. Kwanaki biyun da suka biyo baya, zaman namu ya sake yin tsami bisa dalilai guda biyu. Na farko ya tire kan ra'ayinsa na kada a ayi masa lalle a cikin gidansa. Sannan ya tsiri ya yi wanka ya sheka kwalliyar da ni na koya masa yin ta. Da daddare zai dauki wankakken kaya kuma gogagge ya fesa turaren da duka gidan sai ya amsa tsabar bulbulawar da yake yi, sannan ya fice ko kallon inda nake ba zai yi ba bare ya yi mini sallama. Ba zai dawo ba sai goman dare ta shud'e. Wannan al'amarin ba k'aramin ci mini kwarya yake yi ba. Na rasa inda zan tsoma raina da ba'kin cikin da Tijjani yake guma mini. Mussaman na barina a gida da daddare ni ka'dai kamar mayya. Ranar da muka yi sati a cikin wannan halin. Na bugawa Yaya Ummi waya, ji na babu kuzari ya sanya ta dinga fa'din "Mene ne, me ya same ki Yabi?" Na kasa bu'de baki na ce mata uffan, illah kukan da nake yi mai cin rai, mai kuma sauti sosai. A lokacin kuma dare ne sannan yana gidan. Ya ji ni sarai, tunda a lokacin yana falo. Amma ya yi kamar bai ji ba. Washagari da asuba sai ga Yaya Ummi ta diro mana gidan. Tausayinta ya kama ni. Yargale yargale da ita. Da alamun ma kukana bai barta ta yi barcin kirki ba. Ta same ni kad'ai a dalilin bai dawo masslaci ba. A gigice take tambayar me yake damuna? Murya a dashe tsabar kuka na ce "Tijjani yana shirin kashe ni da raina ne. Haka siddan ina zamana ya saka mini rai zai mayar da ni makaranta na samu shaidar kammala sakandire. Yanzu ya zo ya ce ya fasa. Hakan bai ishe shi ba sai ya ha'da har da soke sana'ata. Sannan dan yasan Baban Marina ba zai saurare ni ba, sai yake amfani da hakan yake musguna mini. Fiye sati yana gaba da ni. Sannan kulllum dare sai ya sheka wanka sannan ya fice ya bar ni a gida sai dare ya raba zai dawo. Ni nasan Bak'ar TA'ADAR sa ya koma. An cuce ni Yaya Ummi." Na fa'da ina rushe wa da kuka sosai. Daidai lokacin kuma ya dawo, amma kukan da Yabi take yi tamkar na mutuwa shi ya hanasu jin motsinsa. Ya zauna a barandar yana son fahimtar abin da yake faruwa. Jikin Yaya Ummi ya yi sanyi. Ta ru'ko hannuna ta ce "Yabi nutsu ki ji ni. Shin me kike masa yake yi miki hakan?". Cikin kuka na ce "Bana yi masa komai". Ta numfasa ta ce "Me yasa kike gaba da shi? Da kina gaishe shi, na tabbatar Yaya Bulkachuwa zai masa miki." Na yi shiru dan kuwa gaskiya ta fa'da. Ta sake ce wa "Da kin ja shi a jikin ki, da ba zai iya fitar da yake yi ba. To me zai yi a wajen bayan yana da d'anyar amarya mai cike da shiriritar kuruciya?" Na bata rai na ce "Kawai saboda ke da shi akwai amana da yarda shi yasa kike shaidar sa a bayan idonsa ni kuma kike bani laifi a kan idona ko?" Na fa'da hawaye na ziraro mini. Ta tsananta ri'ke mini hannu ta ce "Gaskiya ai bata bu'katar ado Yabi. Babu ruwan alk'alami akan kina so ko ba ky so. Kawai girman hakkinsa da ya rataya a kan ki za'a duba. Idan baki sau'ke ba Wallahi halaka zaki yi Yabi. Ni yanzu son nawa mijin nake yi? Amma na yarda kaddara shi ta zaba mini. Dan haka na yi hakuri nake yi masa biyayya, duk da shi din ba duka yake sauke hakkin da shari'a ta gindaya masa ba. Amma na sani ina rabo mai girma a wajen Azza wa jallah". Na tsananta kallonta domin gaskiya ta fa'da. Har zuwa yanzu da ta zarce shekaru goma da aure bata son mijinta, ni shaida ce akan hakan, amma kuma ha'kuri da biyayyar da take yi akan sha'aninsa mai yawa ne. Ta numfasa ta ce "Yabi ba kya yarda da Tijja Yaya Bulkachuwa. Su kuma maza da kike ganinsu komai zaki yi musu na kyautata wa matu'kar ba kya mutunta shinfidarsu, to fa komin kokarin ki a banza ne a idonsu. Saboda haka ki d'auki matakin gyara a tsakaninku." Na nisa na ce "Baya gamawa da wuri Yaya Ummi. Ni gaskiya bazan iya ba." Ta ce "Ahab dama da labarin neman auren da yake yi ya riske ni, sai da na ce na tabbatar ke ce silar k'arin auren sa. Ai sai ki yi tunda al'amarin kishiyata bai saka kin k'yamaci kishiya ba". Wani irin abu ya soki k'irjina, ban san mene ne ba. Amma gaba'daya ji na yi tamkar zan shid'e. Na rushe da kuka mai tsananin gaske. Ta ce "Ai indai kika cigaba da tafiyar da shi a hakan, tabbaskuka na gaba. Ba ki ga Bilkin da yake zuwa wajenta ba, gansamemiya ta yi biyu da rabin ki." Da rawar murya na ce "Me za'a yi da mai BAK'AR TA'ADAH irin ta Tijjani. Aure ko rufa wata biyu ba'a yi ba har ka fara neman wani auren. Na rantse Yaya Ummi sai dai a tsine mini. Amma bazan taba zama da wata macen a k'arkashin ikon Tijjani ba". Ta sake ru'ko hannuna ta ce "Idan kina son ki zauna lafiya, ki yi sana'arki, ki cigaba da tallafa mana. To ki zauna lafiya da mijin ki, ki daina gudunsa, ki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161