Chapter 59
Chapter 59
ko taba ba, amma ban ci ba. Sai bayan isha sosai ya shigo. Hakan ba karamin sake fusata ni ya yi ba. Ina zaune a dakina ido ya yi jawur, ya kumbure saboda kukan dana yini ina yi. Da azama ya iso gare ni yana fa'din "Asiya Toro me ya same ki, kin ga yadda kika zabge kuwa? Ga idon ki tamkar mai fama da matsanancin ciwon apolo. Mene ne yake damun ki?" *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Da zafin rai na ce "Kai ne ka fitine ni, irin fitinar da ko maki'yata bana fatan a fitine ta irin haka." Na sake rushe wa da kuka tamkar an fa'da mini mutuwar mahaifina. Ya ki'dima ya ce "Me na yi miki? Fa'da mini dan Allah". Takaicinsa ya nemi sark'e mini numfashi. Na kasa magana illah hawaye da yake zuba tamkar famfo. Tsawon lokaci ya yi shiru yana sauraron shesshekar kukana. A sanyaye ya mike, murya babu amo ya ce "ki k'arantawa kan ki k'iyayya ta Asiya! Bai kamata ki kuntata wa zuciyoyinmu irin haka ba. Ki cigaba da addu'a da sannu komai zai wuce." Har ya kai bakin kofa ya ce "kin ci abinci kuwa?" Cikin fishi na ce "Bazan sake cin abinci ba, sai yunwa ta mayar da ni gawa In sha Allah! Ya girgiza kai ya ce "Babu laifi". Maimakon ya yi kwanciyarsa sai na ji yana ta buruntu a kicin. Shude war mintina talatin sai ga shi da bowl yana fa'din "Ki dubi Allah da ma'aiki ki tashi ki ci, ba dan ni Tijjani ba. Dan Allah". Na sassauta kukan domin Gwaggo ta cusa mana yin uzziri matu'kar aka ce saboda Allah. Ya zauna kusa da ni sosai ya miko mini. Cikin rarrashi ya ce "Allah ka yarda da Asiya, ka sata cikin bayin da ka yarda da su". Jikina ya yi sanyi. Na kar'ba, na fara cin indomien da ta yi da'di tamkar ba girkin namiji ba. Ni da nake fa'din bazan ci ba, sai gashi na share ta tas. Da hanzari ya karbi kwanon ya mik'o mini ruwan hannunsa mai rangwamen sanyi. Take na nemi jirin da nake ji na rasa. Na yi gyatsa. Sai kawai na gayra na kwanta. A hankali ya ce "da kin daure kin dan yi tattaki kafin ki kwanta". Ban kula shi ba, a haka barci ya sure ni. Bansan sadda ya tafi nasa makwancin ba. Washagari mirsisi na k'i yin abin kari. Bai matsa mini ba. Ya siyo kosai da kunu ya kawo mini. Kwanaki suka yi ta shud'e wa, har na samu sati a gidan aurena. Har lokacin kuma ban yarda na sake d'ora tukunya ba. Shi kuma ko ya yi fishi, ba ya jure ganina ban ci abinci ba. Kan dole sai ya nemo mini. Ranar da na cika kwanaki goma ya fara gazawa da al'amarina. Ga shi ku'din hannunsa sun tasar ma k'are wa. Ya zaunar da ni ya sassauta murya ya ce "Asiya yanzu a ce abincin da zamu ci ba zaki dinga girka wa ba? Kina kallon kayan miyan can da yawa sun lalace. Ya kike so na dinga yi ne? Idan na fita tun safe na dinga bulayin abin da zan yi na samu taro da sisi dan asirinmu ya rufu amma bazan dawo na tarar da kwanciyar hankali ba? Yini nake cikin zullumi da fargabar halin da kike ciki, da abin da zan dawo na tarar. Me yasa bani da wata alfarma ne a wajen ki?" Na zum'bura baki ainun. Tsawon lokaci ban ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Pls Asiya na roke ki, mu zauna lafiya ki kwantar da hankalinki dan Allah". Tsawon lokaci ya dauka yana rarrashi, akan na ce masa na yarda zan dinga yin girki. Amma ban yarda na ce masa komai ba. Ya harzuka ya ce "Allah kai ne shaida ta." Ya tashi ya bar ni. A hakan na cike sati biyu. A wannan lokacin kuma aka fara zuwa mini lalle da kitso. Na rasa a inda zamu dinga zama. Domin tsakr gidan babu bishiya kuma babu rumfa. Baranda kuma idan rana ta bude babu dadin zama. Dakin da kayansa suke nan ne yafi dace wa ya zama dakin da zan dinga yin sana'a ta. Dan haka na shiga na tattara masa kayansa gefe d'aya, na kunna turaren wuta a dalilin kayansa masu datti na zube a k'asan. Na ha'da na d'aure su waje guda. Yini na yi ina lalle. Sai yamma ya dawo gidan da ledar abincin da ya siyo mini. Kallonsa kawai na yi, na gane ya ji haushin cika masa daki da na yi da mata. Ya ajiye abincin ya juya. Sai dare ya dawo lokacin babu kowa. Tuni kuma na share dakin na kintsa shi tamkar ba'a ciki muka yi ba. Fuskarsa a daure ya tarar da ni ya ce "Asiya Toro kada ki kuma shigar mini daki da nufin yin kitso ko lalle". Na cuna baki na ce "Idan na kuma fa?" Ya girgiza kai ya ce "To ki kuma din". Washagari da hantsi sai ga Rafi'a ta shigo mini. Da walwala na karbe ta. Ta dinga fa'din "Amarya ashe haka kika iya kunshi da lalle?" Da murmushi na ce "Ina koya dai, idan kina so sai ki zo na yi miki". Da babbar muryarta ta ce "Ai kuwa na gode sosai". Tijjani na fita na shiga d'akin muka fara yin kunshin. Kafin na gama mata har mutum ukun sun zo. Da azahar ya dawo gidan, ko d'ar ban ji ba, balle na yi fargabar na karya dokar sa. Ga mamakina bai shigo ba, bare ya dauki matakin da nake son ya dauka. Amma sai na ji ya bu'de murya yana kiran Rafi'a daga falon. Ita kuma ta shiga da saurin ta. Wani irin abu ya d'an mintsini zuciyata. Amma na sanya jarumta na boye abin dana ji din. Ina dan jiyo maganganunsu, har na fahimci sun saba dama tunda yayanta abokinsa ne. Bansan me ya ce mata ba, na ga ta fito ta shiga kicin. Abin ya sake buguna. Ban ankara ba na ji ta fara jajjage. Wata babbar mace da na gama sanya wa lallen. Ta kalle ni babu alamun wargi ta ce "Je ki karbi hidimar mijinki a hannun waccar yarinyar tun baki janyo wa kanki sanadin bacin rai ba". Na yi yak'e na ce "Ai tare muke da ita, k'anwarsa ce." Ta saki gauron numfashi ta ce "Tau ya yi babu laifi, na dauka babu sidi bare sadada a tsananinku. Amma dai kada ki fara saka wani lallen, tashi ki je ki marabce shi, ki bashi ruwa sai ki dawo. Ki kula da auren ki da kyau kin ji". Ganin ta haife ni, dan na tabbatar tana da yaran da suka zarta ni.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161