Chapter 23
Chapter 23
kalli Yaya Salamatu na ce "Yaya" Sai kuma na fashe kuka sosai. Dukkansu matan sai suka taya ni kukan in ban da Yaya Ummi da take Jin zafin yadda nake damuwa da lamarinsu alhalin ita ma ba sonta suke yi ba in aka dauke Naziran. Da rauni Yaya Salamatu ta ce "su uku sun kawo dubu sha biyar biyar, yan dakinsu kenan. Sai ummi ta kawo dubu biyar, Ni kuma na bayar da ashirin maigidana kuma ya bada buhun masara da na shinkafa ayi hidimar biki da su". Su Salisu kuwa sun ha'da hamsin a tsakaninsu dan haka dari da ashirin ne a k'asa kacal". Nan da nan na zaro magana tamkar babbar mace na ce "Ai kuwa sun isa Yaya, kuje ku siyo mata katifa da labule da ledar tsakar daki. Na kunce hannun zanina na kunce na fito da kudi kimanin dubu sha bakwai da dari takwas. Na ce ga nawa a siya mata bargo da zanin gado. Su Mama ku fito da kwanuka da tukunya. A kai ta a hakan da ikon Ubangiji watarana sai ta yiwa wani kayan daki na alfarma, ai duniya ce mai rawar y'an mata na gaba ya koma baya". Hatta Mama a wannan ranar na ga kallon sassauci da adalci take yi mini, domin da ta ga na sake dauko bankina na mik'a wa Nazira na ce "Ki fasa ki yi dinkin fitar biki nasan zasu ishe ki tunda kinsan mu din masu k'aramin karfi ne, masu nema a wajen Àllah." A fili take fa'din "Yabi da Nazira sai Allah". Baba kuwa zuba mini ido ya yi, tsawon lokaci kafin hawaye ya goce masa. Duk muka ha'du aka yi ta kuka tamkar an ce ya mutu ne. Domin ita kanta Mama da take ha'da kai da matan su Baban Tsakiya suna sake tsananta mana, ta sha mamaki da ta ga suna yiwa ya'yansu hidimar aure basu yi kara sun saka da Nazira ba. Wata'kila a haukanta zasu yi ko saboda da ita. Da rawar murya Baba ya ke fa'din "Allah ka sake jefa soyayya da tausayi a tsakanin ya'yana, Ubangiji na gode maka". Yaya Indo ta kira Malam Yunus ta fa'da masa ku'din lefe ya bayar yadda zai iya ba sai ya yi ba , domin kuwa muma abin da zamu iya za'a yi. Da yake ba yaro bane ainun, sai ya gamsu ya ce zai yi mata lefen yadda ya sauwaka, sannan zai bawa Yaya Salisu ku'din da ya sauwaka shi mutunci ya gani dan haka komai zai yi. Ba wanda ya san me ake ciki domin kowa ya zuba ido yana jira aje ganin dakunan amare Yayin da ta bangarena nake ta danne damuwar auren da Yaya J zai yi da Maijidda. Ita ka'dai ce amaryar da bata da kuzari a dalilin babu ha'din kai ko zumudin ango, komai sai dai mahaifinta ko na angon su yi mata. Gefe guda kuma Nasiba ta susuce domin ba karamin son Bulkachuwa take yi ba, wanda aka ce ya fito kuma a dangin Babanta sun ce bai shirya ba sai bad'i. Bulkachuwa kuwa yarinyar da suke takaddama ta haihu an yi gwajin halittar dan Adam bashi da alaka da jaririn. Sai dai an yi masa hukuncin bulala tamanin tunda ya amsa da bakinsa ya ta'ba takarta. Wannan lamarin, da bulalar ya yi matu'kar sururuta shi. Ya zama abin tausayi, duk wani iyashegensa ya zubar da rabi. Kowa ya ganshi sai ya tausaya masa. Hatta ni da bama ga maciji sai da na yi masa jaje. cike da alhini, ya dinga fa'din na gode "Asiya Toro, ki yafe mini, a duk sadda na tuna addu'ar da kika yi mini cikin fishi da kika ce sai na hadu da sharrin mace, sai na ce ashe dai Asiya bayan samun tallafin dan aljani yayin fa'da, har baki idan kika yiwa banu adam sai sun taimake ki, ya zama wajabat. Shiyasa na k'udire zan roke ki, ki mini addu'a na zama yadda mutane na gari suke". Na girgiza kai na wuce shi "Ina cewa "Allah ya shirye ka Tijjani". Ya d'aga murya ya ce "Da biyu kika yi wannan addu'a domin da zuciyarki fes take da ni Yaya Tijjani zaki ce". Ban tsaya ba, bare na tanka shi, a zuciyata kuwa ina fa'din mashiririci, ba sauya wa zaka yi ba, borin kunya ne kawai, ka zubar da mutuncinka a idon kannenka da iyayenka, Allah ya shirye ka kawai. Shikenan sai na dawo gida, muna ta shirin bikin Nazira. Auren da ya zo tamkar dirar mikiya, ya yi matu'kar rage mini tashin hankalin da nake ciki. Kitso da lalle nake yi babu hutu, tun safe idan na zauna sai magariba, sallah kawai take tayar da ni. Haka nake mika ku'din ga Baba ina fa'din "A dinga siyan kayan cefanen biki Baba" Da farin-ciki yake fa'din "Madallah da Yabi Asiya". Kallo daya za'a mini a gane ina cikin tasku kawai boye wa nake yi, sannan son Babanmu ya fita kunya da tozarta da ake son ya yi, ya danne wanccan damuwar. Domin yadda nake kishin Babanmu da yan k'ofarmu bana jin anan kusa za'a samu mai yin hakan. Shiyasa na cire son jiki, da lalaci nake sana'a, Ubangiji kuma ya haska, ya saka mini hannu, domin a rana ina hada dubu shida zuwa bakwai, mussamna idan kwanakin da ake yin biki ne. Da ce a birnin Kano nake yarfa kunshin nan ai da ku'di masu nauyi zan dinga ha'da wa, amma hakan ma na gode sosai, tunda mafi yawa manyan mata idan sun zo basa bayar da iya ku'din sai sun mini k'ari. Bana kuma jin k'yashin na bayar da komai dan mu yi hidimar mu cikin rufin asiri. Duk yadda Yaya J yake son mu ha'du na rufe kofofin da zasu sa mu kebe. Ranar litinin dukkanmu muna wajen Dada. Ana ta hira, na yi lakwas a dalilin bani da kuzari, ba k'aramin cizona auren J da Maijidda yake yi ba, har addu'a nake yi kada a wayi gari aga zuciyata ta buga a dalilin ba'kin ciki. Kwana nake yi ina kuka, ina kalubalantar wannan hukuncin da aka zartar mini tare da tsanar Baban Tsakiya da Baban Kasuwa. Tabbas a idona su din ba kowa bane face mutane masu son kai kuma y'an jari hujja. Dada sai farin-ciki take zata aurar da jikokinta kusan goma. Ta kalle ni ta ce ",Ke da Nasiba ne aurenku ya yi gardama, ga shi kune fitanannu." Ban kula ta ba domin abin da yake zuciyata fadinsa da ciwonsa sai ni da mahaliccina. Balle Nasiba da ta bari halin da take ciki ya bayyana a komai na ta. Ni mamakin da take bani wai akan Bulkachuwa take wannan ba'kin cikin, sannan abin kaicon shi bai ce yana sonta ba, kawai ya lura da yadda take mararinsa sai yake amfani da hakan yana sata tana yi masa bauta. Misali komin dare zai kawo indomie ya ce ta dafa masa, ko kuma ya ce ta dafa masa ruwan wanka, ko shayi. Haka idan zai fita zai bata mukullin dakinsa ta je ta gyara masa. Bai zame masa komai ba, ya kawo mata kayansa matu'kar zai ga tana wanki, yana fa'din "Ga karo". Bata damuwa hakan zata karba, ta wanke, ta goge. Shi kenan sai yake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161