Skip to content

Chapter 155

Chapter 155

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

irin kukan da yake yi mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?" Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na. Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da kalubalen rayuwa. Asma'u ki ji tausayin ta?. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata. Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi." Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko iyalinta". Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same su ya rufe da ce wa kada su fad'awa kowa sai abu ya kankama. Domin tafiya gabar kiran Allah ne. A gurgurje na je gidan Nazira na dubo yaronmu. Da yamma muka juyo da Yaya Aliyu akan gobe Baban zai zo BAUCHI don ayi masa passport. Ba a fito da maganar tafiyarmu ba sai da komai ya kammala ya rage saura kwanaki hudu. Baban Marina da kansa ya fad'awa y'an uwansa cewar zasu tafi Saudiya. Da Yabi da diyarta da Dada Tijjani ya biya musu. Aliyu ya biyawa Hauwa. Shi kuwa Yabi ce ta biya masa. Suka ka'du k'warai. Amma da yake dangantarsu ta yi tsami ainun kowa ya hadiye a ransa tunda yanzu so suke ace kowa yafi kusa da Baban Marina a tsakaninsu. Sannan basu gamsu Yabi ce ta biya ba. Duk da dai sun yi matukar sikewa da lamarinta tun auren Iklima. Zuwan tawagar matar gwamna Toro gidan Marina ba k'aramin cece kuce da girmama lamarin Yabi ya janyo ba. Ranar talata da asuba muka nufi Kano tunda an ce shabiyun rana zamu tashi. Karfe tara a airport din ta yi mana. Aliyu bai tafi ba sai da ya ga tashinmu. Sannan ya juya da twins da Ikilima da suka yo mana rakiya. Hamim sai kukan sharbe yake yi. Hanif sai hak'uri yake ba shi yana ce wa "Mun girma fa Hamim. Ammi ba dadewa zasu yi ba. Ba ta ce addu'a zasu je su yiwa Baban 2 ba? Husna zata raina ka fa". Suka bawa Aliyu tausayi. Haka kawai yaran suke ba shi tausayi ainun. Bai bar Kano ba sai da ya siya musu kayayyakin wasa da na ciye ciye dan su warware gabadaya. Kai tsaye a Madina muka sauka. Mun gaji likis. Dole muka kwanta. Dada sai addu'a take yi tana fad'in "Allah k'amshi ya cika hancina, haske ya cika idona, k'arfi ya yiwa gangar jikina k'awanya, farinciki da imani sun cika zuciyata. Allah ka karawa Annabi daraja. Allah ka karbi addu'ar da zamu yi, ka bamu k'arfin da zamu yi ibada ta gaskiya." Sai ta zauna. Sai ta zabura ta je jikin windo tana leken asumayar masallaci ma'aiki. Tana kuka tana fad'in "Rabbani yadda ka sake yi mini gatan ganin koriyar gubba ta d'an Amina mai wuyar ga ni. Allah kasa zan gan shi da idona. Allah ka bani ikon rokon gafararka idan na shiga rauda. Allah ka shirya mini zuria, ka jefa soyayyya a tsakanin ahalina. Allah na yi tuba. Allah mai babban suna aiko ni ya yi takanas, Ubangiji a karba a sassauta a kubuto da shi albarkacin masoyinka Baban Nana". Duk juyin da zan yi zan ga idonta biyu. Babah kuwa barci ta yi sosai domin bata runtsa ba a jirgi, ita take ta fama da Husna. Daf da asuba muka tashi, muka yi alwallah muka nufi masallaci. A harabar hotel din muka had'u da Baban Marina shima ya fito zai tafi. Na kalle shi cikin sabuwar jallabiyar da na siya masa guda uku a Kano. Ya yi fes da shi. Garin Madina rahama ne. Gabadaya zukatanmu cike suke da shauki da rauni. Duk juyin da muka yi da Dada ta saka silifas din ta. Ce wa ta yi "Wane mutum ta taka k'asar Madina da takalmi? Mu dai da muka ga zamu taka ba zata ce komai ba. Allah ya yafe mu kawai" Kan dole muka k'yale ta. Domin har muka yi kwanaki biyar a a Madina bata yarda ta saka ba. Duk ranar da aka yi ranar juma'a ma haka ta tako. Sai da muka shiga motar tafiya Makkah sannan ta saka takalmi, tana hawaye tana fad'in "Allah ina son na sake dawowa. Idna ban samu damar ba, na yi godiya. Allah karbi addu'ar da muka yi." A Makkah kuwa har tausayi suke bani tunda muka je dukkanmu a masallaci muke kwana. Mu yi sallah, mu yi dawafi. Duk shekarun Dada bata zama. Ko dan yar firit ce irina? Ban sake gasgata komai na Dada na kwaso a halitta ba. Sai a tafiyar nan da muka yi. Kamar da muke yi ta baci. Na tsinci kaina da addu'ar kada Allah yasa na yi halinta idan shekarun girma suka cimma ni. Tunda ta sha fad'ar hatta fad'an da na yi ina karama itama haka ta yi a lokacin kuruciyarta. Baban Marina kullum sai ya ce "Dada yau ki kwanta ki huta, Hauwa ke ma ki huta, Ubangiji ya ji addu'ar mu da ikon Allah Tijjani zai fito. Idan kuwa har muka ga bai fito ba, to tabbas zamansa a can yafi alheri. Ku duba shekarun da Annabin Allah Yusuf. Da'n Annabin Allah Yakub, d'an Annabin Allah Ishaq, d'an Annabin Allah Ibrahim A.s. ya yi a kurkuku. An tambayi Annabin Rahma wanne mutum ne yafi kololuwar daraja da nasaba, sai ya ce D'an uwana Yusuf A.s. Amma ya yi shekaru masu nauyi a sijin. Hakan bai zame masa tawaya ba, sai ma k'ara masa kusanci da Ubangiji ya yi. Bayan ya fito kuma Ubangiji ya karrama shi daga bawa ya koma shugaban kasa, kuma babban d'an majalisar sarki." Dada tana kuka ta ce "Hakane Alhaji amma tunda zan iya bari kawai na yi ibada tuk'uru. Na nemi gafarar Allah, na nemi soyayya da tausayi da afuwa ta wanzu a gidan Marina. Bar ni na yiwa Shehu addu'ar ya fito ya cigaba da walwala cikin iyalinsa. Yabi kad'ai idan na kalla sai na ji kuka, bare y'aya'nsa. Ni dai na yafe maka Alhaji. Kaima ka yafe mini". Sai ta kece da kuka. Ya rik'e ta a jikinsa ya ce "Sha'anin uwa ai mai girma ne Dada. Hakkin haihuwa kad'ai ya isa ayi mata biyayya, a girmama sha'anin ta. A kuma dauwama ana rokar mata alherin duniya da na kiyama. Ban kullaci kowa ba bare ke da aljannata take damafare da sawunki." Cikin kuka ta ce "Albarkar d'aki ka rabauta duniya da lahira Alhaji". ** Kwanakinmu goma a Saudiya. Saura kwanaki biyar mu koma gida. Addu'a kam mun yi ta sai fatan alheri ya biyo baya. Imani ya sake cika mini zuciyata. Na ji sassauci mai yawa akan kullatar da na yiwa mutanan da suke gwada mana rashin kirki. Sai na fahimci afuwa da yafiya suna warkar da zuciya, suna sake girmama mutum a wajen jama'a da wajen Ubangiji. Kwatsam na kunna wayata

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161