Chapter 93
Chapter 93
da murya ya ce "Hankalina ne ya tashi matu'ka da gaske. A ce matar aurena tana garanranba a gidajen mutane har almuru da sunan sana'a? Ai k'arshen tozarci ke nan. Amma ai na ha'kura kin san ina sonki fiye da komai Asiya. Ban so wani abu a duniyar nan da ya zarta ki ba. Uwa da ubana ne kawai a gaban ki. Dan haka ki daina damun kanki akan wasu matan. Ba sonsu nake yi ba. Da gaske ba wacce nake so a zuciyata sai ke. Amma zan iya ganin wata ta burge ni ko ta bani sha'awa a dalilin Ubangiji ya sanya sha'awar mace sama da d'aya a zuciyar mazaje. Kullum ina ro'kon Ubangiji ya tsare ni da sha'awar wata macen fiye da ke. Duk sadda na ga wata zata burge ni ko ta ba ni sha'awa gida zan garzayo na ga halalina, na yi abin da nake so da ita. Ke dai idan kin gan ni afujajan na dawo miki, to ban da musu da bijire wa da sunan jan aji". Dan haka ki saki ranki da ni, ke nake so, ke ce halaliya ta, da ke nake fatan na rayu muddin rai". Na fara k'ananun hawaye na ce "To kuma nufinka korata da ka yi da daddare a ganduna ne? Ya tafi a bilis?" Ya tarairayo ni cikin rad'a ya ce "Ai ya wuce tunda da kaina na je na dawo da ke". Na fara turza k'afa ina fa'din "Alkur'an ban yarda ba". Ya sheke da dariya ya ce "Dole sai kin nuna mini kina da alaka da mutanan Gwaram da Birin kudu domin a bakinsu nake jin wannan rantsuwar". Na ce "To mahaifiyata ta fito daga yankin ai kuwa kasan jininsu ce". Ya ce "Haka ne. To yanzu me zan yi ki yarda ki huce". Na shiru ina tunani sai kawai na ce "Yi mini kukan zakara". Ya ce "kukan sa wanne a ciki?" Na ce "oh kukan zakaran kala kala ne?" *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Ya ce "Yana cara idan afijir ya keto, yana yi yayin kiran sallar farillah akwai kuma wanda yake yi idan ya ga kaza yana kyarkyarar ta, yana hilar ta dan ya samu hadin kanta". Kunya ta kama ni na ce "Yi mini wanda yake yi idan alfijir ya keto kawai". Ya kuwa ce "Alkur'an ba shi zan yi ba tunda ni ma yanzu kyarkyarar ki nake yi". Kafin na ce komai ya tak'arkare ya fara wani irin gurnani yan kur kur sai ya kuma ya yi cara tamkar dai zakaran gaske kafin na ankara ya turmushe ni irin yadda zakara yake dank'ar kaza. Washagari da walwala muka tashi ya dawo Tijjanin da yake kaffa kaffa da ni. Sai ririta ni yake yi. Komai shi ya yi har abin karyawa. Na kalle shi cikin nutsuwa bayan ya d'ora ni akan cinya yana shinshinata tamkar maye. Na kama gemunsa na ce "Wannan shine .... d'ina. Amma ba shine na jiya da shekaranjiya ba". Dariya mai yawa ta k'wace masa ya ce "sabo da Allah little mene ne wani dash dash? Ki ce Tijjanin da kika saba fa'da mana tunda har yau ba ni da k'imar da za'a sakaya mini suna". Na yi murmushi na ce "Ai tunda na yi al'kawarin sai na haihu da na saka maka suna, to fa sai na haihun. Idan ka matsu kawai nan da sati na fara amai, ka kai ni asibiti ana gwada ni ace ciki ne, tun a ranar zan fara fa'din sunan na ka". Ya kankame ni sosai yana dariya kwarai da gaske. Ya ce "Nan da shekaru goma masu zuwa zan tisa ki a gaba ina miki bitar wadannan kalaman a lokacin kin kai ashirin da bakwai. Na ce "ko zuwa lokacin y'ay'a nawa na haifa?" Ya zuba mini ido ya ce "Allah yasa sun kai uku" Na ce "Haba dash dash ina laifin hudu ma. Nifa ina son yara da yawa." Ya yi kissing din goshina ya ce "Allah ya bamu masu albarka. Nima ina so. Amma kin san dole control zamu yi bazan yarda ki tara yara da yawa ki man ce da sha'anina ba". Na yi k'asa da murya na ce "Kai ne fa bebina na farko ta ya ya zan mance ka? To ko y'ay'a dari na haifa kai ne a gabansu. Ni burina na haifo mai kama da kai ma". Nan da nan kuma sai na rufe fuskata alamun kunya ta rufar mini. Shi kuma da'din kalamaina ya yi matu'kar kama shi. Ya samu nutsuwar da gaske ina sonsa yanzu. Ya rungume ni tsam tsam ya kasa cewa komai. Ya sakar mini nishin da yake rura mini jiki. Ya ce "Ni kuma na fi son ki haifo mini little girl mai kama da ke. Amma ba mafad'aciya irin Asiya Toro ba". Na cuna baki na ce "Yo ai ni fa'da na sai an tab'o ni". Ya ce "Amma Asiya ai ni bana tab'o ki kike rikice mini. Yanzun nan zamu rabu k'alau. Idan na dawo sai na ga kina share ni, ko mu yini lafiya, idan mun kwanta ki hau buge mini hannu kina ture ni. Haka ake yi?" Na ce "Amma ai sai ka dade baka dawo ba ne, nake share ka. Zuciyata tana harbawa da k'arfi tare da raya mini tadi ka tsaya yi". Ya dad'a ruk'o ni sosai cikin rarrashi ya ce "Shaid'an ne yake wasa da ke Asiya. Kuma dai ai babu kyau a yanke wa mutum hukunci da zato. Ki dinga sassauta mini, da gaske bana son fishin ki, bana son mu dinga fad'a". Na dauke kai bayan na tura baki na ce "Ai kai ne, kake murde mini tunda ka fahimci ka fara shiga raina. Idan ba wuta wuta nake yi maka ba, ba k'aramin jana zaka yi a k'asa ba." Ya kwashe da dariya mai tsananin gaske. Ya ce "Asiyaty an buga an bar ki. Wato da iron hand zaki yi handling d'ina." Na ce "Ai dama yaya Ummi ta ce "Nan gaba sai ka mini fiye da abubuwan da na yi maka. Ilai kuwa na fara ga ni. A buge wa Asiya baki. A zabge Asiya da mari. A dinga yiwa Asiya iyakar daki a gidanta. A rufe wa Asiya gida. Aka fitittke sai ta tafi gida. An fara jawa Asiya rai. Sai an jagwalgwalata sai a juya baya a ce sai ta bada hak'uri. An ki yiwa Asiya ciki. Idan Asiya bata saki lalle ko kitso ta taso ta yi barka da dawowa ba, a yi mata fishi. Asiya ba son a dinga gatsa sunan ta da na garinta take yi ba. Amma haka za'a daddage ana ce mata Asiya Toro. Ai Wallahi na yi laushi. Ina matukar hak'uri. Ban ma sake maka fuska gabadaya ba kake yi mini hakan ina kuma a ce lako lako nake?" Ya jima yana kallona da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161