Skip to content

Chapter 65

Chapter 65

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

"Asiya Toro babu magana, babu yi mini barka da zuwa?" Na galla masa harara na ce "To ni ina ruwana da kai da zan yi maka magana? Ba gaba mu ke yi ba?" Ya ce "mun shirya ai. Na baki hakuri, kakarmu ta baki, mene ne kuma ya yi saura?" Na ja tsaki mai tsananin gaske na ce "Da wa din ka shirya? Ai ni duk mutumin da zai tozarta ni, ya kuma ta'ba lafiyata da sunan duka to babu ni, babu shi har gaban abada". Na fa'da cikin matsanancin fishi. Jikinsa ya fara mutuwa. Ya numfasa ya ce "Ashe duk maganganun Dada basu shige ki ba? Daga tafiyar ta Asiya zaki fara d'aga mini hankali, mene ne nak'asuna ne da kika washe ni har hakan?" Yana rufe baki na ce"nak'asunka ai birjik ne. Mafi muni baka da kamun kai.". Ya zuba mini ido ya ce "sai me kuma Asiya?" Kai tsaye na ce "Baka burge ni ko kadan. Domin bana jin k'amshi a tare da kai. Baka iya kwalliya ba. Kullum kayan ka babu guga. Kalli faratan hannun ka. Kullum na kalle ka ba'kin ciki ne yake kama ni maimakon farin-ciki." Jikinsa ya yi sanyi kwarai da gaske. Idanuwansa suka canja launi sosai. Murya a dashe ya ce "Sai me kuma?" Na ce "Idan na tuna, na fa'da maka". Ya numfasa ya ce "Duk zan gyara indai sune cikas dina a wajen ki. Idan na sauya din shi ke nan zaki daina tsananta mini?" Na sake shan kunu ban tanka ba. Ya ce "To nima ina da damar da zan fa'di abubuwan da kike yi mini da bana sonsu?". Kamar bazan kula ba. Sai kuma na ce "Baka da damar domin ni ba so nake sai na burge ka ba. Ba kuma so nake ka zauna da ni akan dole ba. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shike nan! Amma ina ro'kon ki kada ki sake shiga mini da mata dakina". Na tunzura! Na tashi zaune sosai na galla masa harara na ce "Sannu mai d'aki. Komai dakinka, dakinka. To sai na shiga d'in. Shima ya hassala ainun ya nuna ni da yatsa ya ce "Kada ki fasa Asiya. Ai tunda na gane ba kya son sulhu da sassauci, to mu zuba tsiyatakun mu ga wa zai janye wa wani". Na ja tsaki na ce "Ai ka k'oshi shi yasa ka samu kuzarin yin musayar yawu da ni". Ya juyo a tunzure, ni kuma na zabura na yi shirin kai masa naushi. Dariya ta kama shi ya ce "Wai dambe zaki yi da ni? Ko da yake ai mai hali baya fasa wa." Na ce "oho dai." Ya fita ban sake jin sa ba, sai da asuba ya tashe ni. Da safe ba yadda bai yi ba akan na tafasa masa wani abu, duk da ya shigo da burodi a safiyar, kawai bai dame shi ba ne. Na yi tsallen bad'ake na ce bansan zancen girki ba, gara mu cigaba da zaman doya da manja kawai. Ya shiga ya tafasa farar taliya ya zuba yajin *Annur food* da manja. Ya ci ya fice bai bi ta kaina ba. Sai da na gama komai sannan na d'ora shayi. Na karya na yi wanka. Ina zaune babu wuta, kuma babu kowa. Sai da azahar sai ga y'anmata uku sun zo k'unshi. Muka shiga d'akin da ake ta mini kashedin kada na shiga na fara yi musu. Na gama wa mutum d'aya sai ga Hajiya babbar mace sosai. Dan zata haife ni. Mun saba tuntuni, wani lokacin har gidanta ina zuwa na yi mata, sanadin haka suka saba da Gwaggona. Na marabce ta da murna. Na kammala saka musu. Na kammala yiwa Hajiya a hannu. Sai ga shi ya dawo. Ban san me yasa ba, na ji faduwar gaba ainun. Wata'kila ko dan ya yi ta jaddada mini kada na shigar masa d'akin da nufin yin kunshi ne? Ya lek'o ya tabbatar ban ji maganar sa ba. Ya juya ko gaisuwarsu bai amsa ba. Ya dauko bokiti ya janyo ruwa. Hajiyar ta ce "tashi ki je ki masa sannu". Na ce To" ba dan ina so ba, na yun'kura na fita. Na gan shi ya gama cika bokitin, ya dauko na tsaya ban ce masa kanzil ba. Zuciyata ta tsinke a dalilin yanayinsa ya koma na Bulkachuwa na asali, ba na yanzu da ya koyi sassauci ba. Ya shige ni bai ko kalli inda nake ba. Ya kai ruwansa band'aki. Nima na koma na cigaba da lallena. Mintina biyar sai ga shi ya shigo d'akin babu sallamah. Y'anmatan suka fara gyare gyaren jikinsu yayin da Hajiyar ta rasa yadda zata yi a dalilin duk na yiwa hannuwanta k'unshin. Ba zato ya cire rigarsa ya mak'ale. Zuciyata ta tsinke. Wani irin abu ya tokare ni. Kafin na wartsake sai kawai ya zame dogon wandonsa, ya yi saura daga shi sai singileti da gajeran wando. Hankalina ya kai k'ololuwar tashi lokacin da ya cire singletin. Ya dauki tawul din da yake rataye ya daura a kugunsa. Ban san me ya hana shi zame gajeran wando ba. Yasa kai ya fice zuwa band'aki. Na yi kasa da kaina hawaye ya b'alle mini. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Gaba'daya y'anmatan suka bi shi da kallo. Wani irin mak'aki ya tokare ni. Na sani zai burgesu tunda Ubangiji ya masa kyakkawar sifa kwarai da gaske. Motsa jikinsa da yake yi, ya sanya jikinsa ya ginu sosai. Wanne irin wula'kanci Tijjani ya yi mini yau? Na fa'da a zuciyata. Matar ta ce "Cire mini lallen nan. Ai bansan maigidan baya so ba. Na tabbatar ba da izininsa kike wannan sana'ar ba. Shiyasa ya dauki wannan k'azamin matakin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yau na ga lukutar tsiya ni Hadiza." Ta fa'da cikin kad'uwa. Na fara kuka sosai, ina yi, ina cire mata. Ai kuwa ina gamawa ta ja ni jikinta ta mak'ure ta rufe ni da duka tana cewa "wanne irin shak'iyanci kike yi masa da ya janyo miki wannan d'anyen hukuncin. Shin baki da makusanta da suke fa'da miki gaskiya ne? Kowa ya kalle shi yasan yana tsananin son ki. Me kike yi masa?" Dama so nake na yi kukan sosai, ko na samu sau'kin zugin da kirjina yake yi mini. Dan hakan na bu'de baki na dinga canyara ihu. Ita kuwa sai dukana take tamkar ita din Gwaggo ce. Sai kuma ya fito a bazame. Dan ya ga me ya sani irin wannan kukan. Ganina a hannun Hajiyar ta matse ni tana ta mintsini na ya sanya shi ce wa "Na ha'da ki da Allah ki bar ta haka nan Hajiya, k'yale ta" Ai kuwa ta k'yale ni. Ya tsaya daga ba'kin k'ofar ya mika hannu ya d'auko jallabiyarsa da

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161