Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

TA'ADAH* *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin *Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Ina alwallah ina kuka. Ba abin da ya sake karya mini zuciya irin yadda na jiyo Baban Marina yana cewa Baba "Ni fa ki daina ro'ko na Hauwa! Tuni na yafe mata, amma walwalata ce ba zata ga ni ba, har sai ta kwantar da hankalinta an yi hidimar nan lafiya lafiya. Sannan kuma ta zauna lafiya da mijinta kamar yadda y'anuwanta suke zaune lafiya. Ina ce Ummi gidan mai iyali aka kai ta? Ga kuma mijin ya d'orawa ransa masifar son abin duniya. Ba ya sauke hakkin da shari'a ta wajabta masa. Duk k'uncin da take ciki yau shekaru kusan takwas da aurenta, bata ta'ba zuwa gabana da nufin wata matsala ko da zummar na taimake ta ba. Na sani kuma tana bu'katar a taimake ta, amma da yake ta dauko ha'kurin uwarsu ta shanye komai tana zaune da y'ay'anta, sai kuma ta yi tabarar koyon sana'a cikin cire girman kai da buri. Shiyasa ni kuma ban ta'ba yin sallah ban roka mata sassauci a wajen Ubangiji ba. Duk kuma wanda Allah ya ba shi nisan kwana zai ga yadda Allah zai albarka ci zuri'arta. Allah sai ya yi mata tukuicin hakuri da biyayyar da ta yi da ikon Allah". Da k'yar na tokara na tashi zuwa daki na tarar da Gwaggo tana share hawaye. A sanyaye na ce "Gwaggo baki huce da ni ba ne?" Ta girgiza kai sai kuma ta ce "Ina mamakin duk alherin da mace zata yiwa namiji na ha'kuri da juriya akan al'amarinsa ko na ahalinsa. Amma idan d'anta ya yi laifin da ita kanta bata sani ba sai ya shafeta. Ko sai yaushe uwa zata kubuta daga irin wannan kalubalen a k'asar hausa? Duk lalacewar uwa ba zata so d'anta ya zama marar tarbiya ba. Na sani akwai uwayen da basa son laifin ya'yansu, amma me yasa aka fi yiwa masu hakuri da kawaici raddi? Yanzu duk laifinki a kaina ya k'are. Yana wahalar gaske Babanku ya yaba ha'kurin da nake yi a gabana sai dai a bayan idona. Shikenan ita mace ba za'a yabe ta a kurzanta ta ba? Ba za'a yayata alherinta ba, amma kuskuren da ba ita ta yi shi ba ma sai an yi mata tuya a kai". Ta fa'da hawaye na sake k'wace mata. Na taya ta kukan da take yi domin na sani sanadin tafiyar da na yi ne. Da rawar murya na ce "Ki k'ara hakuri Gwaggo! Idan kika yi sa'a Ubangiji ya yabi ha'kurinki shikenan kin gama dace wa." Ta zuba mini ido sosai ta ce "Kema na hore ki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ko bana raye shine tsanin da zaki ri'ke, ki tsallake dukkan k'alubale a wannan duniyar". Jikina ya sake sanyi. Domin kalmar ko bata raye ta yi matu'kar dukana. Na ha'diye kukan na tayar da sallah. Sai dai hawaye bai yanke mini ba, na idar da sallar ina zaune ina lazimin Ya ladifu da fatan na samu sau'kin halin da nake ciki. Washagari sassafe Babah ta koma Bulkachuwa. Ala dole na ha'kura na zuba ido aka cigaba da shirin aure, wanda yake sake k'arantowa. Duk da na ha'kura amma wata irin rama nake yi mai tayar da hakankalin masu kallona. Na sake zama wata yar sumoli da ni. Ba annuri a fuskata. Na kasa yiwa jama'a kitso bare kuma lalle. Idan ba k'ure wa ta yi ba yana wahalar gaske na yi magana. Na zama very silent. Makarantar boko ma na daina zuwa duk da a shekarar k'arshe muke. Kwatsam sai ga Yaya J ya dawo daga Bauchi. Bai samu labarin aurena da Bulkachuwa ba sai a jiya. A ki'dime ya iso gidan Marina. Ya gurfana gabana Dada yana fa'din "Dada wanne irin abu ne haka? Ta ya ya za'a dauki Yabi a bawa Bulkachuwa! Saboda Allah Dada wannan daidai ne? Me yasa aka hana shi Nasiba baki tsawatar ba? Me yasa aka tirsasa ni na auri Maijidda? Akan me ita kuma za'a yi mata hakan? Ciwon abin ba shi ya yana sonta ba. Idan saboda kada na sameta ne kuka k'ulla wannan al'amarin, na sadaukar da soyayyar da nake yi mata, na janye, bazan sake furta sonta, ko a bani aurenta ba. Amma ki yiwa Àllah Dada kada ki kassara mata rayuwarta. Waye bai san BAK'AK'EN TA'ADODIN da yake yi ba? Ta ko ina basu dace da juna ba. Yabi mai son sana'a ce, yayin da Tijjani bai damu da ya gina kansa ba, irin mazan da suke barwa mace hidimar da shari'a bata dora musu ba ne. Tijjani manemin mata ne, yayin da Yabi ta kasance mai tsananin kishin gaske. Tijjani fari ne, Yabi bak'i take so. Tijjani mai zafi ne. Yabi mai tsiwa ce. Ta ina zasu ji da'din zama? Ta ina suka dace?" Kafin Dada ta ce wani abu Bulkachuwa da yake tsaye a bakin k'ofar Dada ya ce "Bamu dace da juna ba Jabir. Sai dai ka sani Ubangiji ne yake jujjuya al'amura, yake kuma k'addara afkuwar komai ko da bamu tsara faruwarsa ba. Maganganunka sun yi matu'kar ta'ba zuciyata. Tabbas gaskiya ka fa'da, duk da na ji na muzanta. Da a ce son Yabi bai yi mini kamun kazar kuku ba. Dana tirje wa aurenta. Sai dai an jarrabe ni akan ta cikin kankanin lokaci." Ya numfasa ya sake fa'din " Na gode da ka ankarar da

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161