Chapter 22
Chapter 22
guda a jikinsa. Ina fatan Ubangijinmu Allahu ya sanya mu cikin masu soyayya dan Allah. Har kuma yanzu da nake miki wannan jawabin ban cire alkalamina a cikin tawada ba. Ban cire rai cewar kaddara tana iya bani damar mallakar ki a matsayin matata ba. Ina neman alfarma, komin kankantar damar da zamu samu ta cikar burinmu kada laifin da bani na yi ba, ya shafi hakan Yabi. Ina da burin idan mun yi aure na mayar da ke makaranta ki zurfafa a ilimummuka daban daban. Amma ko yanzu ma ban fitar da rai ba, lokaci zai zo da zaki tsaya ki yi karatu tuk'uru, ki cire shiriritar da kike yi. Mu tsananta addu'a, mu barwa Allah ya yi mana zabin da ba zamu koka ba. Kin fini gaskiya duk al'amarin da babu saka albarkar iyaye to tsinannen al'amari ne. Fatan alheri gareki Yabin J". Ya fice da sauri. Jikina ya yi matu'kar sanyi, domin na tabbatar akwai abin da Yaya J ya ga ni a cikin zumuncin Gidanmu da ya warware masa duk wani confidence dinsa. Na kagu na samu labarin irin wainar da ake toyawa a gidan Marina. Na rasa yadda zan yi, domin Yaya Salisu ba mai zama ya tattauna magana da mutane ba ne. Na matsu kwarai na ga Nazira domin a bakinta zan ji komai kuma babu k'arya ko karin gishiri a cikin kalamunta. Kwanaki suka yi ta shudewa, ban samu ganin Nazira ba, ban kuma ji labarin komai ba. Abin da yake damuna daya ne takunkunmin hana ni zuwa gida da aka sanya mini. A hakan har na shafe kwanaki ashirin da biyar a gidan Yaya Salisu. Na riga na kai k'ololuwar gajiya da son jin makoma ta. Gashi ba wanda ya zo daga gidanmu. Dan ma ina samun y'an kitso da k'unshi, suna biyo ni, haka na unguwar ma suke yi mini layi. Rannan da na gaji, sai kawai na zari jiki na doshi gida a sayyadata duk da tazarar gidan Yaya Salisu zuwa Gidanmu tafiya ce mai tsayi ainun. Tunda na kusa k'arisa wa na fara jin jikina na kakkarwa, ga kuma luguden da zuciyata take yi tamkar ta faso ta fito. Bakina na ambaton sunan Allah, duk da idan ance na fa'di me nake fa'di ba zan iya tantance wa ba. Na fa'da zauren na yi kicibus da Baban Tsakiya, zai fita, da alamun rashin sukuni a tare da shi. A farko kamar ba zan gaishe shi ba. Bansan ya aka yi ba, cikin rawar murya na ce "Baban Tsakiya ina yini?" Ina daga tsaye ban rusuna ba. Ya mini dak'uwar da ta zame masa dabi'a ya ce "Baban farko ba na Tsakiya ba. Wato ke tabbataciyar yarinya ko? Sai kin ha'da da inkiya saboda ba kya mini kallon arziki.l? Zan ga mai daura miki aure, sai dai Ubanki ya waklice ki da kansa. Kuma indai ina numfashi duk wanda ya zo neman auren ki sai na fa'da masa rashin d'aarki da hatsabibanci irin na ki, domin fadar gaskiya a neman aure jihadi ne kabiran". Na yi k'asa da kaina ba tare da na ce komai ba. Ya juya ya tafi yana ta yi mini sababi da kwashe albarka da fatan tsiya iri iri. Na jingine a jinkin garun ina tambayar kaina "Wai haka kowa yake fuskantar bacin rai da danginsa ko kuwa iya ni ce? *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH*. Take na tuno Nazira bata fuskantar tsanani irin nawa a wajen Baffannin namu. Amma kuma ko ka'dan bata samun sakin fuska da alherin da suke yiwa ya'yansu. Na sake tafiya dogon tunanin yadda Baban Marina yake mua'amalantar nasu yaran. Mua'amala ce ta sassauci da ja a jika. Domin duk talaucinsa, yana k'ok'arin siyan albasa ko su mangwaro ya ce mu mika kofofinsu. Hakanan indai zai yi aski sai ya ha'da da ya'yansu an musu ya biya. Bayan nan duk wani rikicin da ya'yansu zasu rakito shine zai yi ta zarya yana bada ha'kuri har sai komai ya daidaita. Amma su ba ruwansu damu, wani ikon Allah Yaya Musa da yake a lalace sun fi sonsa, sun fi yinsa, sun fi tattalin farin-cikinsa. Na jijjiga kai a fili kuma sai na ce "Allah haska kofar Baban Marina, Allah ka jibanci al'amarinsa da na ya'yansa. Na shige cikin gida ban doshi k'ofar Dada ba. Yanayin da na tarar da Babanmu da ahalinsa ya sake sanyaya mini jiki. Na shiga bakina da sallama na isa kan tabarmar da suke zaune na tsugunna ina gaishe shi cikin girmama wa. Ba walwala Baba ya ce "Asiya me kika zo yi? Ba na ce sai na neme ki ba?" Da rawar murya na ce "A mini afuwa Baba! Na kasa jure ji daga gareku ne." A sanyaye ya ce "Na miki afuwa Yabi zo ki zauna. Da rarrafe na karisa kusa da shi a dalilin rawar da jikina yake yi ya sake ta'azzara. "Na yi godiya Baba Allah ya k'ara maka lafiya, ya shirya maka zuri'a, Allah ya mayar da ahalinka wasu masu fa'da aji". Ya yi murmushin da babu nisha'di. A sanyaye ya ce "Ameen Yabi! Duk yadda zan yi ba zan iya cire miki wannan BAK'AR TA'ADAR k'ullaci da ta shiga ranki ba. Amma abin da zan fa'da muku duk taku, duk wanda bai mutunta y'anuwana ba, to nima kar ya mutunta ni". Jikina ya yi sanyi, na yi kasa da kaina, na kasa cewa komai. "Yabi". Ya k'ira ni murya babu amo. Na amsa a hanzarce "Na'am Babanmu". Ya yi gyaran murya ya ce "Nan da kwanaki goma sha biyu auren y'anuwan ki. A duk wanda kuka taso ke da Nasiba ne kawai babu ku a cikinsu. Da gobe zan je na sanar da ke maganar a nutse cikin kwanciyar hankali. Na tura wa iyayen Abdulrashid su turo ayi magana to bansan inda aka haihu a ragaya ba, sai suka aiko mini da sun yi wa d'ansu mata tuntuni, ba da yawunsu yake neman auren y'ata ba." Jikina ya sake daukar bari a dalilin idan na fahimci maganar Babanmu kenan zan rasa Yaya J da kuma Abdul tashi guda, wannan shine biyu babu, kamun gafiyar b'aidu. Na tattaro dukkan jarumta na yafa a dukkan sassan jikina da fuskata. Na ce "Babu damuwa! Allah ya sanya alheri. Amma Baba har da Adda Nazi kenan?" Na fa'da cike da karsashi irin na tsananin karfin hali. Ya ce "Da ita Yabi, sai dai bana jin za'a yi tariya da ita, domin ban mallaki komai na aurenta ba, tunda titsiye aka yi mini." Na kalli dukkan yaran gidanmu masu hankalin suna wajen hatta Yaya Musa kuwa. Hawaye ya b'alle mini na ce "A a Babanmu da ikon Ubangiji a ranar zata tare. Na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161