Chapter 83
Chapter 83
kalle shi ba, bare nasan me yake ciki. Ga mamakina shima bai kalle ni ba, ya koma k'arshen gado ya kwanta. Washagari ma da asuba ya fice, k'ofar d'akin ya buga da k'arfi. Wanda na gane tashina ya yi dan na yi sallar asuba. Ya dawo ya ajiye burodi. Ya ha'da nasa shayin ya karya ya fice. Na yi abinci na ajiye masa na rana, amma bai dawo ba. Da yake lahadi ne. Mutum biyu sun zo lalle, haka kitso ma mutum uku na yiwa. Kafin la'asar babu kowa. Duk da zuciyata babu da'di a dalilin yadda na lura Tijjani ya tsananta fishin da yake yi. Wayata na dauka na shiga manhajar WhatsApp. Sai ganin Umm Nihla ta yi posting hadaddun materials daga Malaysia. Ina matu'kar son irin yadukan. Ba don komai ba, sai dan basu da nauyi, sannan gasu da taushi, ga kuma sau'kin ku'di ainun. Abin burgewa kuma basa kodou sai da ka gaji da su ka bayar. Wani yellow da blue suka tafi da ni. Kai tsaye na ce mata ina sonsu. Ga mamakina duk ku'din basu yi tsanani ba. Ta tambayi a wanne garin nake? Na bata amsa da Toro. Ta ce to sai a saka miki a motar Jos kenan?. Tunda kunfi kusa akan Bauchi. Na ce "A a akwai sister ta Aisha Lame jakadiyar oriflame. Ita zaki aikawa zasu same ni. Ta yi mamakin cewar nasan Aisha Lame. Na ce "To ai yar garinmu ce. Sannan muna da alaka ta wajen kakata da ta haifi Babana. Umm Nihla ta turo emojin mamaki ta ce "Ai kuwa Aisha na da kirki, kafin na bar Nigeria a wajenta nake siyayyar kayan kwalliya da spices. Farashin kayanta mai sau'ki ne ainun". Cikin alfahari na ce "Ai ko anan haka ahalinsu suke, mutane ne masu kirki kwarai da gaske. Nima da aurena ta bani kyautar fame wash. Yanzu kuwa na tura mata ku'din wani zan siya saboda na gane muhimmancinsa". Daga haka ta turo mini asusunta da zan tura ku'din. Sai mamakin yadda duniya ta samu cigaba nake yi. Ina Toro amma na sayi kaya a hannun wacce take zaune a Malaysia. Har na tura ku'din, ta tabbatar mini ta ga ni. Nima kuma ina da tabbacin zuwa gobe zan ji Aisha Lame ta karba mini. Na saki gauron numfashi. Na fara lissafin ku'dina domin so nake na yi k'undubalar fara shafa man oriflame. Idan nafi haka sheki da d'aukar ido zan fi daukar hankalin Tijjani fiye da yanzu. Haka na lalubo lambar Aisha Lame cikin sa'a tana online, ita da kanta ta za'ba mini Wanda yafi dacewa da farare. Itama take na tura mata ku'dinta. Na fa'da kuma za'a kawo mata material d'ina ta ha'do ta aiko aiko mini. Muka yi sallama. Yau ma sai bayan Isha ya dawo. Ban kula shi, shima bai kula ni ba. Kwanaki uku muna fishi da juna. Abin na cina a zuciyata, amma na daure na matse na share shi. Mussaman da bai shata mini layi da dakin sana'ata yadda yake yi a watannin baya ba. A kwana na hudu Gwaggo ta yi mini waya a lokacin ina tare da masu lalle. Muka gaisa ta ce "Yabi ba zaki zo ki gaida Dada ba ne? Kaf yaran gidan nan kowa ya zo ban da ke. Kuma kullum sai Tijjani ya zo ya duba ta. Amma daga ke har shi baku yi hankalin ki zo ki duba ta ba. Sai ta mutu ki zo gaisuwa ne?" Jikina ya yi sanyi na ce "Zan zo. Shine bai ce na zo ba". Da sauri ta ce "Ke ma k'aramab niyya ce da ke. Nasan Tijjani ba zai hana ki zuwa gaida Dada ba". A sanyaye na ce "Ki yi ha'kuri zan zo In sha Allah". Ta saki gauron numfashi ta ce "Ya dai kamata". Sannan ta kashe wayarta. Kamar almara ana idar da azahar ranar sai ya dawo. Cikin sa'a na gama yiwa wacde nake sawa. Saura mutum biyu su kuma dama sai mun yi sallah. Ban yi abinci ba tunda ba dawowa yake yi ba. Ko cefane ne idan ya kawo mini. A k'ofar gida zai bawa yaro ya shigo da shi, ya yi juyawarsa. Na bishi falon. Murya a dakushe na ce "Sannu da dawowa". Ya amsa babu walwala. Sannan ya ce "yunwa nake ji. Me kika dafa?" Na dauke kai na ce "Ban yi komai ba, tunda nasan cikina kawai zan yiwa". Shima tasa fuskar a daure ya ce "To sai ki dora yanzu. Sauri nake yi kuma". Ban ce komai ba, na juya na shiga kicin din. Na dora farin ruwa dan nasan ina da miya a fridge. Daga nan na nufi bayi dan yin alwallah. Sai da na zuba makaroni sannan na yi dakinmu dan yin sallah. Bayan na idar na shiga falon na dauko miya. Na tarar ta nuna. Na ta ce na dauraye. Na dora miyar dan ta d'umama. Na shirya a tire na kai masa. Bai nemi na zauna muci kamar yadda muka saba ba. Nima kuma ban zauna di'n ba. Na tafi na cigaba da yin lallena. Ya gama ya fita. Har dare ina ta sakar yadda za'a yi a gobe na je na gaida Dada. Muna kwnace kowa na k'arshen gado. Dukkanmu mun kasa barci da alamu akwai abin da ya damemu. Ni dai nasan yadda zan fita gobe nake ta tufka da warwara. Tsawon lokaci muna hakan. Sai kuma na ga ya mirgino ya same ni a jikin bangon da na lafe. Bai ta'ba ni ba. Amma ya mannu da ni sosai. Murya k'asa k'asa ya ce "Asiya Toro idan muna fa'da ai bai kamata mu sanya aurenmu a cikin rikicin ba. Kawai mu yi harkar aurenmu. Allah bar shi da safe muci gaba da gabarmu tunda bani da darajar da zaki mini laifi ki bani hakuri". Nan da nan na gano jarumtarsa ta kare ne. So yake mu kebe. Maimakon na yarda tunda nima na kosa da gabar sai kawai na kwabse na ce "Sawa na nawa kuma? Ai tuni ka sanya shi a ciki. Yau kwananka nawa da yin fatali da shi?" Ya ru'ko hannuna a hanzari ya ce "To yau na cire shi Asiya. Mu shiryasu kin ji. Mu din ma, ko yanzu kika bani hakuri mun shirya. Kin bata mini rai. Wai har ki ce mini zan doki aurena. Ai ban zaci har yau ba kya sona ba Asiya". Yadda ya yi maganr sai ta yi matu'kar ta'ba ni. Ban san me yasa yake yawan bani tausayi ba. Na numfasa na ce "Nima ai ka bata mini rai. Akan me zaka dinga duka na? Ko ka dinga yi mini barazana da duka. Ai na dauka ko wani ka ga zai dokar maka jikin nan nawa sai yadda karfinka ya k'are, ba wai kai da kanka ba". Da sauri ya ce "Bilhiillazi ba wanda zai doke ki a duniyar nan na bar shi ya kwashe kalau. Sai ko Gwaggo da Baban Marina. Amma kowa ye zan motsa k'wannjina a kansa. Ni kuma ai ba haka siddan nake dukan ki ba. Sai na ga zaki kuskure. Sannan kuma ai ba mai yawa nake yi ba". Na cuna baki duk da a duhu ne na ce "To ni dai bana so, ka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161