Chapter 151
Chapter 151
iren wadannan nasihohin ne suka dagargaza mini tunanim son ganin su Baban Tsakiya a halin tagayyara, na huce da su nake nema masu gafarar Ubangiji. Na gamsu idan suna cikin tozarci dole dai jininmu ne kuma gidanmu daya. Nazira akai akai take ziyarta ta. Mu yi hira, ta daho mini abinci, ko ba zata zo ba sai ta aiko mini duk da gidan namu da abinci amma kullum sai ta ciko cooler ta kawo mini. Muna hira na ce "Adda Nazi wai ya ya Saiwowin dahuwar tattabaru din nan kuwa? Ni dai na ga kyaunsu. Ya sabunta ni a wajen Baban 2 sosai". Ta ce "hm kayya bari ke dai suna da kyau. Amma maigidan ne kuzarinsa ba mai yawa ba ne. Na yi dariya na ce ke kuma babu s'auki." Ta ce ba haka ba ne". Na ce To zan karbo miki moringa tea ya dinga sha a shayi ko a lemo, zai sha?" Ta ce "zai sha ba shi da matsa akan hakan. Amma dai Yabi kada ki saka na ba shi abin da zai cutu ko ya hallaka ni" Ta ba ni dariya ainun na ce "Kai Adda Nazi. Garin zogale ne fa sai sai saiwowi marasa illah. Yana da d'an kudi amma yana da kyau ainun". Ta ce shima a kano ne?" Na ce "eh a wajen mai saiwowin ne duka daga Chad take kawosu. *08032773332*. Ta ce "Tom shi ke nan. Na gode." Sai da muka yi wata biyu. Muka koma BAUCHI. A lokacin cikin ya shiga wata na hudu. Tun ina jin kunyar Babah har na hak'ura na ware a dalilin itama mita take yi. Wai a sadda muka yi abin da muka yi, ban yi zaton zan ji kunya ba, sai yanzu? Ranar da muka je Tijjani ya fahimci ciki ne da ni har ya yi k'wari ya kasa magana ya tafi ya yi sujjud shukur. Babah ta koma gefe ta yi kamar bata wajen. Ya dinga murna da yi mini addu'a. Gabadaya na danyace. Na ciko sosai. Duk wata ko ban je gidan gwamnati ba, sai Hajiya ta kawo mini kudin envelope tare da nanata basu manta maganar maigidan ba. Karamci kad'an na yiwa Hajiya, sai ya janyo mini sanadin alheri mai yawa. Na kuma fahimci tausayina take ji da gaske. A haduwarmu Allah kad'ai yasan adadin alherin da nake samu. Su Hamim ta mayar da su tamkar jikokinta. Suna bata sha'awa. Kullum a cikin kawo musu suturu masu kyau take, ga kayan wasa kala kala. A haka rayuwar ta cigaba da garawa har na shiga watan haihuwa. A lokacin kamfani ya sake biyan kudin filin Tijjani. Na yi siyyya mai rai da lafiya amma na kudire ba zan yi Taron suna ba. Ya fad'awa Aliyu yadda za'a yi masa da kudinsa. Yaya Aliyu Kuma Bai fad'a mini yadda za'a ba, Nima ban tambaye shi ba. Bayan ya ce a ware wanda za'a yiwa Baban Marina da mahaifiyarsa hidima. Da ragowar yan'uwan. Ya ce Aliyu ya dauko 250 ya yi wani abin. Cikin ikon Allah watan Muharram da kwana bakwai na haifo yarinya sankaceciya. Jawur da ita tamkar tsada. Wanda ya yi daidai da 1 ga watan goma miladiyya. Babah ce ta karbi haihuwar domin cikin dare ciwon ya tashi. Kafin Aliyu ya zo da mota tuni na haihu ta gyara wajen. Kawai mun je asibitin ne an duba ni. A daren muka dawo gida. Babah ta zuba yarinya ido ta ce "Ke kuma Aliyu kika debo?" Na kalle ta. Domin ni fa bana gane kamar yara. Aliyu ba sosai suke kama da Bulkachuwa ba, sai dai suna yanayi saboda jini d'aya. Ihisan ce suke kama da Tijjani kwabo da kwabo shi yasa su Hanif suke matukar kama da ita. Dan idan muka hadu kowa ita yake zaton ta haife su ba ni ba. Washagari Babah ta d'auki jinjira ta kai wa Tijjani da kanta. Aliyu ne ya kaisu. Tare da su Hamin da suke murnar sun yi KANWA tamkar su mayar da ita ciki. Ya karbe ta cikin kunyar uwarsu. Ya zuba mata ido yana jin sonta da tausayinta na tsaga shi. Zata girma babu soyayyar uba alhalin ba mutuwa ya yi ba. Ya tsinci kansa da ce wa "Allah ka mini sakayya da duk wanda ya k'ulla mini sharrin da aka nesanta ni da iyalina, na kuma rasa y'ancina. Aliyu ya juya domin idonsa ya ciko da k'walla. Babah kuwa tuni take sharbe. Domin ya bata tausayi k'warai da gaske. Murya na rawa ta ce "yi mata addu'a ka kuma yi mata huduba. Ya shiga jero mata addu'oin tsari da albarkar rayuwa. Ya Kalli Aliyu ya ce dauke ta ka yi mata huduba da duk sunan da kake so." Ya saka hannu biyu ya dauke ta ya yi mata kalmar shahada ya lakaba mata Hauwa. Ya mikawa Babah ita yana fad'in sunan ki na zaba mata ". Da sauri ta ce "Ba kuwa sunana zata ci ba. A saka mata Asama'u. Don Yabi tasan mun san alheri, muna kuma gode mata.". Aliyu ya ce "Hakane Babah. Ya sake sabuwar huduba ya rad'a mata Asama'u. Maimakon ya bawa Gwaggo sai ta mika mawa Tijjani domin ta ga bai gaji da kallon ta ba. Ya ce "Aliyu rago nawa zaka yanka mata? Domin gabadaya kai ta kwaso, kamar da ta yi da kai ta shahara." Ya ce "Haka na ga ni, Babah ma ta ce ni ta kwaso. Biyu za'a yanks mata. Ana yaye ta kuwa zan dauke ta". Tijjani ya ce "Yabi kuka zata yi Aliyu. Twins ne naka. Kai na haifawa su, ga shi nan kana ta tiri tiri da su babu gajiyawa. Ko yanzu idan kana so ka wuce da su, amma wannan barta, ita ce zata debe wa Yabi kewar zaman jirana". Babah ta ce "Uhum! Nan da nan ya kame bakinsa domin ya shafa'a da ita." Sun jima kafin su tafi su bar shi cikin alhini. Yarinyar ta shiga ransa fiye da twins. Suna isa suka tarar da mutanan Toro. Gabadaya ahalin Baban Marina ne sai Dada. Da murna ta fad'i sunan jaririyaya. Kowa ya yi murna take Yaya Salamatu ta ce sai a kirata Husna. Na ce "To". Farincikin sunan Gwaggo ya zangwanyar da alhinin da nake ciki. ** Na Dade da gane Dada ba k'aramin son Bulkachuwa take yi ba. Domin sai yanzu na fahimci kafatalin jikokinta tafi sonsa. Tunda bata iya boye son tagwaye. Ni kaina na sake samun daraja ne a wajen ta saboda Tijjani. Kullum ta gan ni sai ta yi kuka. Y'aya'nsa kuwa komai hannunta ya taba sai ta basu. Tana yi tana fad'in "Allah ka yiwa mai babban suna abin da zato bai yi zatonsa ba. Wanda duk ya k'ulla masa wannan salalar tsiyar Allahu ka dabaibaye duniyarsa da firgici da tashin hankali." Kaitsaye Babah ta bawa Dada jinjira. Ta zuba mata ido tana kuka ta ce "Mai sunan manya ya haifi Aliyu. Sai na tuna ranar da aka haife shi. Haka yake sak." Aliyu da yake tsaye a bakin k'ofar ya ce "Dada ikon Allah! A gaban y'aya'na da kannena kike maganar haihuwa ta?" Ta ce "To uwaka ma bana yi zancen haihuwar ta bare kai". Ya ce "Ai shike nan, dama ni ba wai kina sona ba ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161