Chapter 101
Chapter 101
matar ta yi hakuri ta zauna da shi ko?" Ya kasa amsa mini. Na zarce da ce wa "Ana rudarku da cewa duk abin da namiji ya yi ado ne, na mace ne kaico. To ka saurare ni da kyau abin da zan fa'da ka sani sai dai zan sake yi maka matashiya ne na kuma kafa maka hujja tunda yanzu ka sanya an tursasa ni na yafe maka. Laifin namiji baligi da na mace baliga a banagaren barna duk daya ne a fuskar addini tunda duk hukunci iri d'aya Ubangiji ya zartar. Al'amari irin wannan kuma bashi ne in ji Annabin Rahma. Idan mutum ya bata y'ar wani, shima za'a bata tasa. Idan ka yi da matar wani, kai ma za'a yi da taka.! Na kaurara murya na ce "Na yarda baka yi zina ba Tijjani. Amma kana kusantar ta. Kana bin hanyar da ta bi. Ka sani kuma Allah da kansa ce wa ya yi kada mu kusance ta, ba wai kada a aika ta ba. Ina ro'kon ka, ka daina kusantar ta bare tsautsayi ya sanya ka fa'da yin ta da auren ka. Ina jin tsoro da zullumin kada na fara haihuwa a b'ata mini yara. Ina cikin fargaba kada laifin ka ya jefa ni cikin had'arin a lalata ni da aurena". Ya zabura ya ce "To y'ar sarkin mugun fata da jawo bak'in alkaba'i." Na kalle shi na ga ya shiga rud'u a dalilin furucina sosai. Kishinsa ya bani mamaki ainun. Ban ji d'ar ba na ce "Gaskiya na fa'da maka, wacce Annabi ne ya fad'a tun gabannin kakaninmu su iso duniyar. Bayan haka kuma ina son ka sani laifin da ka yi tabbas na ha'kura. Amma ina tabbatar maka idan na sake kama ka da irin wannan laifin to fa ka sani ka kuma ri'ke a zuciyar ka ba zan sake zama da kai ba Wallahi". Ya matso kusa da ni ya rungume ni sosai yana fa'din "Da ikon Ubangiji bazan sake ba Asiya. Ki taya ni addu'a. Ina kuma ro'kon ki sake hakuri, ki shafe wannan al'amarin a zuciyar ki. Wallahi summa Tallahi iya abin da ya faru ke nan, kuma a wannan ranar na ta'ba yin hakan, kada shaidan ya rinjayar miki ce war na saba yi din ne. Na kuma fahimci Ubangiji ya so ni da alheri ne shi yasa ma asirina ya tonu." Na saki ajiyar zuciya mai nauyi na ce "Shike nan Allah ya yafe mana gaba'daya." Ya sake ri'ke ni sosai yana fa'din "Na gode sosai, Allah ya sanya ki cikin bayinsa da yake kar'ba daga gare su." Hawayen da ban san dalilinsa ba ya dinga zuba mini. A hankali na ce "Ameen". Shike nan muka rufe maganar. A ranar ma mutum uku suka zo lalle amma hakuri na basu da gabatar da uzzirin ban warware ba. Domin gaba'daya na rasa karfin zuciyata. Rauni mai yawa nake jin yana bina. Sannan wata irin karaya da al'amarin Tijjani ya haifar mini da gajiya da kasala masu nauyi a zuciyata wanda gangar jikin ta rasa k'arfi da kuzari. Bai ce komai ba. Amma jikinsa shima ya mutu domin ya fahimci k'arfin halin da nake yi iya gangar jikina ne kawai. Da daddare ya ri'ke ni, ya dinga rarrashi, da ban baki irin wanda sai masanin falsafa ne zai dinga harhada kalaman masu nauyi a mizanin masalaha. Na amsa da ce wa "Na ha'kura da gaske." Ya ce "To me yasa ba zaki y lalle ba Asiya? Na sani kuma ke ma kin sani, rufin asiri ne mai yawa sana'ar taki take yiwa jama'a." Murya na rawa na ce "Zuciyata ta karye, jikina babu k'wari." Sai kuma na ke ce da kuka fiye da wadda na yi a gabansu Malam. Ya kasa ce wa komai tsawon lokaci mai yawa ina kukan, shi kuma yana shafata tamkar jinjira. Na jima ina kuka bai hana ni ba. Har sai da kukan ya tsaya cak dan kansa. Na koma ina ajiyar zuciya mai d'auke da shesshek'a. Ya sassauta murya ya ce "Kin yi kuka Asiya da ikon Ubangiji ba zaki sake kuka akan irin wannan al'amarin ba. Ki yi ha'kuri, wannan rufin asirin da kika yi mini, ni ka'dai nasan yadda na sake jin ki a raina. Ni ka'dai nasan yadda girman ki da nauyin ki suka yi mini rubdugu. Ke yarinya ce k'arama amma hankalin ki na manya ne. Kin yi k'ank'anta kin tsunduma cikin irin wannan bak'in-cikin. Ina ro'kon Ubangiji ya sanya wannan ne kukanki na karshe akan wannan matsalar a dukkan rayuwarmu gaba'daya". Na amsa da"Ameen" a hankali. Murya babu amo na ce "Bana son wannan gidan, ba zan yi farin-ciki a cikinsa ba. Ka samo mini wani ko daki daya ne zan zauna". A hankali ya ce "Da ikon Allah zan samo miki, amma ki d'aure zuwa lokaci ka'dan kin ji". Na ce "To shike nan". Ya dinga fa'din Na gode sosai my little. Allah ya bani dama da zan jiyar da ke da'di mai yawa". Na ce ni "Ka tsare mini mutuncina da naka da kuma soyayya da tattali nake so fiye da komai". Ya ce "zan miki Asiya, zan yi kokarin kiyaye ko wacce irin BAK'AR TA'ADAR da zata sanya ki kuka. Yanzu yaushe zaki fara yin k'unshin dan na tabbatar kin huce kin kuma yafe mini?" Na shagwaba na ce "Sai ka yi al'kawarin ba zaka dinga yi mini sababi akan k'aramin abu ba. Bana son shouting". Ya numfasa ya ce "Zan dinga k'ok'arin ina yin fa'dan a hankali. Amma bazan yi al'kawari ba, kin san wani lokacin ha'kurinmu k'wace wa yake yi, abin da zaki fahimta shine sab'awa a zamantakewar aure ba k'iyayya ba ce, matu'kar kuskure ne irin na zaman yau da kullum ko kuma sab'anin ra'ayi". Na ce "Tom shike nan jibi zan fara yi In sha Allah" Ya tsananta rik'on da ya yi mini yana fa'din"Thank you my little girl". Daga hakan kuma ya shiga bai baye ni da zafaffar soyayya mai goge dukkan tsatsar zuciya. Washagari muka yini cikin nutsuwa da walwala mai yawa. Tun safe kuma na yi status da cewar gobe idan Allah ya kai mu zan fara k'unshi. Shike nan na ha'kurkurtar da zuciyata na manta komai. Na rungumi mijina da sana'a ta. Illah iyaka na yanke mua'amala da Rafi'a. Mahaifiyarta kuwa ban fasa gaishe ta ba, ban fasa mutuntata ba. Illah iyaka shiga ne bana yi. Ita ma kuma Rafi'a din ta daina shigo mini. Wata biyu da faruwar hakan na fara wani irin zazzabi mai zafin gaske. Domin kwana nake yi mutsutsukun ciwon jiki. Gaba'daya ji nake tamkar ana kwankwatsa mini kasusuwan jikina. Ga bana iya cin abinci. Haka nake kwana ina yini cikin wannan halin. Sa'armu d'aya akwai kayan abinci tare da mu. Sannan yana k'ulla lallen da siyar da ruwa. Babu matsalar babu sosai a tare da mu. Kwana biyu ina ta shan maganin zazzabi da na rage rad'ad'in ciwo. Amma babu sau'ki kullum gaba ciwo yake yi. Hakan ya sanya shi fita ya yi buga bugarsa ya samo ku'di ya ha'da da wanda muke da shi, ya kai ni asibiti. Yini muka yi domin sai da aka k'ara mini ruwa. Aka yi mini gwaje gwaje. Da yamma aka sallame mu bayan sun tabbatar ina da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161