Chapter 20
Chapter 20
ce "Babanmu ne basa so fa, gara miki ma hakan, Allah ya kawo miki mafi alheri me za'a yi ma da auren dangi irin namu ne?" Mun jima sosai sannan muka tafi, bayan na bata labarin Malam Yunus da yake son Nazira. Ta yi murna, ta yi farin-ciki, ta bamu dari biyar mu hau mashin. Bayan ta bawa Nazira kaya a leda ta kaiwa Mamansu. Na koma gidan Yaya Salisu, su kuma suka wuce gida. Kwanana shida da barin gida sai ga Yaya J a gidan Yaya Salisu. A matu'kar birkice na ganshi. Ya kasa mini magana, tsawon lokaci kafin ya ce "Me yasa haka Yabi?" Ba walwala na ce "me yasa, me ke nan?" Ya ce "na dauka ko baki ha'da komai da su Baban Tsakiya ba zasu ci darajata bare kuma iyayenki ne da zasu daura miki aure". Na bata rai na ce "Bana ma bukatar su mini walittaka Jabir, domin komin kashin Babanmu da ake ga ni, Ubangiji ya azurta shi da yara mazan da zasu maye mana gurbin kowa. Kai ko ba ni da yan'uwa maza a cikin gidan Wallahi Ammar da Bulkachuwa zasu iya daura mini aure duk da kasancewarsu ya'yan mata ne, amma idan har ya kasance sai ku to lah shakka zan iya saka hula na wakilci kaina ko kuma na samu alkali ko liman". Jikinsa ya yi matu'kar yin laushi. A sanyaye ya ce "Ni yanzu mene ne laifina a nan Yabi?' Yana rufe baki na ce "Rashin biyayyar ka. Na tabbatar an fa'da maka ka kiyaye ni, domin ban cancanci ka aure ni ba, saboda mahaifina ba shi da daudar duniya". Ya yi kasa da kansa ya ce "Ni da ke muke magana ki daina sako mini manyanmu domin wannan ba dabi'a ce mai kyau ba. Na gallah masa harara na ce "Madallah" Na tsuke bakina na yi gum. Ya marairaice ya ce "Yabi kada ki bari a bada kofar da za'a yi mana farraku, ina son ki, ina kaunar kasance wa da ke, jikina na bani kamar ma na kusa barin duniyar nan, ki taushi zuciyarki kada ki zalunci wanda yake tsananin sonki Yabi. Ban miki komai ba, kada ki hukunta ni da laifin da bani na yi miki shi ba". Jikina ya yi sanyi. Na kasa magana domin gaba'daya ya d'aure ni da jijiyoyin jikina. Zufar da take karyo masa ta sanya na sake jin sonsa na taso mini. Kafin na yi magana sai kawai na tuno maganganun mahaifinsa a kaina, wai ni da nake matsayin y'arsa, yar dan-uwansa amma ya jefe ni da mafi munin kalma wai ina bin maza, ke nan karuwa ce? Bayan ga hakan kuma ya ci mutuncin mahaifina wanda wansa ne. Take na ji karshen jakanci ne na cigaba da mua'amalantar jininsa da sunan soyayya. Mussaman da ya ce yana tausayin zuri'ar da d'ansu zai kwaso musu ni. Na dago cikin karfin zuciya na ce "Jabir mu yi datse wannan soyayyar ka ji, na rantse maka tun jiya na shak'e ta, na kwashe mata karama. Babanka ya tabbatar mini Maijidda ya za'ba maka, domin ita ce arzikin ubanta yayi daidai da shi, ban yi ba'kin ciki ba, domin kullum zabin Allah muke nema. Alhamdulillah! Na karbi wannan kaddarar da hannu bibbyu, domin Ubangiji na bar wa al'amarin, ya yi mana za'bi da kansa. Amma zan roke ka Yaya Jabir ka yi iya kokarinka wajen taka burki a ta'ba mutuncin Baban Marina da ahalinsa. Ina jin tsoron kada wannan matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba. Ina jin tsoron kada a wayi gari a ga gidan Marina ya zama sansanin yaki a tsakanin jini guda". A matu'kar birkice ya ce "Allah kada ya kaddara mini ganin hakan Yabi! Ina fatan mutuwa ta riske ni kafin wannan lokacin" Na girgiza kai na ce Shi kenan". Ya marairaice ya ce "Na tsugunna miki Yabi Asiya? Ki taimake ni, ki fahimce ni, idan kin kwantar da hankalinki ai za'a a samu sulhu ta sanadin aurenmu. Sai mu kawo dai-daito, an yi abin da yafi haka muni, kuma an dawo an shirya, kada ki tsananta, ki yanke mini hukuncin da babu laifina. Allah da kansa baya kama mu da laifin iyayenmu ko na y'ay'anmu. Daure ki ji tausayina, na rantse idan kin bani ha'din kai ba abin da zai sa na bar ki komai za'a yi kuwa" . Na girgiza kai na ce "Idan na yi hakan ba sonka nake da gaske ba. A gaban iyayenmu Baban Tsakiya ya ce "Idan aka baka aurena Àllah ya isa. Baya ga hakan kuma ya tsane ni, tsanar da ya danganta ni da karuwa ce ni, kuma ya ce na zage su, hakan ya janyo ubana ya kore ni saboda shi kullum yana sonsu, yana musu kyakkawan zato". Daga haka kuma sai kuka ya subuce mini. Bai hana ni yi ba, shima kuma idonsa ya ciko jijiyar kansa ta yi rud'u rud'u tabbacin yana cikin rud'u mai girma. Da murya kuka na ce "Maijidda ta fini kyau, ta fini gata tunda Babanta mai ku'di ne, ta fini komai, ka karbi zabin iyayenka na tabbatar Ubangijin adalci zai juya maka al'amarint fiye da al'amarina, tunda ka yi biyayya. Zan fa'da maka gaskiya ko zan yaudari kowa bazan yaudare ka ba. Kana da muhimmanci a rayuwata, da gaske ina ganin mutuncin ka. Na roki arzikin ka rabu da ni, na riga na ha'kura da kai Wallahi, maganar soyayya kam ta kau". Ya numfasa ya ce "Oh! Haka kaddara ta za'ba mini? Na so ace kin saurare ni, na so ace kin bani dama mun ha'da hannu da k'arfe mun yaki wannan *BAK'AR TA'ADAR* da take neman zame wa alummarmu tamkar wutar jeji. Ina cikin zullumin yadda zumuncin yau ya koma tsakanin masu kumbar susa. Ina cikin takaicin yadda aka jahilci d'an-uba. Ina matu'kar so a ce kin zama matata ta yadda zamu kawo cigaba ta fuskar zumunci a cikin zuri'armu ta hanyar mua'amalantar kowa da girmama wa. Amma babu komai, mu ci gaba da addu'a Allah baya juyar da addu'ar masu kyakkawar manufa". Ya saka hannu ya zaro hankicif ya fara goge zufar tashin hankali da take yanko masa, kalaman sa ba k'aramin sukurkuta ni suka yi ba. Amma na yi jarumtar waske wa domin har cikin zuciyata nake jin ban cancanci na zama cikin ahalin Baban Tsakiya ba. Ya kasa cewa tsawon lokaci sannan ya yi karfin halin cewa "Fatan alheri mai yawa gare ki Yabin J". Sai ya dawo da sauri cikin rawar murya ya ce "Yanzu kin mini adalci idan kika jingina sunan ki da wani na? Yanzu kin manta komai, bani da wata alfarma a wajen ki?" Na yi kasa da kaina na ce "Alfarmomi masu yawa kuwa . "Kai na fara so, kai kawai nake yiwa uzziri da sassauci bayan iyayena, sannan idan akwai wanda na yarda da son da yake mini to kuwa kai ne. Sai dai ko kusa bazan yaudari kaina ba. Iyaye girmansu yawa ne da su, Annabi (S.A.W) ya yi ta jan hakankalinmu akan mubi su. Idan kuwa hakane zan gwada maka cikakkiyar soyayya ta hanyar dora ka akan turba sahihiya, iyayenka duka biyu basa son almarinka da ni. Dan haka ka bar son zuciyarka, ka musu biyayya, na yi imani Ubangiji ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161