Chapter 114
Chapter 114
dauki lokaci mai yawa ba, muka rabu da matsalar babu. Domin sosai yake samun ku'di tunda ba balance yake kai wa ba. Ni ce ma na koya masa dabarar ya dinga ajiye wani abu a banki saboda ko watarana motar zata bukaci gyara. Ko wata lalurar zata gitto bakatatan. Ba ja in ja ya yarda da shawara ta. Akai akai yake yiwa mahaifiyarsa da Baban Marina sako. Dada ma bai barta a baya ba. Wani lokacin idan ya je Jos sai ya tsaya ya musu alheri, sannan ya taho. Hatta su Baban Tsakiya yakan yi musu alheri kai musu kayan miya ko doya. Ku'di ne dai baya basu. Wannan rufin asirin da ya samu ya sanya masu yi masa kallon banza suka shiga nan nan da shi. Akai akai ake bugo masa waya, sabanin lokacin baya da ba'a saka shi cikin mutane bare a tuna da shi. Rannan kwatsam sai ga shi ya dawo da Nasiba tare da akwatinta shake da kayan da suke nuni zata jima tare da mu. Na gama nazarinta. Gaba'daya ta goge ta yi fes da ita. Ta cika ko ina dam tabbacin yanzu tafi samun nutsuwa. Ni ce shaida muka akan son da take yiwa Baban 2. Na ha'diye komai na yi mata uzziri tunda shi so Ubangiji ne yake kitsa shi a zukatan bayinsa. Sannan a lokacin da aka zartar da aurena da shi bata yi mini koamai ba, sai fatan alheri duk da kuwa yadda al'amarin ya buge ta. Dan haka nima a yanzu zan mata kawaici ka'dan. Amma ban da aurensa. Wannan kam bazan iya ba. Na kuma tabbatar da niyyar hakan aka turo ta. Uwarta zata yi komai dan ganin Tijjani ya aure ta ba tare da ta jin kunyar ubana ba. Ta manta yadda ta ture komai ta yi sanadin datse soyayyarsu. A yanzu kuma da ake ganin ya samu mamora shine za'a lika masa ita. Ko kunyar ha'damu kishi bata yi. Kiri-kiri take nuna mini tsana tamkar wadda agola ce ni a gidan haka take yi mini. Da daddare muna kwance gaba'daya na kasa sakin raina. Har shi ma na ji haushinsa ya turnik'e ni, akan wanne dalilin zai dauko ta tunda ga Toro su taho Bauchi? Ya kasa ha'kuri ya ce "Little wai mene ne?" Na yi masa banza. Ya tunzura ya ce "Amma dai kin san na tsani na miki magana ki share ni ko?" Na kasa bu'de baki na ce mass komai a dalilin kuka nake yi irin na sharbe. Jin shesshekar kukana ya sanya ya shiga rud'u. Ya dinga tambayar ba'asin kukan nawa. Sai da na tabbatar na rikita shi matu'ka da gaske sannan na ce masa "A kan me za'a sa ya kawo mini Nasiba gida ba tare da yarda ta ba?" A hankali ya ce "Dada ta ce na taho da ita ta mana kwana biyu. Ita ma kuma ta da'de tana fa'da mini tana son zuwa ta ga sabon gidanmu. Shine yau da ta ce zata biyo ni na ce to". Na tashi na zauna na ce "Hakan ya yi. Wato har waya kuke yi ko Tijjani?" Ya zuba mini ido sosai domin yasan tunda na gatsa sunasa gatsal to zan iya yin komai na rikici a tsakaninmu. Ya sassauta ya ce "Dan ta zo mana bakunta mene ne a ciki?" A tunzure na ce "akwai komai ma. Bana son bakuntar ta, ba kuma zata zauna mini a gida ba". Ga mamakina sai ce mini ya yi "Wai gidan na ki ne?" Na kad'u matu'ka da gaske. A matu'kar sanyaye na ce "A a naka ne mantawa na yi, amma ka tabbatar ba zan yarda da kai alhalin ina ganinku a gida daya ba." Na koma na kwanta, shi ma ya kwanta bayan ya juya mini baya da alamu ya yi matu'kar fusata da na ce Ban yarda da shi ba. Ya sani kuma ina da hujjar da zan guji zamansu a gida daya, mussaman karamin gida irin namu. Washagari muka tashi kowa na ganin laifin d'anuwan sa. Na yi matu'kar boye wa Nasiba halin da muke ciki. Tare da ita muka karya a kwano daya. Tunda shi ya fice bai saurari abincin ba. Da daddare ma hakan muka sake kwana babu jituwa. Domin nasan jira yake na ba shi hakuri, na kuma rarrashe shi. Ni kuwa al'amarin da yake cina ba k'arami ba ne. Ko magana bama yi ni da shi. Ba dan bana son ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu ba da ko dakinsa ba zan je ba. Amma ina zuwa bayan mun sha hira ni da ita. Ranar da ta yi kwanaki biyu da daddare mun kwanta. Na bu'de baki na ce "Tijjani gobe bakuwarka zata yi kwanaki uku a gidanka. A ka'idar shari'a kuma bakunta ta kwanaki uku ce. To kasan yadda zaka yi ta bar maka gidan a gobe, ko kuma ka ga abin da baka so". A tunzure ya ce ",Tun yaushe na ga abin da bana so Asiya? Ai tunda babu yarda a tsakaninmu magana ta k'are. Ba kuma zan kore ta a gidana ba. Ni da kika gan ni bana manta alheri komin tarin kalubale da rashin kirkin mutane. Dan haka komai zaki yi Bismillah". Na ce "Hakane. Madallah da Tijjani". Kasan zuciyata kuwa tamkar na tashi na cinnawa gidan wuta haka nake ji. Washa gari ya saka kai ya fice bayan ya amsa gaisuwar ta a tsaitsaye ba tare ma da ya kalle ta ba. Haka kuma yake yi mata tunda ta zo. Mun gama karyawa na kalle ta na ce "Nasiba zan je Kangire dubiya. Wata'kila na kwana, wata'kila kuma na dawo. Na tafi da yaran nan ko na bar miki su?" Zucyarta daya ta ce "Ki barsu mana indai baza su yi rikici ba. Idan suna ganin Babansu baza su yi kuka ba ai babu damuwa". Na ce "Hakane. Na shirya kayana set uku a dan k'aramin akwatina, na yi sallama bayan na yi dabarar tura tagwaye kwaso shanya a baya. Na fice a hankali, bayan na ce mata na bar ki da wahalarsu kuma". Ina jin ta tana fa'din 'yayanki ba nawa ba nawa ba ne ke nan Yabi?" Ban tsaya bata amsa ba gudun kada su fito, su ga tafiya ta. Da azahar ya koma gidan a dalilin ya dawo daga Dass. Ya tarar da yara na kukan neman Amminsu. Ya fahimci Yabi ta fice ta bar gidan babu izininsa. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi, ransa ya baci ainun. Cikin hikima ya ce "Da nasan da wuri zan dawo ai bazan bari ta fita ba.". Nasiba da take kicin ta ce "Nima da ta ce mini zata iya kwana a can na shiga zullumi." Ya mik'e ya ri'ke hannun yaran suka fita, ya rasa inda zai tsoma ransa da wannan tashin hankalin da ya kewaye shi. "Sha'anin mata yana da gigitarwa. Mene ne abin tafiya ki bar dakinki idan ba kalen masifa ba little?" Ya furta a fili a kuma ki'dime. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161