Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

daga kongo". Ba zato na ji ta gwabe mini baki. Tare da cewa "A ina kika san iskancin? A ina kika ga yana iskancin? Kinsan girman al'amarin da kike fadi kuwa?. Dan sun fito daga kongo shike nan sai ki yi shaidar zurr? Annabi ya tsananta jan kunnenmu akan shaidar zurr. Kinsan matakan da sharia ta gindaya kafin a zartar da ce wa mutum ya yi zina? Sai an ga mutum turmi da tabarya, kuma daga bakin muminai da aka gasgatasu har guda hudu. Ba dan komai ba saboda kiyaye nasaba da mutunci. Amma mutanan yau sun manta wasiyyar ma'aiki a kan kazafi da shaidar zurr. Ki kiyayi yada sharri Yabi." Na kasa ce wa komai a dalilin ba k'aramin azaba na ji ba, domin da k'arfi ta bugi bakin nawa. Ta zarce da fa'din " Àllah ka shiryi duk wanda ya kauce hanya, Allah ka shirya zuri'ar al'ummar Annabinka. Allah ka shirya Tijjani, ka bashi sana'a, ka tsare shi, ka mayar da shi nagartacce". Na amsa ameen a zuciyata, ina alkalancin maganganun Dada da na Gwaggo akan Bulkachuwa. Shike nan sai na kame bakina ban yarda na sake fa'din wannan maganar ga wani ba. A hakan har aka shafe sati dai-dai lokacin saura sati biyu aurenmu. An kawo lefen Nasiba. Lefe kuwa mai kyau, komai sai son barka, domin komin kushen mai kushe na zai kushe kayan ba. Amma gare ta babu wata murna. Dan ko dazun nan sai da na ga tana wanke wa Bulkachuwa kayansa. Ba kuma sata ya yi ba. Ajiye wa ya yi a inda ake wankin ita kuma ta jika ta wanke tare da na Dada. Kwanaki biyu a tsakani aka kawo lefena. Sun yi kokari kwarai da gaske domin duk ha'duwar kayan Nasiba, nawa sun zarta nata da ka'dan. Amma abin mamaki ahalin gidanmu basu zuzuta kayana kamar yadda aka yi ta kuranta na Nasiba ba. A lokacin kuma Dada da y'ay'anta kullum sai sun zauna, Babanmu ne kawai ba'a sa shi a cikin zaman sai Baba ta Bulkachuwa ita kuwa ba a garin take ba. Saura kwanaki goma sha biyar auren Dada ta zaunar da Babanmu. Bamu san me ta ce masa ba, amma dai mun ga ya shiga cikin rashin sukuni har washagari. Ashe ce wa ta yi auren Yabi da Nuru ba zai yiwu ba matu'kar tana da iko akansa. Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi. Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata. Dukkansu suna zaune a dakinta. Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku? Kullum da abin nake kwana, nake tashi, tare da zullumin kar'bar da zaka yiwa al'amarin. Sai kuma na tuna ikon da shari'a ta bawa uwa ". A sanyaye ya ce "Hakane". To maganar auren Yabi da wannan ba'kin yaron ba shirayayya ba ce daga Allah. Domin mai sunan manya za'a bawa ita." Wani irin zullumi ya shige shi. Murya a raunane ya ce "Dada ina ce Nasiba yake so?" Nan da nan ta ce "Nasiba ai ubanta ne ya yi iko a kanta ya ce dan k'aninsa zai bawa." Ya ce "Dada ina ro'kon arziki a ba shi wata cikin yaran Badamasi ko na Iliya tunda an riga an karbi komai na aurent a, akwai nauyi mai yawa a tsakaninmu da uban yaron nan ke ma shaida ce". Ta kai kallon ta ga Baban Tsakiya ta ga ya murtuke fuska. Nan da nan ta ce "Duk abin da yake tsakaninku da Tanimu ya kai da yar'uwar ka ne?" Da sauri ya ce "Ba kai ba Dada! Sai dai haramun ne neman aure a cikin aure." Baban kasuwa ya ce " Ai ba bisa son zuciya ba ne, biyayya ka yi, Allah kuma zai karrramaka tunda ka bi uwa. Idan ya so sai a bawa Nura Kaltume ba shike nan ba." Baban Marina ya kalli kaninsa da wani irin duba. Yana mamakin son zuciya irin tasa. Ya dauki y'arsa ya bawa Jabir yasan kuma saurayin Yabi ne. Yanzu kuma a kan idonsa yake fadin zai sake bawa Nura y'arsa tunda yasan akwai mamora a tare da yaron. A hankali ya ce "To ko zaka lamince na bawa Tijjani Kaltumen kawai?" Nan da nan ya ce "Ina! Ai ba ita Dada ta umarta ba, so ka ke na shiga fishin uwa?" "Shike nan Allah ya amsa addu'ar ka, Allah ya sanya albarka a cikin wannan ha'din , ya amintar da lamarin. Na bawa Tijjani Yabi, da dukkan zuciyata"! Baban Marina ya fa'da cikin wani irin yanayi mai ban tausayi. Dada ta ce "Allah ya yi albarka". Har ya yunkura zai tashi sai ya ce "Zan bawa shi Nuran kanwarta. Komai da suka kawo da sunan Yabi ya koma kan Ubaida". Ya fita yana ha'da hanya. A zaure suka yi kicibus da Bulkachuwa. Baban Marina ya kalle shi cikin wani irin yanayi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Dubi gashin kanka, kamar ba bahaushe ba, ka dubi wando jikinka, tamkar babu iyayenka a gidan, yaushe zaka zama cikakken mai kamala ne?" Ya sunkuyar da kai ya ce "Za'a gyara Baba" Domin kuwa da dukkan zuciyarsa yake ganin kimar Baban Marina fiye da su Baban Tsakiya. A dakin Dada kuwa Baban Kasuwa ya dinga fa'din"Dada ai da kin ce a ba shi Kaltume kawai, ina ce ta fi Ubaidan a haife?" A dan tsorace ta ce "Ga ni na yi zan takura da yawa, sannan dole hankalin mutane zai dawo kanmu". Ba shakka ya ce "To ya dawo mana! Idan ka daka ta mutane ai ko sallah ba zaka yi ba, domin kana yi suna kallon ka, ba dan su gyara maka ba, sai dan su gano na'kasunka su yi zundenka Bare kuma akan wani al'amarin duniya da bai zame komai a juya maka manufarka kyakkawa zuwa mummuna ba." A sanyaye Dada ta ce "Hakane". Suka tashi ba tare da sun so a bawa Nura Ubaida ba. Washagari sassafe Baban Marina ya zaunar da matansa ya shaida musu juyin da aka sake yi, da kuma hukuncin da ya yanke akan yin madadi da Ubaida. Daga Inna har Gwaggo abin bai musu da'di ba. Mussaman Gwaggo da take gani ita ce zata fi shiga cikin tashin hankali, domin matu'kar Yabi bata samu dacen aure ba, to komai ma zai kwace mata ne. Ga Ummi ita ma fama take a nata gidan. Shike nan a hakan zasu kare ita da y'ay'anta?. Shirun da suka yi gaba'daya shi ya sake sanyaya masa guiwa. Ya ce "Kun yi mini zuru?" Mama cikin walwala ta ce "To me zasu ce Alhaji? Y'ay'anka ne fa ka yi iko da su, sannan ba shawara ka nema ba, tunda an riga da an zartar to wace ce zata yi inkarin hukuncin Dada matu'kar tana son ka rabauta?". Maganar Mama ita ta sanya wa Gwaggo k'warin guiwa domin ta sani so take ta ganta cikin rashin sukuni da tashin hankali. Nan da nan ta ha'diye damuwarta, ta murmusa tare da ce wa"Allah ya sanya alheri da albarka, ina fatan Allah ya sa ace gara da aka yi". Wata irin nutsuwa ta zo wa Baba

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161