Chapter 67
Chapter 67
sani a gidan ubana ma ina da inda aka ware mini nake zama na yi sana'ata." Ya koma gefe ya ce "Gidan ki ne ba wai ba ne". Da rawar murya na ce "Wallahi ba nawa ba ne. Domin da nawa ne ba zaka tozarta ni irin haka akan d'aki ba." Ya nisa ya ce "Tsakanin ki da Allah sau nawa ina gargadinki akan dakin? Ai ba sana'a na hana ki ba. Dakin ne ba zai yiwu ace mata suna shigar mini ba. Tunda dai shine dakina zan yi iyakacin kokarina na ba shi kariya irin yadda ake bawa dakin mijin da yake da daraja. Ki zo ki yi anan dakin, ko a falo ba ni da matsala da hakan. Amma wancan dakin baki isa ba, ba ki biyo hanyar da zai zama k'arkashin ikon ki ba Asiya". Na ji tamkar na sharara masa mari. Amma da na tuna maganganun Hajiya. Da alwashin da ta yi na zata fa'da wa su Gwaggo halin da nake ciki. Ya sanya na ha'diye dukkan fishina na ce "Ai shike nan". Ya mik'o mini ledar awara tare da ce wa "Ga shi na san baki ci abinci ba.". Ban kula shi ba. Ya mike ya ce "Sai da safe, yau na gaji likis." Kwana na yi, ina nadamar yadda zan dawo da Tijjani dakin nan alhalin bai nuna yana son ya dawo ba". Washagari bayan na idar da sallah barci me nauyi na yi. Sai wajen goma saura na farka. Na tashi na ga ya ajiye mini burodi. Na ga kuma kusan duk kayansa har wanda ban ga ya sa ba, ya wanke su, ya shanya su a igiya reras. Ashe fitar da yake yi da asuba aiki ya samu a gidan burodi. Kullum ya je suka yi aikin kwabi da d'aure wa. Za'a bashi babban burodi d'aya da donot guda hudu, da ku'di dubu da dari biyar. Idan ya dawo kuma ya huta sai ya fita gurin aikin saka tiles ko na gyaran setlite ko had'awa. Duk abin da ya samu a ranar zai yi. Na burodin ne sau hudu a sati. Dan haka baya rasa yan k'udade hidimar yau da kullum tunda ya k'i jikinsa. Mafi yawa kullum sai ya shigo da taliya daya ko macaroni. Wani lokacin kuma magi rabin leda sai da na ga robar maggin ta sake cika duk da bamu cinye kayan abincin namu ba. Da na yi tsam sai na fahimci baya son kayan abincin su k'are ne. Shi yasa kullum sai ya siyo wani abu ya ajiye akan kayan abincin, duk da har yanzu girkinmu ba kankama ya yi ba, sai na ga dama nake dafa wa. Jiya da garin rogo ya shigo rabin kwano. Ban ce masa komai ba, da na ga ni. Amma har zuciyata na fara gamsuwa Tijjani ba zai bar ni da hidimar gidansa ba, kamar yadda ake hasashe. Sai dai bazan yi saurin shaidar hakan ba sai nan gaba. Shiru bai dawo ba, yan k'unshi suka zo. Na rasa yadda zan yi, rana ta take barandar ba zata zaunu ba tunda inuwa bata zo wajen ba. Ni kuma ina k'yashin yi a falona. Na kasa samun mafita. Kan dole na ce musu "Ba ni da lafiya bazan iya yi ba. Suka tafi suna mini fatan samun lafiya, tunda sun san ni, sun ga kuma ramar da na yi. Suna fita yana shigo wa da alamu sun yi kicibus ma. Na kalle shi na dauke kai. Ya zuba mini ido ya ce "Sai yaushe zaki fara yi mini oyoyo da barka da dawowa ne?" Na gatsina fuska na ce "Eh ai ka yi mini sallama da zaka fice, bare ka saka ran zan yi maka sannu idan ka dawo". Ya girgiza kai ya ce "kullum fa sai na yi miki sallama Asiya. Yau ma sai da na leko na ga barcin na ki ya yi nauyi. Ni kuma wai kada na katse miki shi yasa na fita. Amma ki yi ha'kuri". Na dauke kai na ce "To". Ya mik'o mini leda tare da ce wa "Ungo nasan ki da son gurjiya, ganin ta na yi manya manya da ita. Shine na siyo, na taho na kawo miki". Na kar'ba a hankali na ce "Na gode". Karon farko da na yaba masa har na yi godiya. Da'di ya kama shi ya ce "Nima na gode miki. Ko na zauna na bare miki ne?" Tausayinsa ya kama ni wanda nake kasa gane dalilin raunin da yake kama ni akan sha'aninsa. A hankali na ce "Na hutar da kai" Dadi ya sake kama shi, walwalarsa ta karu. Ya zauna kusa da ni ya ce "Fa'da mini sunan turare mai k'amshi, kuma mai sau'kin ku'di." Kamar bazan kula shi ba. Sai kuma na bu'de baki na ce Dagmar". Ya zuba mini ido sosai sannan ya ce "Na tsani turaren nan, duk yadda yake da dadi mai nutsar da zuciya Asiya. Ya mike ya girgiza kai ya ce "Na gode da wula'kanci! Ai na sha ganin kwalin turaren a dakin Jabir. Shine kike son nima na saka saboda ki dinga jin kamshinsa a tare da ni?" Ba'kin cikin da yake zuciyarsa ya kasa boyuwa. Ya juya ya bar gidan gaba'daya. Kafin na tashi, sai ga shi ya dawo ya kwashe kayansa ya shiga da su dakin ba tare da ya tsaya ninke wa ba. Ya fito a hanzarce ya fice tamkar kububuwa. Abin mamaki sai na ji babu da'di. Yadda idonsa ya canja launi duk sai na damu ainun. Ga shi ban roke ki shi ya bar ni na dinga zama a dakin da yake yi mini tijara a kansa ba. Na tashi na shiga d'akin. Na ga ya zube su akan tabarmar da take shinfide a k'asa. Kamar na ninke sai kuma na fasa. Na janyo na rufe masa. Da yamma sai ga shi ya dawo da cakwal da gawayinsa a leda. A tsakar gidan ya yi shimfida. Ya fita ban san inda ya samo rushi ba. Na ga dai ya zo ya zuba gawayi akai. Tunda ya fara gugar nan bai tashi ba, sai da ya kammala tsab. Ya kalle ni ya ce "kin dafa abincin, ko baki yi ba?" Ba walwala na ce "Na dafa". Ya ce "To a dan bani". Ya fa'da fuskarsa a tamke. Na tashi na zubo masa, na rufe sannan na kawo. A wajen ya ci. Sannan ya kwashe kayansa ya yi dakinsa da su. Zuciyata ta yi nauyi tabbacin da gaske ba zai bar mini dakin ba. Ya fito, ya shiga wanka. Ina zaune a barandar ya fito cikin farar shaddarsa wani irin kamshi sai dukan hancina yake yi. Kamshin da ban ta'ba jin irinsa ba, mai matu'kar da'di. Ya yi kyau tamkar wani hamshakin attajiri. Zuciyata ta buga da irin haduwarsa, ya taje sumar kan nasa da take cike. Gashi bai sanya hula ba. Shaddar ta gogu. Kuma babu dying tunda ya sake waccar mai cibiri cibiri lokacin bikinmu, bai sake b'ata ta ba. Ya dai tara amma babu rini ko murde wa. Na kasa gane me nake ji. Na gan shi a yadda nake son ganinsa. Bai wani tsaya ba ya ce "Sai na dawo ya fice da alama masallaci za shi. Amma ga mamakina bai dawo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161