Skip to content

Chapter 132

Chapter 132

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

ya mutu. Ya kasa ce wa uffan. Na ja tsaki mai tsananin gaske na tashi na bar masa wajen. Muka k'ulla gaba sosai. Domin ya kullaci zuwan Baban Marina da kalamansa, dazu har da shaguben laifinsa ya shafi twins a wajen Baban Marina bai kula su ba. Yana wankin kayansu yana mini azanci. Ya kuma zabe iya nasu ya bar mini nawa. Ko kallo bai ishe ni ba. Domin sosai nake jin zafinsa. Ranar da aka tabbatar mini su Baban Tsakiya sun kai masa kudin aure gidan iyayen Nasiba kwana na yi ina kuka. Sassafe na yi Bulkachuwa. Ina zuwa na sake tarar da wani abin alajabin. Fad'a kawai Babah take mini wanda babu rarrashi ko nuna soyayya a ciki. Cikin sanyi ainun ta ce "Haba kina da k'warzaba Yabi. A kanki aka fara yin kishiya ne? Tun yaushe kike jidali?. To ni bazan iya hana shi aure ba. Ni nan da kike ganina kan kishiya aka kawo ni. Mahaifiyar ki ma kan kishiyar ta zo, sannan bayan ita ma ya sake yin wata. Ina dalilin wannan kai komon da kike yi na azina?" Na kafe ta da ido na ce "Har cikin zuciyata nasan ba haka siddan kika mini hakan ba. Allah Ubangiji ya kawo karshen wannanan al'amarin." Na fada ina kuka sosai. Ina kula da yadda kukan nawa ya raunanta amma ta kasa ce wa komai. Haka na dawo Bauchi da kaina. Tare da hak'urin dole. Amma ni kad'ai nasan me nake ji a zuciyata. *Toro* Tunda a kai kudin auren Tijjani gabadaya lafiya ta yiwa Baban Marina karanci. Ba komai ke nukurkisar sa ba illah yadda babu wani mutum d'aya a gidan Marina da ya fito ya nuna rashin dacewar al'amarin. Ya kasa samun Hauwa uwar Tijjani a waya. Kowa murna yake yi da auren. Tun jinyar na sand'arsa a hankali har ta kai ya kwanta. Ba'a samu wanda ya fito ya soki al'amarin a cikin yan'uwansa ba, balle a farga da yadda bakinciki ke sakatarsa. A wannan karon dukkan juriyarsa ta k'are. Ya yi amannar yan'uwansa basa son sa da gaske. Ban da haka mene ne za'a fifita Nasiba akan Yabi da take yar gidan? A cikin wannan yanayin Babah ta Bulkachuwa ta zo garin. A dakinsa ta tarar da shi. Kallon sa kawai ta yi hawaye ya tsinke mata. Domin a cikin sati kacal tsufa ya keto masa na ban mamaki. Tausayi ya kamata, ta sani bakin cikin yadda al'amarin ya juye ne yake neman kassara shi. Mussaman yadda kowa ya koma bangaren uwar Nasiba da ta take komai ta runtse idonta. Babban abin da yake damunta bata san me yasa take jin tamkar idan ba a yi auren Nasiba da Tijjani ba zata dauma a cikin kaico. So take ta bude baki ta barranta kanta daga lamarin amma ta kasa. Murya na rawa ta ce "Sannu Yaya! Ya kalle ta da idanuwansa da suka kad'a. Murya babu amo ya ce "Hauwa Tijjani zai yi aure nan da kwanaki kad'an. Bana inkarin k'arin aurensa domin kuwa yana da sukunin da zai ajiye mace hudu ma. Amma ki sani Wallahi ba zai had'a mini y'aya'na guda biyu kishi ba. Idan har dukkan ku babu mai fitowa ya yi magana to ni na yi. Bazan yarda na mutu na bar Yabi a cikin wannan taskun ba. Domin na san kafatalin ahalin gidannan ba zata samu wanda zai mata adalci irin na uba ba. Ke nake da garantin zaki tsaya mata. To ga shi ke ma an juya miki tunani. Shin kina ganin ya dace na zuba ido ana jifanmu ni da ahalina da sihiri bayan na jure dukkan k'iyayya da warakin da na shafe lokaci mai yawa ana mini ni da zugata?" Kamar a tsaorace ta ce "A a Yaya! Ni kaina ina tambayar kaina me yasa na kasa yin magana? Me yasa nake jin tsoron yin magana? Me yasa tashi d'aya na ji soyayyar al'amarin ta shige ni fiye da komai a yanzu?" Ya jijjiga kai ya ce "Na barwa Allah ya kawo mini dauki. Abin da nake so da ke yanzu. Yau din nan ki shiga mota ki dauko mini Yabi. Saboda ke na bawa Tijjani ita. Kin sani a wanccan lokacin ba shi da rigar da za'a bashi aure, asalima hana shi ake yi gida da dawa. Ke na bawa amanarta, ke na damkawa ita a hannunki. A yau kuma ina son ki dawo mini da ita salin alin yadda na baki ita cikin girma da arziki". Ta fara kuka mai tsananin gaske. Tana fad'in "kada ka yi hakan Yaya. Daure mu bi al'amarin a nutse. Tunda har ka gano sihiri ne, ka taimake ni mu lalubo bakin zaren mana!" Ya yi shiru yana sauraren kukanta. Ya numfasa ya ce "Bayan sihiri ai kin san yadda ni da y'aya'na muka zama saniyar ware. Lokacin da Jabir yake hakilon zai had'a Yabi da Maijidda gabad'aya kowa tofin Allah tsine aka yiwa lamarin. Bansan adadin kashedin da Dada ta yi mini akan na jawa Yabi kunne ba. A gabana Badamasi yake fad'in Jabiru ba zai auri Yabi ba. Iliya kuwa shi ma ya sha fad'in "Daga ranar da aka ce Jabiru zai auri Yabi to a lokacin zai sako masa Maijidda. Amma kuma an zuba ido tare da bada goyon baya a kwace wa Yabi mijin da ba'a yarda aka bata shi ba, sai da aka tabbatar ba shi da mamora. Yanzu kuma da ya samu madogara sai aka ga yafi k'arfin ta. Tunda abin hakane sai ta fito ta basu waje. Adalcin Ubangiji ya ishi kowa. Kuka kawai take yi tana jin yadda tsoro da sanyi yake d'ada girma a zuciyarta. Murya babu amo ta ce "Dan Allah Yaya ka janye umarnin na dauko maka ita. Kasan dai yadda Ubangiji ya mutunta sha'anin aure. Ka yi hak'uri mana har muga karshen wannan waki'ar". Ya yi shiru kamar ya yarda sai kawai ta ji ya ce "Wallahi ba zai had'a su ba. P bi mini kadina. Bare ina fatan na yi tsawon rai dan kawai ran Yabi kad'ai ". Kukanta ya karu. Tana yi tana ce wa "Allah ka warware wannan dambarwar. Ubangiji ka taimaki zumuncin ka fahimtar da ni abin da yake boye. Allah na tuba astagafirillah. Ta mike ta tafi babu waiwaye. Ya bi ta da ido yana gasgata surkullen dabaibaye zuciyarta aka yi. Hawaye mai ciwo ya dinga gangarowa ta kwarmin idonsa. Gwaggo ta shiga ta tarar da shi a hakan. Ta zauna ta ce "Alhaji ba zaka karanta wa kanka damuwa ba? Ina jin tsoron kada ka hadu da ciwon nan mai shanye barin jiki". Murya a karye ya ce "Ban da darajar sallah da salati Asama'u ai da tuni zuciyata ta buga ma gabad'aya. A ce haka zan kare cikin bak'inciki da tashin hankalin cikin yan'uwana? Yanzu na rasa mutum daya da zai yuwa Yabi kara da alkunya duk cikin dangina? Tausayin yarana gabad'aya ne yake neman kassara ni. Idan na mutu haka zasu yi ta tashi fad'i babu mai tsaya musu, yanzu shi ke nan bani da wanda zai kula mini da alamarinsu ko wanda zan damk'asu a hannunsa?" *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba*

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161