Skip to content

Chapter 84

Chapter 84

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

daina". Da sauri ya ce "To. Amma kema ki daina yi mini taurin kai da rashin kunya. Idan na ce miki ya isa, ko bari. To ki bari din kawai". Ban amsa ba, amma na ji, zan kuma kiyaye. Ya nisa ya ce "To me zaki ce mini?" Na fara tirza kafa ina kukan shagwaba tare da cewa"Ai tunda ka buge mini baki shikenan an yi zuza. Kuma ba sharri na yi musu ba. Gaskiya na fa'da.". Ya ru'ko ni ya ce "Amma tunda raina ya baci, kuma har na fa'da miki ba, sai ki rarrashe ni, ki kwantar mini da hankalina ba?" Na dinga k'unk'unin ina fa'din "Ni ba wani rarrashin k'ato da zan yi". Da yake bai ji me nake fa'da ba. Ya jani jikinsa ya rungume. Ya dinga shinshinata tare da sakin maganganun masu nauyi. Ni kuma na cure jikina, na dunk'ule. Na dinga ja masa rai. Ban yarda na sallama masa ba. Sai da na ce "Yaushe zan je na gaida Dada?" Murya na rawa. Ya ce "Kina ce mini sorry gobe zan kai ki tun safe ki yini a can". Da murna na ce "idan ban ce maka ba fa." Ya ce "Zan kai ki, amma minti talatin tana cika zan tiso ki a gaba mu dawo gida". Sanin da na yi da gaske yake yi, ya sanya na bu'de baki cikin walwala na ce "Ka yi hakuri Tijjani". Nan da nan ya sake rungume ni sosai ya ce "Thats my little girl. Na huce, na kuma yafe miki. Daga Nan abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne. Domin Ni da kaina na tabbatar na yi missing Tijjani da jagwalgwalonsa masu sanya ni tsumaye. Abin da ban yi zaton zan yiwa Tijjani ba, sai da na yi masa a wannan daren. Wanda ba karamin gigita shi na yi. Da safe ya tashi ya dinga yi mini hidima da bare-bare. Ni kuma kunya ta yi mini k'awanya. Da wuri muka shirya ya kai ni gida da kansa. Ya kuma ce sai an yi sallah isha zai zo mu tafi. Sai da zamu shiga gidan ya bu'de but din mashin d'insa ya fito da lemon maltina guda biyu da lucozade shima biyu a leda. Ya mik'o mini ya ce "Ki bata". Na kar'ba tare da cewa "Na gode! Ni ban yi tunanin na siya mata komai ba". Bai ce komai ba, muka shiga gidan. Nan kuwa jakar hannuna cike take da omon viva 85kg zan bawa su Gwaggo. Da kuma alwar da zan raba wa kannena. Tare muka gurfana da shi a gaban Dada muna gaisuwa cikin tausayi da alhini. Bansan ai haka ta jigata ba. Kanta har a lokacin a suntume ya ke. Ga hannu a targade ya sha nadi da bendeji. Ga fuska da k'afafuwa duk sun kuje sosai. Duk yadda ta ji jiki, har jikin ya yi yaushi amma bakinta ras. Ta kalle ni ta ce "Ai Yabi Allah ne yasa da sauran kwana a gaba. Gaba'daya ji na yi tamkar wadda k'asa ta dare na afka. Kai wato wanda yake yawaita ro'kon Allah da neman kariya daga tsautsayi da asara zai ga sassauci a lamarinsa. Ni nasan k'addara bata sauya wa. Amma k'arfin addu'a yana rage zafinta. Na gode wa Rabbani da ya sanya ni cikin bayinsa masu yawan ambatonsa masu kuma yawan gode masa." Tijjani ya ce "Haka ne Dadarmu". Ta muskuta, na kalle ta tausayin ta ya sake kama ni a dalilin nasan bata ji dadin zaman ba. Ilai kuwa kafin na yi wani abu. Sai cewa ta yi "Mai sunan manya matso ka gyara mini zaman nawa. Gaba'daya a takure na ke." Da sauri ya matsa cancakat ya cira ta. Ya ce "Asiya sa hannu ki gyara mata zaninta". Na gyra mata din cikin azama". Ya mayar da ita ya tokare mata baya da filo mai tauri. Ta ce "Allah ya yi maka albarka mai sunan manya. Allah ya tsare ka daga tsautsayi da asara. Allah ya sa kafi karfin magauta. Ubangiji ya bu'de maka k'ofofin alheri". Ya dinga amsawa cikin walwala. Na k'ulu, wato Tijjani kawai zata yiwa addu'a. Na daure na ha'diye ban fashe ba. Can ta zuba mini ido. Sai kuma ta koma ga Tijjani ta ce "Mai sunan manya da alama komai ya dai-daita. Wannan haske da sheki da cikar da Yabi ta yi ba iya na abici ba ne kawai. Ana takar ta sosai gaba'daya ta fara bude wa" Ba ni ba, hatta shi kansa maganar ta yi masa nauyi ainun. Ya yi maza ya sunkuyar da kansa ba tare da ya ce uffan ba. Ita kuwa ko a jikinta sai faman murmushi take yi tana fa'din "Alhandulillahi. Allah kasa zan ga jininka kafin duniyata ta kare". Na mike bayan na tura mata ledar gabanta na ce "Ga shi nan Dada. Allah ya k'ara lafiya bari na tafi inda nima za'a yi nan nan da ni. Kin riga kin saba da hubbu ra'as. Tunda muka zauna ba kya ta tawa. Sai mai sunan manya, mai sunan manya. To na barku ku k'arata". Ta k'yal-k'yale da dariya bayan ta ja ledar tana ce wa "Wayyo Yabi mai dogon hannu. Da'dina da ke akwai ungo. Duk cikin jikokina na d'aki ke ce kika kawo mini tsarabar dubiya. Ko wacce da sun zo da mijinta ta ga ya bani dubu ko dari biyar shike nan sai ta ja ta tsuke. Wai suna nufin mazansu sun fanshesu. Har Nasiba haka ta zo mini hannu na dukan cinya. Ita kam mijinta bai zo ba, bare ya bani. Amma mijinki kullum ne. Sai ya kawo mini kunshin nama, ko lemo da ayaba. Ai yanzu na ga ne biki mai zuciya a ke fa'dawa ba mai dukiya ba". Na ce "Ke kuma Dada da son a baki ki ke. Ban da haka ina lafi ma da aka zo aka duba ki?" Na kalli Tijjani na ga ya kyafta mini ido, alamun na bar maganar haka". Na sanya takalmi na ce "masa na yi cikin gida. Sai ka shigo". Na tafi na bar shi tare da ita. Ina jin tana cewa "Ah yarinya ta yi bundum ta yi cikar daki. Ni dama nasan ruwan wankan aure duk zai sanya muku nutsuwa." A zaure muka yi kicibus da Yaya Anwar yayan Nasiba. Na gaishe shi da mutunta wa domin shi d'in kamamme ne. Ya amsa tare da ce wa "Yabin Bulkachuwa yau a gidan Marina? Tunda aka yi aurenku ke ce ban ga kin zo ba. Bulkachuwa ya rufe ki ruf. Ma sha Allah! Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku". Kunya ta kama ni. Na wuce ban ce komai ba. Amma sunan da ya kira ni da shi ya sanya mini wani irin shauki a zuciyata. Duk kame kamena na fara gasgata cewa na fara son Bulkachuwa. Irin son nan mai shiga a hankali ya yi karfi mai tsananin gaske. Ga shi wani irin kishinsa nake yi irin wanda ban ta'ba jin irinsa akan ko wanne namiji ba. Kawai ina waske wa ne dan kar ya fahimci halin da na ke ciki. Tunda shima na fahimci mai iyashege ne. Ina shiga k'ofarmu aka dinga yi mini oyoyo tamkar ba Yabin da kowa ya ga ji da ita ba. Hatta Mama sai da yi mini

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161