Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

domin dama uwar Yabi yake ji. Ya sani borin da Yabi zata yi ba zai yi tasiri ba tunda an yi sa'a ita din mai jin maganarsu ce mai kuma kishin kada su kunyata ne. Ya dinga yaba mata tare da sanya mata albarka. Ya juya ga amaryarsa Inna uwar Ubaida. Ya ce "Ke kuma fa?" Murya babu amo ta ce ", Allah ya sanya albarka". Ya sake numfasa wa tare da cewa"Yadda kuka kwantar mini da hankali a lokacin da aka jefa ni cikin matsanancin hali, ina rokon Ubangiji ya kewaye y'ay'anku da farin ciki da kwanciyar hankali a wannan aure. Allah ya sanya alheri mai yawa ya biyo baya. Allah ina rokon a azurtasu ta inda muka zata da ta inda bamu zata ba". Suka amsa da ameen cikin juriya. Amma Mama bata ce uffan ba. Ha'din kai da ya samu daga wajen matansa ya taimaka kwarai wajen kwantar da hankalinsa. Har dare muna namu yi, ban samu labarin komai ba. Sai dai na lura da rud'anin da Gwaggo take ciki, gaba'daya ta zama wata iri, ta yi zuruzuru. Na tambaye ta ta ce mini gudawa take yi. Take na gasgata na tura Anas ya siyo mata filagil. Da daddare bayan dare ya d'an fara tura wa Baba ya kiramu ni da Ubaida. Na cika da mamakin ha'damu da ya yi. Muna durkushe a gabansa, shi kuma yana kan kujerar ba'kin karfe irin ta da, da take dakinsa. Ya kalle ni ya ce "ku zauna sosai. Ina bu'katar hankalinku da nutsuwarku". "Muka nutsu kuwa, amma gaba'daya zuciyata ta shiga rud'ani sosai. "Shi da kansa ya jima bai iya yin maganar ba. Ya jima yana juya maganar yana tunanin ta yadda zai iya fa'dawa Yabi a karo na biyu za'a bawa wata saurayinta. Babban damuwarsa irin yadda ya ga ta sanya Nura a ranta. Ransa ya baci fiye da jiya. Ba'kin cikin y'anuwansa ya mamaye shi. Wai me ya tsare musu a wannan duniyar ne? Da k'yar ya yi k'arfin halin cewa "Yabi kinsan ce wa a duniya ba wanda zai so ki, ya so cigaban ki irin ni da gyatumarki ko?" Ba haufi na ce " "Eh Baba". Ya ce "Madallah! Sannan kuma ba wani abin kaico da zai dunfaro d'a mahaifi ya zuba ido ya cimmasa, sai idan abin ya gagare shi. Ina son ki fahimce ni, ki mini adalci, ki kuma ninka biyayyar da zaki mini a wannan karon.". Jikina ya fara tsuma, zuciyata ta shiga zullumi, idanuwa suka cika da ruwa. Na kasa bu'de baki na ce komai dan tsananin bugun da zuciyata take yi. Ya numfasa sosai ya ce "Ina son na fa'da miki auren ki da Nura ba zai yiwu ba, ba kuma na son ki kalli hakan a matsayin shirina ko shirin wani, ki yarda shirin Allah ne, shi kuwa idan Ubangiji ya jarrabe ka, ka yi ha'kuri a farkon al'amarin kana da lada da sakamako mai girma". Take ruwan da ya cika a gurbin idona ya tumbatsa ya fara zuba. Ina jin nauyin da zuciyata ta yi ba zai kwatantu ba. Wacce irin Bak'ar kaddara ce nake gudu take bina da gudu shigen na fanfalaki? Na kasa bu'de baki na ce uffan domin sai na fara hasashen mafarkin da nake yawan yi ne akan aurena da Nura zai iya ruguje wa. Jin shiruna ya sanya ya ce "Na sani kina sona, son da yake sanya ki son duk abin dana haifa, ko nake so. Ina ro'ko ki taimake ni, na yiwa mahaifiyata biyayya, ni kuma zan dauwama ina miki addu'ar wanye wa lafiya da kuma rufin asirin duniya." Cikin rishin kuka na ce "To Babanmu". Ganin irin rudin data shiga sai wata dabara ta zo masa. Sai ya ce "Babanku Iliya ya bu'kaci na bawa Nura Kaltume a madadinki". Na d'ago a matu'kar birkice na ce "Wai me na yi muku ne Baba? Yan'uwanka suna azabtar da ni, kai kuma ka zuba ido kana kallo, ka kasa kare mini darajata! Ko dai da gaske karayar arzikinka tana damfare da zuwana duniyar nan mai cike da ba'kin ciki mai tsanani?" Na fa'da ina kuka sosai. *Auzubillahi! Na yafe miki Yabi! Na sani kina cikin ki'dima ne, ni kaina da na haife ki kiris ya rage ban zautu ba a dalilin wannan al'amarin. Allah ka sassauta, Allah ka kawo mafita. Allah kada ka jarribi Yabi da jarrabawar da zata bijire mini. Bare ta haifi wanda zai bijire mata." Na yi kasa da kaina ina kuka kasa kasa. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Tsawon lokaci kafin na ce "Na ha'kura da shi Baba. Amma Wallahi indai aka ba shi Kaltume to zan roki Ubangiji ya matso mini da ajalina kusa, domin na sani bazan sake farin ciki ba. Indai kunyar Babansa kake ji, to ka bashi Ubaida tunda dama saboda kai ya turo d'ansa ya neme ni, ka bashi ita, zai fi mini sauki a maimakon ka rasa suruki nagari irinsa". Ina rufe baki kawai Babanmu ya fara hawayen da ya daskarar damu. Wanda na tabbatar na zallar ba'kin ciki da kuma farin cikin yadda nake tsananin son y'anuwana. Ai ko murya na rawa ya ce "Irin yadda kike son yan'uwanki haka nake son nawa, amma shaidan da son zuciya sun shiga cikin al'amarinmu sun yi kane kane." Ya daga kai ya ce "Allah kada ka jarrabi ya'yana da rugujewar zumunta". Jikinmu ya sake yin mugun sanyi ya ce "Ubaida kin ji me yayarki ta ce shin zaki bi bayanta wajen sadaukar da burinki, ki mini biyayyar da ke ma zan dauwama ina yi miki farar addu'a?" A sanyaye ta ce "Zan yi Baba! Na amince, da ikon Ubangiji ba zan kunyataku ba, komai zan zama kuma a duniya a sanadin auren nan, na sani arzikin Adda Yabi na ci, ba kuma zan juya wa al'amarinta baya ba". Zan yi zumunci da ita a cikin ko wanne hali da rayuwa zata wullamu". Daga hakan kuma ta fashe da kuka sosai. Wanda ita kanta bata san dalilinsa ba, amma dai tana jin na tausayin Yabi ne. Da ya rasa yadda zai fadi Tijjani ne mijin da aka zaba mata sai ya ce "Yabi ki tsananta addu'ar shiriya ga Tijjani! Ki kuma rage tsananta al'amarinsa ta yadda zaki fahimce shi da kyau, Annabi ya ce "Addu'ar miji akan matarsa karbabbiya ce, haka addu'ar mata akan mijinta karbabbiya ce. Dan haka ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, da kuma a cika kirjjnsa da soyayyar ki da tausayin ki, sannan a buda masa kofofin arziki" A ki'dime na ce "Baba dan Allah warware mini wannan curarren bayanin, d'an yi mini gwari gwari". Da matu'kar rauni ya ce "Tijjani zan aura wa ke". Ai kuwa na dage na zunduma ihu ina birgima, ina fa'din "Wayyo Allah mutuwar tsaye ta samu Yabi! Wayyo Allah nakasa ta zo mini. Yabi zata zama iyalin mai *BAK'AR

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161