Chapter 126
Chapter 126
ni da yara zuwa Kano. Ya yi mana siyayya. Muka kwana biyu, muka juyo da kaya niki- niki. Yara na baya duk barci ya sure su. Ya sassauta murya ya ce "Zan canja motar nan. Zan siyo wacce ta fita." A takaice na ce "Allah ya kara budi". Ya zarce da fad'in "Ana mini cinikin wani gida mai kyau a Toro zan siya". Nan ma a gajarce na ce "Allah ya sanya alheri." Daga haka bamu sake magana ba har muka iso Bauchi. A dalilin ya fusata duk yadda ya kwashe ni ya mini hidima bai sa na saki raina ba. Ni kuma ina masa kallon a yanzu yana ganin yafi karfina tunda yana samun duk abin da yake so. Kasuwa tana gara masa ainun. Shi yasa gabadaya yake neman bijire mini. Duk abin da yasan bana so a yanzu baya jin komai ya yi a gabana. Jiya da daddare ina jin sa a waya yana ce wa "Ga ni kike ba zan iya bata wayar ba? Wai me kika dauke ni ne? Bari ki ga na sayi gidan da zan saka.ki a ciki, ki ga yadda zan fito da maganar gabadaya. Namiji dan zai k'ara aure sai a ce ba zai iya ba? Mata nawa ne a gidansu? Nima kuma mahaifina biyu gare shi. Da ba'a karin aure da ba'a haife ni ba, tunda tawa gyatumar ce amarya a gidanmu ". Dai dai nan na fito a bandakin. Nan da nan ya katse wayar tare da ce wa "Zamu cigaba da tattauna wa da safe". Ya katse wayar tare da kashe ta gabadaya. Tun lokacin na sake karaya da shi. Tabbas aure yake nema kuma a Toro tunda har zai sayi gidan da zai saka ta a can. Sannan tun yanzu na dame ta tunda har tana masa shaguben tsorona yake ji ba zai iya aure ba. A raina na shiga yiwa mutanan da suke ganin Bulkachuwa tsorona yake ji Allah ya isa ta fi goma. Domin a yanzu da kowa yake mini kallon ina cikin rufin asiri da jin dad'i a gidansa. Ni kad'ai nasan me nake fuskanta. Nafi samun nutsuwa a lokacin da ba shi da ko sisi. A yanzu ba abin da bani da shi a gidan na cima, tunda ga kan nama, kifi, madara, dankali, doya, bare kuma kayan miya, da duk nau'in kayan abincin. Ruwa da lemo basa yanke wa. Komai baja baja yake ajiye mana. Haka sutura ta wadace ni ainun. Amma kuma bani da nutsuwar da nake da ita a da. Ba ya shiririce mini kamar lokacin baya. Dan haka sai na fi son waccar rayuwar da kowa yake mini kallon tausayi. Babah ta kawo mana ziyara. Ta dinga rarrashi tare da shan cikina akan matsalar da ta sanya bana girma, da na fara murmure wa zan sake tsomare wa. Ban yarda na ce komai ba, saboda nasan ba zata yi masa ta dad'i ba, idan ta tafi kuma ya hau sababin ina had'a shi da uwarsa duk da ba komai yake mini ba, ni ce nake zaluntarsa. Da kanta ta fahimci a yanzu ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. Gamu nan ne dai, babu warkajabi irin na da, babu nishadi a tare da mu duk da ba gaba muke yi ba. Da daddare bayan yara sun yi barci ta zaunar da mu tana bincikar matsalarmu a kokarin ta na son ta sulhunta mu ta dinke barakar da kullum take sake bunk'asa a zukatanmu ba tare da mun ankara ba. Tsawon lokaci ban iya bude baki na ce uffan ba. Ta hakura ta koma kansa. Cikin kwanciyar hankali ta tambaye shi me yake faruwa. Ai tamkar gudawa haka ya b'arke da zano laifukana. Ya kaurara murya ya ce "Gata nan gabadaya ta ki sarrafuwa mini. Ko dariya take yi da y'aya'nta idan na zauna a cikinsu ta gintse dariyar ke nan. Idan tana zaune a falo na zauna sai ta san abin da zata kirkiro da zai sa ta tashi ta bar mini wajen. Ba zan mata abu ta nuna ta ji dad'i ba, zata dai ta ce ta gode a takaice. Gabadaya ta fitini kanta ta kuma fitine ni. Gara ma da Allah yasa kika fahimci masifar da d'orawa ranta. Gata nan ta fada miki mene ne bana yi a gidan nan da zata kwarzabe mu irin haka. Yanzu idan na fita har fargabar dawo wa nake yi tsabar yadda take shagulatin bangaro da ni, da dukkan al'amarina. Ban sani ba ko miyagun kawaye suke hure mata kunne. Na tabbatar cikin da baya zama idan ta samu ma akwai dalili, idan an tsananta bincike, tunda ta riga ta taurare mini, ita tasan me take nufi da zaman". Na yi k'asa da kaina ina hawaye mai cin rai. Zuciyata tamkar ta fad'o k'asa idan yana danganta b'arin da nake yi ni ce da alhakin hakan. Babah ta dawo kaina cikin tausasa harshe ta ce "Haba Yabi me zai sa ki abin da baki yi a da ba, sai yanzu da kike girma, kuma Ubangiji yake ta yi muku Alam nasharaha. Me zai sa ki yi haka?" Na fashe da kuka mai ciwo na kasa ce wa koma a dalilin yadda nake gunji da shessheka mai nauyi. Baba ta yi zuru tana kallon yadda nake kukan. Ta koma kansa ta ce "Kai ne kake musguna mata, kai ne ka janye dukkan rarrashi da tarairaiya a tsakaninku saboda kana ganin kana ajiye mata komai na bukata." Ya yi shiru. Ta sake juyo wa gare ni ta ja ni zuwa jikinta tana bubbuga bayana cikin rarrashi. Tsawon lokaci ina kuka su kuma ba wanda ya iya ce wa komai. Sai da na yi kuka sosai, domin tsawon lokaci ina ta son na yi ban samu inda zan yi ba. Shi yasa yanzu na yi shi son raina. Sai da na nutsu sannan ta d'ago ni ta ce ",Fada mini damuwowinki Yabi". Na ce "Babu komai Babah". Na saci kallonsa na ga ya kidime sosai domin ya sani idan har na ce babu komai to kuwa abin da yake raina mai nauyi ne. Irin kukan da na yi kuma ya saka shi zullimi. Babah ta hau fad'in "Wato ban isa ba ko Yabi? Na zaunar da ku dan na ji matsalalolinku amma kin ce babu komai alhalin ko makaho idan ya ji irin kukan da kike yi yasan kina cikin bacin rai." Idona ya sake cika da hawaye na ce "Wallahi Babah ba isa ne baki yi ba, ke ma kin san yadda na dauke ki. Kawai ban san me zan ce ba ne. Abin da na fahimta kawai yanzu ya fi k'arfina ne. A yanzu ya samu damar da zai auro daidai da ra'ayinsa, irin wacce ta dace da shi. Ai dole na ga komai! Dole komai zan yi masa ya zama laifi, dole ya janye dukkan tausayi da sassauci a tsakaninmu, Tunda bana birge shi. Yana zaune da ni ne a kan dole, gane hakan da na yi ya sanya na koma gefe dan na ba shi dama ya yi komai tunda Allah ya ara masa damar." Na goge hawayen da ya zubo mini da hijabin jikina. Babah ta yi shiru tana kallonmu tare da nazari sosai. Ta kasa gane waye yafi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161