Skip to content

Chapter 146

Chapter 146

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

siya masa fiye da dozin guda duk wata. Kayan shayi da su conflakes kam ba'a maganarsu. Babah har fad'i take wai kayan suna yin yawa. Biskit irin masu dadin nan kullum na yi lalle sai na siya, kafin lokacin da zamu je, sai na yara masu yawan gaske. Sannan bana raba shi da cincin da cake. Kullum fes muke ganinsa. Illa duhu da ya yi. Amma da dukkan zuciyarsa ya karbi kaddarar da ta fad'o masa. Da wuri muke tafiya, da k'atuwar tabarmarmu. Tunda Yaya Ammar yana cikin manyan gandorurobobin kurkun bamu da matsalar komai. Domin yini muke sai yamma lis muke dawowa. Muna zaune mun gama cin abinci. Ya kalle ni ya ce "Baba lafiya bata zo ba yau?" Na yi murmushi na ce "Ta ce wai takuramu take yi, ba zata zo ba sai wani zuwan". Murya babu amo ya ce "Da ta zo abin ta." "Ni ma hakan na ce mata Wallahi". Ya kalli yaran suna can nesa damu suna kallon bishiyar mangwaro da y'aya'n suka sauko kasa kasa ana iya mika hannu a tsinko. Ya kankance murya ya ce "Little kina kewata ko?" Na yi k'asa da kai, idona ya cicciko domin babu yadda za'a yi mu zo bai mini wannan tambayar ba. Na fahimci ita ce tafi damunsa. Na kalle shi na ce "Ina kewar ka sosai Baban 2. Kullum dare idan na kalli inda kake kwanciya sai na jika filo da hawaye! Amma ina karfafa kaina guiwar cewa tunda muna shakar numfashi daya a wannan duniyar akwai lokacin da zai zo da zaka dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa. Ina kuma da tabbacin rayuwar da zamu yi zata Fi wacce muka yi a baya nutsuwa da kwanciyar hankali. Yaya Aliyu yana matukar kokari akan gidanka. Su Yaya Salisu da su Ammar suna taimaka, bamu da matsalar komai sai rashin ka." Ya ce "Ke Baki fad'o naki k'ok'arin ba little ". Na ce "Ka sha fad'a mini, ni kake da tabbacin ba zan gaji da hidimar y'aya'nka ba. So nake ka gane ba y'aya'nka ba kawai kai kanka da mahaifiyarka ba zan gaji da hidimar ku ba, muddin ina numfashi." Ya kasa magana. Sai can ya nisa ya ce "Ina son ki sosai little. Ina rok'on Ubangiji ya taya ni son ki, ya k'ara miki hak'uri da jarumta". Cikin rauni na ce "Ameen" domin ya yi matukar ba ni tausayi. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "jiya shekara ta d'aya a nan. Tunanin ki kad'ai yasa nake ganin na dade. Amma ban da hakan ba k'aramin gata aka yi mini ba. Domin tunda nake ban tab'a samun damar da nake yin ibada nake ambaton Ubangiji irin a wannan lokacin ba. Na gamsu akwia hikimar Ubangiji ta sakaye ni a nan. Ba ni kaina ba, ko ke addu'ar da nake yi miki little ta ishe ki, bare kuma y'aya'n ki. Shi yasa ban damu sosai ba, da aka kasa fitar da ni". Na ce "Allah ya karba. Ina kuma ganin tasirin addu'ar ka garemu domin bamu tozarta ba Baban 2." Ya ce "Ki tsananta addu'ar nan ta*RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Kullum ina fad'a miki tasirinta mai yawa ne". Na zuba masa ido, shi ma ya zuba mini tsawon lokaci muna kallon juna, idanuwanmu cike da k'walla. Ya yi k'arfin halin danne nasa hawayen ya hadiye. Ya ce "So nake na gan ki da ciki Little" Nasan yadda kike son haihuwa. Na kuma tabbatar renon ciki da hidimar bebi zaisa ba zaki ga nisan zaman da zan yi ba". Na ce "Ta ya ya hakan zata kasance Baban 2?" Domin ni kaina idan har zan samu cikin zan yi matukar farinciki mai yawa. Ya ce "Kina so?" Na daga kaina da sauri amma ban yarda na d'ago kaina ba. Domin haka kawai na ji kunya ta rufe ni. Ya ce "Shike nan zan roki arzikin Ammar ko zai mini alfarma". Na ce "Me zaka ce masa?" Ya ce "Zaki ji daga baya." Na d'ago na ce "Amma Baban 2 idan na samu ya bare kada ka ce na zubar maka fa, nasan halin ka". Ya dan murmusa ya ce "Ai ina fad'a miki ne dan na rama rikici da tashin hankalin da kika dinga yi mini kafin ki samu cikin twins". Na rufe idanuwana ina dariya sosai". Na ce "wanccan satin dai aka daura auren Nasiba". Ya ja tsaki ya ce "Ammar ya fad'a mini. Ya isa haka kuma". Na yi maza na sauya maganar da ce wa "Ka saurare ni da kyau Baban 2 ". Ya ce "Ina jin ki". Na ce "Jiya wata baiwar Allah ta mini waya akan gobe suna son na je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi. Na ce su saurare ni kad'an. So nake mu tattauna me zaka ce game da hakan. Na fi son na yi komai da yardar ka". Ya yi shiru. Sai kuma ya ce "Kuna da matsalar Wani ma abinci ko ma bukata ne?" Da azama na ce "Wallahi bamu da ita. Kuma Ubangiji yana kawo mini mutane har gida babu yanke wa." Ya ce "To bana son zuwan ki gidan mutane Asiya" Na zuba masa ido na ce "Bajq zuwa, ba Kuma zan je ba. Amma sai nake ganin da ka yi hak'uri na je wannan din. Domin ina son a shiga jikin matar gwamna. Watak'ila ta sanadin ta sai Ubangiji ya fito mini da kai, tunda ka hana ni dauko maka lauyoyi, ka hana ni neman taimakon manyan mutane. Ka bani dama yanzu,tunda ita mace ce kuma komai sai da sabab" Ya yi shiru. Kafin ya nisa ya ce "Tsoro nake ji Asiya. Ina jin tsoro kada ki samu dama mai yawa ki fi k'arfina ki k'asa yi mini hak'uri da kike yi yanzu" Ya fada hankalinsa a tashe ainun. Na ce "Haba mana Baban 2! Me yasa kake wasiwasi a kaina? Har duniya ta nade ni taka ce. Ina fad'a maka idan shekaru hamsin aka daure ka Wallahi zan jure na jira ka. Da bakinka ka fad'a mini akwai iyaye mata da suke sadaukar da kuruciyarsu saboda y'aya'nsu. Ashe ni baka gamsu zan yi irin wannan sadaukarwar idan kasa ta rufe maka ido ba. Tunda ga shi da ranka ma kana kallon ba zan iya sadaukar da komai saboda na reni yayanka ba." Ya girgiza kai ya ce "Ba hakan ba ne Asiya. Na sani zaki yi mini komai. Sannan ke yaranki basi yawa". Na ce "Ba yanzu ka gama mini albishir din zaka samo hanyar da zamu bi mu samo wasu yaran ba? Har na fara tunanin zan ga likita dan a d'ora ni a maganganun da zan zasu taimake ni wajen samun ciki da wuri. Ashe da wasa kake yi, ni kuma have nasa rai". Ya ce "Ba wasa nake yi ba. Na ce "To ka ba ni wannan damar. Bana son na yi abu ba tare da ka sani ba, bana son na bata maka rai Baban 2 ". Ya saki ajiyar zuciya ya ce"Shike nan. Amma tare da yara da Babah za'a dauke ku". Da sauri na ce "Dama tare da su zamu je. Na gode, Allah yasa hakan ya zame mana sanadin alheri". Ya ce "Ameen. Daga haka na shiga ba shi labarin

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161