Skip to content

Chapter 152

Chapter 152

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

. Yaya Tijjani ne na ki. Kin ga da kin bini a hankali gobe dia na zo na kai ki wajensa." Ta marairaice ta ce "A sannu ma zan bika Ali gadanga angon kilima". Ya ce "Assha kin batawa amarya ta sunanta. Amma dai zan zo, ya hau gaishe ta. Sannan suka gaisa da su Mama. Ya ce "Ummi ni da ke waye babba ne?" Ta ce "Mama fad'a masa". Mama ta ce "Ita ce babba ranar sunanta aka haife ka". Ta nuna shi da yatsa ta ce "To ka ji Wallahi ka kiyaye ni" Ya rik'e kiirji ya ce "oh saboda Ikilima zaki dinga zare mini ido? Sannu gyambo uwar son girma! Haka kike yiwa Yaya Tijjani?" Ta ce "Ai shi yayana ne kuma duk da hakan girmama ni yake kamar me saboda ya yarda surkuta gaskiya ne. Sai kawai kukan da take danne wa tunda ta ga jaririyaya ya kwace mata duk da dai wasa suke yi. Kowa ya yi k'asa da kansa ana taya ta kukan da take yi. Domin tun fil-azal idan akwai amintattun da ba cikinsu daya ba a gidan Marina to Yaya Ummi da Bulkachuwa ne. Akwai shakuwa da kauna a tsakaninsu mai yawa. A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri ummilolo! Ai yana fad'in hakan sai kuwa ta sake rushe wa da kuka na sosai. Don kuwa Bulkachuwa kad'ai yake ce mata ummilolo. Daada ma ta bare baki ta shiga taya ta suka dinga yin sa kamar me. Da k'yar suka yi shiru. Aliyu ya tafi jiki a sanyaye. Yana fad'in ba zan sake zolayar ki ba Ummi har sai d'an-uwan ki ya fito. Har dare babu nishadi a tare da mu. *Marubuciya Nazifa Nashe tana sabon littafi mai suna Gaskiyar lamari* *Ku bibiye shi , babu jira, babu nadama*. *Ku tuntube ta a wannan lambar* *08033748387*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *Tuni labarin ya fara nisa, yana kuma da dadi da darasi*. *08089965176* *07084653262* *✍️ ★ALKALAMIN JIKAR NASHE📲 *GASKIYAR LAMARI* (New Book) Wattpad @Nazeefah381. Arewabooks @nazeefah. *Kina bibiyar wannan kasaitattan labarin kuwa?* *Babu jira babu dako, domin tuni an yi nisa.* *Tuntube marubuciyaar wa wannan lambar* *08033748387* *INA MATUKAR GODIYA GA FANS DINA NA AREWA* *NA JI DAD'IN YADDA KUKA YI SUPPORTING DIN RUBUTUNA. UBANGIJI YA KARFAFE KU, YA SHIRYA ZURIARKU*. *ZAN YI KEWARKU* *GA WADANDA BASU BIBIYI LITTAFAINA NA BAYA NA, ZAN KAWO MUKU SU AREWA AKAN FARASHIN MAI SAUKI*. *Godiya kan godiya ga jama'ar what's app, mussaman wanda suka saka kudinsu suka sayi wannan labarin*. *Na gode sosai, bazan gaji da gode muku ba*. *Yabo da jinjina ga y'an special wadanda nake basu ta private, na gode da soyayyarku ga rubutuna.* Sai washagari aka hak'ura da juyayyin rashin Bulkachuwa. Dada tun asuba ta yi wankan tafiya gano shi. Tana yi tana fad'in "Allah a saukakawa wannan yaro. A jibanci lamarinsa. Ya ci arzikin ma'aiki. Ya ci albarkacim Shehu mai karama". Da wuri ya kawo Iklima. Ya ce "Dada zan dawo idan an yi azahr zan kai ki gano mai sunan manya." Ta ce "Ina ce yanzu zamu tafi Ali?" Ya ce "Ai yanzu baza su bari ma a gan shi ba." Ta kyabe baki ta ce "Ina ce Ammar yana wajen? Ni da nake da kafa har a mini iyaka?" Ya ce "Yi hak'uri, ki bari na dawo, tiyatar haihuwa zan yiwa wata mata karfe tara zan shiga." Ta rausayar da kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?" Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can. Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?" Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ". Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa. Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa. Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya Bulkachuwa sai mun sake zuwa". Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba". Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na yi azumi uku da ikon Allah". Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya. Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa. Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?" Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa". Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai". Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa komai ba?" Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?" Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161