Chapter 16
Chapter 16
cewa "Kin bar ta tafi baki bi mini kadina ba?" Na yi tsam dan na jiyo amsar Dada. Kamar ba zata tanka ba sai kuma na ji tana ce wa "Na k'i na yi mata maganar. Yar kankanuwa a gabanki, sannan kin bata kwanaki arba'in cif amma kin kasa kwatar kanki a hannunta sannan dan asaranci ki ce na tare miki fa'da? Ai kinsan fa'dan ta baya mutuwa akan me zaki tsokano abin da yafi karfinki?" Maijidda da bata yi zaton haka Dada zata ce ba, domin mun saba yin fa'da da yan k'ofarsu ta basu gaskiya ko da kuwa ni ce mai gaskiya. Dada ta ja tsaki ta ce "Sadda nake cikin shekarun kuruciyata haka nake nima duk girman mace bata bani tsoro, haka nan duk wanda ya mini kan ice sai na yi masa na kara. Sai yanzu na fahimci wannan tijarar ta Yabi sawuna ta biyo domin komin sharrin mai sharri ba zai ce ubanta mafadaci ba ne ko kuma uwarta. Dukkan iyayenta sanyin kalau ne, dan kuwa inta sune kiyama ba zata tsaya ba." Kukan Maijidda ya tsananta ta dinga yi tana ce wa "Ai dai kinsan bata isa ta kai ni k'asa ba, dunbular mini kirji ta yi ta yakushe ni a wajen." Salati Dada ta dauka tana cewa "Ikon Rabbani, tarihi na maimaita kansa ni Fadimatu. Wallahi Maijidda sadda aka mini auren fari ina kankanuwa aka kai ni babban gida, matar wan miji ta saka ni a gaba, duka, kyara zagi. Har na fara girma a cikin fargabar wannan baiwar Allah na ke. Ai kuwa da tura ta kai bango na fara rama abin da take yi mini. Har muka kai jallin da muka fara dokuwa, sai dai kashi take bani da yake ta fini sosai, ai sai kawai nake fakar ido idan muna damben ina mintsinin nonuwanta ko na na cije su. Shi kenan na yi maganin gallazawarta, ta shiga kiyayata. Yau ga Magajiyata na samu a haulata". Ta fa'da tana tafa hannu tana sake jan salati. Na wuce ina son yin dariya amma ba'kin cikin Bulkachuwa ya dabaibaye ni. Na wuce shashinmu ina jaddada wa kaina ko a gaban Baban kasuwa ne Maijidda ta tsokano ni sai mun sake cire raini, bare Dada. Bamu jima da dawowa ba sai ga mahaifiyar Maijidda da kanta ta kawo togaciya. Fadi take "Tura ta kai bango kullum Yabi sai ta yi mini sanadin bacin rai jiyan nan ma sai da ta dakar mini Kaltume akan sun samu sabani da Ismail, akan me zata tisa mini yara a gaba irin haka?" Ha'kuri kawai Gwaggo take ta bata, Inna da ta rage tsananta gaba da ni a dalilin ina yiwa yaranta hidima tamkar yan dakinmu, sannan ba mai tab'asu a waje matu'kar ina wajen sai hakan yayi tasiri, ta rage daukar zugar Mama. Dan haka sai ta ce "Ban da ke ma Abu da shiga shirgin yara ina ce Maijidda ta girmi Yabi ne? Sannan idan kinsa ha'kuri anjima ka'dan zaki iya ganinsu tare". Nan da na ta harzuka ta ce "To Yabi ni kaina ai sai ta dake ni tunda fa'dan yan- iska take yi, ban da dai ta riga ta rik'a ta yaya zata dinga dumbular kirjin y'anmata, tabbas dayan biyu ne, ko dai niyyar kisa take yi ko kuma ta shiga sahun masu *Bak'ar Ta'adar* neman mata." *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*. *07036662633*. Gwaggo ta ce "Dutse a tsakaninmu da duk masu wannan al'amarin, muna neman tsarin Allah da su, muna kuma nema musu shiriyarsa." Ta ce "ASMA'U Wallahi kin siffatu da agwagwa, ace wai baki isa ki sarrafa y'ar cikinki ba, ta gallabi kowa a gidan amma ba k'ya yi mata fa'da, saboda tana samun ku'di shiyasa ta gagareku? Sai ayi ta fankamar ku'din kitso da na lalle ne, alhalin munsan samarin da suke mata layi ne suke bata. Wallahi idan ba sa'a kika yi ba sai Yabi ta hana ki shan ruwa kamar yadda ta fitine mu". Na fito na ce "Umma ya isa haka nan, ba zai yiwu fa kizo k'ofarmu ki zagi Gwaggo ba". Ta mini dakuwa ta ce gidanku tabbataciyar yarinya marar albarka". Tana rufe baki na ce "yarinya tana bayan uwarta Wallahi, albarka kuwa da ikon Ubangiji sai na yi ta". Gwaggo ta yo kaina na ki guduwa tasan kuma matu'kar ta kawo mini duka ban gudu ba, na riga na shiga yanayin da nake bu'katar a kashe ni kawai na huta. Inna ta yi maza ta karbe itacen hannun Gwaggo tana fa'din "Wannan ai sai ki sabauta ta". Yayin da Umma Abu ta juya tana fa'din "Zaman babban gida ko masifa, ba dama a ganka da haske sai an tisa ka a gaba da ba'kin ciki da hassada tamkar dai kai ofne ka tare wa mutum nasa arzikin". Tana fita Gwaggo ta kalli inda nake a tsaye kik'am tana fa'din "Kin ji da'di ai da wannan wula'kancin da kika janyo mana". Ban ce komai ba, sannan kuma ban ji a raina cewar zan koyi ha'kurin dole idan an ta'ba ni ba. Wannan rikicin yana cikin al'amura masu tsananin gaske da ya faru. Domin da daddare babu kunya bare kawaici Baban kasuwa ya gurfanar da mahaifina a gaban Dada yana ta sababin ya gaji da yadda na takura wa ya'yansa amma ubana ya kasa tsawatarwa. Da yake Dada bata iya tsallake umarninsa sai kuwa tabi bayansa. Ta dinga fa'din ai tsoron zuciyata yake yi. Cikin rishin kuka Baban kasuwa ya ce "Ki gafarce ni Dada! Wani satin zan koma gidana dana kammala gina wa tun bara, amma na kasa tashi saboda ke, to yanzu kam zan tashi na gaji da wannan masifar Wallahi". Dada ta ce "Wallahi ko ubanta ba zai tashe ka ba tunda matsayinku guda a cikin gidan bare kuma ita. Share hawayenka ita ce zata bar mini gidan". Na sake kasa kunne domin tunda aka aiko cewar Babanmu ya zo in ji Dada nasan karata za'a kai sai na bi bayansa ba tare da yasan ina binsa ba. Na makale a soron Dada ina addu'ar kada Allah ya kawo Bulkachuwa tunda dakinsa a cikin soron yake. Ta ce "ka fa'dawa Yabi ta tsayar da miji da dukkan yaran ma. Na umarce ku, ku aurar da su nan da watanni biyu". Baban kasuwa ya ce "Shi kenan" Ya fice ya barta da Babanmu." Ganin zai fito ya gan ni sai na yi maza na fice daga soron na tsaya a bakin k'ofar shashinmu. Ya zo wuce wa ya dallaro mini ido da sabuwar tocilayit dinsa da alamu suka nuna yau ya zuba mata sabbin batira saboda tsananin hasken ta. Na dauke kai tare da saka hannunwana na rufe fuskata dan rage wa kaina kaifin hasken da ya dauke mini ido. Takaicin rashin gaishe shi ya sanya ya ce "Asiya ce?" Na dauke kai a shak'e na ce "Yabi ce?" Ya kuwa bu'de murya ya ce "Ja'irar yarinya mai mugun y'anci dama nasan ke ce zaki gan ni ki mini irin wannan iyashegen. Na ce ba, zaki yiwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161