Skip to content

Chapter 100

Chapter 100

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

nake so wacce bata san namiji ba sai a kaina tamkar yadda na same ki". Maimakon na ji da'di sai na sake shiga rud'u. Da rawar murya na ce "ka tabbatar ba budurwa ba ce? Ashe ba iya abin da na ga ni ya gitta a tsakaninka da ita ba kenan?" Cikin ido ya kalle ni da dukkanin gaskiyar sa ya ce "Na rantse iya abin da ya faru kenan. Amma kuma duk macen da bata san namiji ba ai ba zata dinga shige masa ba. Ba ni na je inda take ba, ita ta kawo kanta. Ko da ina son na ta'ba ta sai amince, kin ga ni kuma ba dole na yi mata ba, da son ranta ne, na tabbatar bani ka'dai ta ke yiwa hakan ba, ba ni ka'dai take sakarwa ba. Dan haka ina cikin nutsuwata bazan auri shasha ballagaza ba". Y'anmata kalubalenku abin da mijin Yabi ya fa'da shine gaskiyar magana, saurayin nan da kike amince yake ta'ba ki ba zai aure ki ba, sai tsananin rabo. Idan rabon auren ya rantse kuwa har ki tsufa a hannunsa ba zaki fita daga zargi da wula'kancinsa ba. Ba shakka wayewar da ta sanya kika bar shi yake lalube ki, to shifa a ballagaza wacce ta saba cudanya da maza daban daban yake miki kallo. Sannan ticket din kaskanci kika yankarwa kanki. Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali ya yi wanka. *Cikakken labarin zai fara zuwa muku ranar 09/09 wanda a wannan ranar mahaifiyata zata cika shekaru ashirin da uku da barin duniyar nan*. *Dan haka zan yi amfani da wnanan damar dan ku taya ni mika mata addu'oin gafara da rabauta a wajen Ubangiji*. *Na gode sosai Ubangiji ya saka muku da alheri bisa soyayyar da kuke yiwa rubutuna*. *VIP 1K* *REGULAR 500* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM* *ZENITH BANK.* *A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08032773332 KO KUMA 09069067488* *NA GODE SOSAI* ✍️. *ANTI KULSUM BAUCHI HOW FAR?🥰* *KIN TUNA RANAR DA NA CE MIKI INA RUBUTU?😄* 67&68. Na daskare a zaune, wato duk tantirancin namiji shi kamila yake so. Duk yadda zaki sadaukar masa da komai da sunan soyayya shi fa a zuciyarsa ba haka ba ne. A yau na k'ara fahimtar darasin rayuwa. Na kuma k'ara gode wa Allah da na tsallake sirad'in yanmatanci lafiya. Na kalle shi cikin tu'ajjibi na ce "To ka sani Wallahi bazan zauna a cikin gidan nan ba. Matu'kar kana son kwanciyar hankali da walwala to kuwa bana son gidan, ba kuma zan zauna a cikinsa ba." A rikice ya ce "Asiya kin san dai da yadda aka biya ku'din rabin shekara yanzu wata guda tal muka yi, ta ina zan fara neman wani gidan?" Ido cikin ido na ce "koma ta ina ne, na baka nan da sati if not Bilhiillazi bazan ha'kura ba. Sai dai ka nemi ni ka rasa shike nan sai ta tattaro ta maye maka gurbina." Ya yi muk'us ya kasa zaburo mini. Ya nisa ya ce "Haba little nan da sati me zan yi na samo ku'di? Kin san dai ba dawo mini da kudin zasu yi ba, bare na kama wani". Na ce "Sai na baka aro, ka karbi zobena ko dan kunne ka siyar, sai ka biya ni idan ka samu hali". Ban san ya aka yi ba kawai ya fara nuna ni da yatsansa cikin sababi yana fa'din "Nafi karfin ki kama gida na zauna a ciki Asiya. Ba zan yi wannan lalacewar ba, har abada da ikon Allah." Na kafe shi da ido tsawon lokaci har ya fara kame kame. Na nisa na ce "Tijjani ni kake yiwa wannnan shouting din?". Na girgiza kai na ce "Ba laifin ka ba ne. Laifina ne da na yarda da afuwar da Malam ya yi maka ba tare da na bayyana tozarta ni da ka yi ba. Afuwar da aka tilasta ni na yi maka ne ya baka kuzarin yi mini sababi irin haka ko? To Wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Komai za'a yi da ni kuwa". Na mik'e na bar shi, ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi. Domin ya ga na koma Yabin Marina marar sassauci. Ban jima da shiga d'akin ba sai ga shi ya biyo ni jikinsa a sanyaye. Ya zauna kusa da ni ya tausasa harshe ya ce "Ke little ba ki fahimce ni ba ne. Ki yi hakuri, zamu tashi, amma pls ba nan da sati daya ba dan Allah." Na ce "To". Ai kuwa nan da nan ya hau fa'din "Na rok'e ki fa Little. Ban son irin wannan to din na ki". Na share shi. Ya dinga jaye-jayen magana amma ban tanka masa ba. Sai kuma ya bani tausayi yadda ya yi shiru ya rasa abin yi. A zuciyata sai hango girman gatan da Ubangiji ya yiwa mazaje nake yi. Domin duk girman laifin da zasu yi wa mace sai Ubangiji ya sanya hakuri da sassauci had'i da rauni a zukatan mataye. Nan da nan mace zata yafe ta kuma manta musganwar miji. Na tuna ranar da ya rufe mini gida dan kawai na je na na yi sana'ar da zan samo masa ku'din da zamu rufa asirinmu. Amma har washagari yana sababin sai na tafi gida. Amma ni na fita unguwa na dawo na tarar yana shek'a ayarsa. Na girgiza kai domin nasan da ace ni ya ga ni a cinyar Yaya J sai ya masa dukan mutuwa tunda ba k'arfinsu daya ba. Ni kuwa zai yi wahalar gaske idan bai sallama ni ba. Na kalle shi na ce "Na tambaye ka?" Ya d'aga mini kai tabbacin eh. A hankali na ce "Idan ni ka ga ni a cinyar wanin ka ya zaka ji?" Ya ce "Wata'kila zuciyata bugawa zata yi, wata'kila kuma na had'u da mummunan hawan jinin da zai kanannad'e ni." Na sake zuba masa ido na ce "Amma me yasa baka yi zaton nima sakamakon hakan zai iya samu na a dalilin ganin wata a jikin ka ba?" Ya fara sosa k'eya. Da k'yar ya ce "Ban san ya aka yi hakan ta faru ba. Ni gaba'daya am upset ma". Na girgiza kai na ce "Hmmm". Muka yi shiru sai kuma na ce "Kuma zaka zauna da ni idan ka gan ni a irin yanayin da na gan ka?" Ba ja in ja ya ce "Ba zan iya ba". Na zuba masa ido ina masa kallo mai tsananin gaske. Na kaurara murya na ce "Amma kuwa son zuciyar ka azimin ne Tijjani." Bai yi inkari ba. Bai ce komai ba, na kuma tabbatar da dukkan zuciyarsa ya bani amsar. Kamar daga sama sai na ji ya ce "Mace daraja ne da ita sai wacce ta wula'kanta kanta. Duk matar auren da zata bada k'ofar da wani namijin zai mata waya, ko doguwar gaisuwa dama ai ba kamammiya ba ce. Ba kuma yadda za'a yi mijinta ya gasgata ta. Bare kuma a ce har ya ga ni da idanuwansa, tabbas ba zai zauna da ita ba, ko kuma idan ya ri'ke ta din ma bisa wani dalilin to fa har abada ba zata ji dadinsa ba." Na sassauta na ce "Amma shi namiji idan yana sharholiyarsa ko da kuwa a cikin gidan aurensa ne dole ne

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161