Chapter 110
Chapter 110
zaki ji kunyar abin da kika yi". A hassale na ce ",To mene ne zaka tayar a gabanta? Gaskiya kada ka sake yi mini irin haka. Idan kuwa ba hakan ba kasan kai ma ka mini laifin da ban ta'ba bude wa an ji ba". Nan da nan ya shiga nutsuwarsa ya ce "Ai ni ba da bacin rai na fa'di hakan ba. Amma ba zan sake ba, mu rufe maganar haka nan. Na girgiza kai na juyar da fuskata gefe. Ya shiga kiran sunana a hankali, na ki juyowa. Ya diririce. Ya ce "Asiya wasa fa nake yi miki. Me zai sa mu yi fa'da a gaban Babah". Na ce "Ai so kake ka bakanta ni a wajen ta, shi yasa ka dauko wannan maganar". Ya marairaice ya ce "Billahillazi ba hakan ba ne. Gaba'daya ya rikice jin na lauya magana zan tado da tashin hankali. Ya dinga lallaba ni da son sai na dawo da walwala ta. Ni kuma ina sane na yi masa hakan. Bamu bar garin Bulkachuwa ba sai da muka shafe sati biyu. Da zamu tafi, tamkar wanda muka je fatauci saboda kayan da muka samu. Lafiya k'alau muka isa Toro. Kwana biyu a tsakani ya koma Bauchi. Kwatsam aka tashi da mutuwar mijin Nasiba. Wannan mutuwa ta bigemu, domin babu jinya sai mutuwa. Ashe kasurgumin dan shaye shaye ne. Can wajen sharholiyarsu rikici ya kaure tsakaninsa da abokinsa ai kuwa ya daba masa kwalbar a kahon zuci ya mutu a wajen nan take. Gaba'daya maganar ta cika Toro da kewaye. Na tausayawa Nasiba kwarai da gaske, duk da dama ba zaman dadi take yi da shi ba. Duk cikinmu ita ce bata samu sukuni a gidan aurenta ba. Yaranta biyu Muhsin, da kuma Maryam da bata fi watanni shida da haihuwa ba. *Watanni bakwai a gaba* Zuwa wannan lokacin mun koma Bauchi da zama. A satin nan kuma na yaye yara. Bulkachuwa aka kaiwa Babah su. Kwance nake ina fama da zazzabin da ciwon nono ya zuba mini. Ga kewar yara, abin sai ya hadu ya kwantar da ni. Nasan Hanif ba shi da matsala, amma Hamim kam sai Allah. Rashinsa ya fi takura ni. Tijjani kuwa sai tsokana ta yake da fa'din Hanif ne kawai zai dawo, Hamim ya zama dan Bulkachuwa. Bana ce wa komai amma na sani zolaya ta yake yi. Sai da na sha allurai sannan na warware. Sannu a hankali na shiga saboggina tunda anan Bauchi ma na fara sanuwa a wajen k'unshi da kitso, sai dai ba kaman Toro ba. Matsakaicin gida ya kama, cikin madaidaiciyar unguwa. Cikin nutsuwa da rufin asiri mukr rayuwarmu. Har yau din nan Bulkachuwa tattala ni yake yi. Baya kaunar abin da zai ha'damu rikici sai dole. Baya mini fishin da ya wuce na kwana d'aya. Ni ce dai nake jarumtar share shi na lokaci mai yawa. Duk da ni din ma karfin hali nake yi. Yanzu haka Tijjani yana da nasa teburin a cikin kasuwar ma'ana ba k'arkashin Alhaji yake ba. Watanni uku ya karbi ku'dina ya mallaki wajen flda zai ajiye teburinsa. Zobena daya muka siyar. Yanzu haka jiya ya kai ni na zabi wanda nake so ya siya mini a madadin nawa. Na sani ba dan ya samu damar biyan ba ne, sai dan yana son ya biya ni ne. Hakan kuma bai sa sun rabu da Alhaji Auta ba. Ana cikin haka guda cikin kamfanin sadarwa ya nemi kafa turakan ayyuknasu cikin unguwar da filin Tijjani yake. Gaba'daya mutanan da suke da fili a wajen kowa fata yake a ce su karbi nasa, tunda haya zasu kar'ba. Alhaji Auta har addu'a ya baza a yi masa ko ya samu ya d'an farfado. Kamfani har yanzu zagaye yake tare da wakilinsu da suka san ilimin kimiyya suna ta auna inda zasu fi samun sabis. Gaba'daya Tijjani bai sa hankalinsa a wajen ba. Gara ma jiya ya ce mini ku'din da mutum zai samu a shekara d'aya kacal ba k'ananu ba ne. Ina bu'de baki na ce "Idan akwai alheri a cikin samun da za'a yi, Allah ya saukar a kan filinmu". Ya ce "Kayya! Amma tunda Allah kika ce ai magana ta k'are. Ameen". Muka bar magana a hakan. A wannan tsukun auren su Yaya Ammar da na Yaya Rabiu da su Kaltume ya zo. Muka shirya muka tafi tare. A can muka tarar da Babah da y'an yayenta. Hamim na ganina ya cakume ni, ya cukuikuiye hijabina wai bazan gudu na bar shi ba. Hanif kuwa kawai kwantar da kansa ya yi a jikina. Tijjani ya kalle shi ya ce "Kai ma ka bi bayan d'anuwan ka, baka ta tawa ko?" Ya kalle shi kawai. Ya yafice shi tare da ce wa "zo mana Babana". Ya kuwa isa gare shi ya kwanta. Yayin da Hamim ya rikice sai ya sha nono. Da k'yar Tijjani ya yane shi suka fice. Babah ta ce "Ai ban yi zaton darun d'anuwana ya kai haka ba sai yanzu". Na ce "Ai ba shi da sau'ki Babah. Hanif ya fi sassauci". Ta ce "Babu hadi ma. Allah ya musu albarka ya tsare su. Ki yawaita yi musu addu'ar tsari da kuma kambun baka". Cikin na ce "To". Duk inda na shiga sai an kalle ni. Da na juya baya za a hau zancena. Haka Ikilima ta jiyo mini gulmar da sa'anina da muka taso tare su Saratu su Maijida. Suna fa'din ",Ai gaba'daya Bulkachuwa tsorona yake ji saboda ina da ku'di. Duk kafafar da nake yi da burgar kwalliya da yadikan yan gayu na Umm Nihla collection. Ni nake yiwa kaina ba shi ba ne. Su kuwa sun gode Allah mazajensu ne suke dawainiya da su yadda Allah ya hukunta. Barin Maijidda da a yanzu suke Kaduna. A dalilin Yaya J ya samu aiki a kwalejin kimiyya ta kaduna(Kad-poly). Gaskiya ne duk ta fimu d'aukar ido. Amma kuma ba wai ta fi kowa kwanciyar hankali ba ne. Ko wacce ita tasan yadda take zaune a gidanta. Nasiba tuni ta sake dawowa gidanmu gaban Dada. A yanzu da bata da aure ma tafi walwala da kwanciyar hankali. Tunda yayanta Ammar na kula da ita daidai gwagwado. Sannan iyayen mijinta suna ri'ke da Muhsin cikin kulawa, Maryam din da take shan nono ma sukan yi mata aike lokaci zuwa lokaci. Gaba'daya ta murmure ta dawo da jikinta da ta rasa a baya. Sai daga baya aka gane komai na d'akinta ashe ya siyar tunda mashayi ne kuma dan caca. Da ace wata a k'ofarmu hakan ta same ta da anyi yamididin halin d atake ciki. Amma wannan shiru ake ji. Tallafin da take samu ya sanya take figa take yin y'an sitturu da kayan kwalliya dan haka fes take bata da makusa. Na yi tsuka na ce "Basu da abin yi ne, koma a ya ya na ke rayuwa ai babu ruwansu, tagayyara da ake mana fata kuwa ba zamu shige ta ba in sha Allah." Amma a tunzure nake kwarai da Maijidda. Na kuma ku'dire indai ta sake ta mini maganganun banza yadda ta saba yi mini, idan mun hadu a taro, to a wannan karon zamu sake gwada yar kwanji dan na tuna mata baya. Ta fitine ni da yawa. Nazira da take gefe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161