Skip to content

Chapter 150

Chapter 150

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

Kamar jira jikina yake na zo Toro ai sai kawai na hau wani irin zazzafan zazzabi. Hak'ora na har kad'uwa suke yi. Ga azabar ciwon k'asusuwa. Sai na ji tamkar ana kwankwatsa mini jikina. Kullum jiki sai dada rikice wa yake yi. Amai ya tisa ni a gaba. Ba dama a d'ora tukunya yanzu zan fara amaye amaye. Hankali iyayena ya tashi. Da yake yanzu mamam ta hakurkurtar da zuciyarta ta daina tsiyataku, aka rasa me za'a ce mini. Tunda alamu k'arara na mai shigar ciki sun bayyana mini. Gwaggo ta rasa me zata ce mini. Sai da dare ya yi dare. Ta yi gyaran murya bayan ta gama danna mini jiki ta ce "Yabi alamun shigar ciki nake ga ni a tare da ke" Sanin a cikin zullimi take ya sanya ban tsaya noke noke ba na ce "Ni ma ina kyauta zaton shine Gwaggo". Ta hau salati ta ce "Cikin haihuwa Yabi?" Na ce "Shi fa Gwaggo". Ta dauki sabon salati ta ce "Ta ina kika samu ciki Yabi? Nasan dai da ikon Ubangiji ba zaki yi ashararanci ba, ina kyautata miki zato." Na saki ajiyar zuciya. Ga shi ina jin jiki. Ina nishi na ce "Na gode da kyakkwar shaida Gwaggo". Daga haka na kulle bakina a dalilin yadda nake jin tsananin kwankwatsa a duka jikina. Kan dole ta tashi doro alwallah ta tada sallah. Ganin bata samu nutsuwa ainun ba. Ya sanya bayan ta yi sallama na ce "Gwaggo Zaton da kike kyautata mini tabbas hakane. Kuma hakkun ciki ne. Idan Babah ta zo ki tuntube ta ki ji me zata ce akan hakan". Ta zuba mini ido ta ce "Yabi a gidan kurkun kuka yi cikin ko a ina?" Na fara nishi ina fad'in "Ki bari ta zo, ni ba iya bayanin nan zan yi ba. Dan Allah ki zo ki cigaba da matsa mini kafafuwana". Ta sake daukan salati tare da tafa hannu. Sai nanata iko sai lillahi take yi. Sai ta yi shiru sai ta sake zabura ta d'auki salati tana ce wa "K'warzaba da jarabar yaran yau ta kai kure wa. Ni Asma'u ina kallon zamani". A kan dole ta cigaba da yi mini tausa. Tana yi, tana hirji domin ta shiga mamaki mai yawa. Da safe da Baban Marina ya shigo duba ni. A sanyaye ta ce "cikine da Yabi Alhaji". Babu dar ya ce "Ma sha Allah! Ai rabo ba k'aramin al'amari ba ne. Allah ya raba lafiya". Ta yi galala ta ce "Alhaji na ga baka ka'du ba! Ya murmusa ya ce "kad'uwar me zan yi bayan na gasgata Yabi tamkar yadda na gasgata yunwar cikina. Ita tasan yadda ta had'u da mijinta. Tana da miji kuma dan na ganta da ciki sai na bi ba'asi, akan me?" Ta ce "To ai kowa yasan baya nan, sai kuma a ganta da ciki, kana jin yadda ake daura mata magana haka siddan. Ina kuma a ganta da ciki". Ya ja tsaki ya ce "Idan har kika daka bak'ak'en taadodin jama'a babu abin da zaki yi. Ya mik'e yana ce wa "Sannu Allah ya raba ku lafiya." Ya saka kai ya fice. Satin su baba biyu sannan suka dawo, cikin sa'a ido daya ya budu. Daya ya mutu. Aka yi murna da yi mata barka da arzikin da ta auna. Babah tana zaune a dakin Gwaggo. Yayin da nake kwance akan k'aramin gadon. Na samu sauki, amma jikin babu k'warai. Gwaggo ta ce "ikon Allah Yabi dai ciki ne da ita." Ta dauke kai ta ce "Ho ke kam yanzu kina neman baci da magana. Ina dalilin wannan tuyar da kike yi ne. Nasan da shi tun kafin mu zo." Gwaggo ta sake ce wa "ikon Allah sai kallo. Abin ne yake dafa ni. Wato kinsan komai ke, shi yasa ta ce idan kin zo, na ji a bakin ki". Babah ta mik'e ta ce "Sai ki yi ke kad'ai ina dalilin bin wannan diddigine haka? Mace da mijinta". Da mamaki Gwaggo ta sake ce wa "To wai a kurkun, a ina suke haduwa ni Ma'u! Babah ta fice ta ce "A a nima ban sani ba. Sai ki tambayi mijin nata tunda ita kin saka duk ta sururuce da kunya. Domin ke sai akan girman ki zaki baci da magana, sai ki je ki gano shi, ki tambaye shi yadda aka haihu a ragaya ". Ta fice da sauri. A haka muka sake shafe sati biyu. Yaya Aliyu ya zo ya kwashi yara ya ce tunda ba tafiya zamu yi ba, to ba zasu yi asarar karatunsu ba. Na kuma gane Babah tana son ta zauna da Dada a dalilin ta damu da lalurar da ta sami autarta. Sannu a hankali na fara warware wa. Matan gidanmu sai nan ake yi da ni. Mama da kanta sai ta tambayi abin da zan ci. Na tabbatar ta dad'e da ajiye makamanta. Amma yadda nake tiritiri da rik'e musu gidan ya kara mini kima k'warai da gaske. Ahalin gidanne dai idan muka had'u ko idan na fita da nufin zagaye ake bina da kallon k'urillah da tuhuma. Yara basa iya ce mini komai ba. Amma da kunnena na jiyo matansu Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gulmar cikin jikina suna fad'in "iyalin Tijjani bata yi shashanci ba, ai a yi mamaki, irin fasadin da ya yi a doron kasa, sai kurum." Na yi kamar ban ji ba. Domin a yanzu da nake fama da rashin Baban 2 mene ne bazan yi hak'uri a kansa ba? Baban Tsakiya kuwa fama yake da ciwon hawan jini. A dalilin mafi yawan y'aya'nsa sun kangare. Dama dai Jabir ne mai dama, to a lokacin da yake da dama bai bari ya taimaki kowa ba. Domin ko ni a farkon farkon rufe Baban 2 idan ya tura mini kudi sai ya ce "Ba sai an ji ba". Dan haka mafi yawa yanzu ba'a taimakonsa ko tausayinsa domin a lokacin da ya samu ba wanda ya more shi. Sai aka yi mutuwar kasko. Shi kuwa Baban Kasuwa manyan y'aya'nsa guda biyu na farkon mata ne. Amina sai Maijidda. Kuma dukkansu a yanzu kowa fama take a gidanta bare ta taimake shi. Gara ma Maijidda yanzu ne babu ta same su. Aminu na ukun sa'an Anas ne, yanzu suke tasowa. Gabadaya rayuwa ta yi juyin waina. Baban Marina da ake ganin babunsa a yanzu yafi su rufin asiri. Abincinmu yafi na kofofinsu. Ba kuma kudi ya yi ba. A a Y'aya' ne suka taso, muka hutar da shi fafutukar rayuwa. Har yau kuma idan Baban Marina ya samu damar da zai yi mana wasiyya sai ya ce "mu zama masu afuwa da manta sharri, mu kuma rik'e alheri komin kankatarsa. Ko waya ka yi masa sai ya ce "Ba jarumta ba ne fad'a a tsakanin yan'uwan juna. Ba kuma tsoro ba ne idan kai mai gaskiya ka janye ka barwa wanda ya karkace, masalaha ne da takaita rikici. Har ilah yau ba imani ba ne ka yi fatan ganin wani ya shiga mummunan yanayi duk yadda ya zalunce kuwa. Mafi yawan sakayya yanzu tun a duniya Ubangiji yake fara yinta. Matukar kana da gaskiya baka nufi kowa da sharri ba, to sai ka ga alheri komin dade wa. Iri

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161