Chapter 95
Chapter 95
Har kan gashinsa k'ura ne. Na ce "Bari na juyo maka ruwa wanka ga shi akan gawayi. Da kai ya amsa mini. Na sirka ruwan na kai masa bandaki. Ya shiga ya yi. Ya fito ya jika kayan da ya cire. Sannan ya shiga daki dan ya shirya. Kafin nan kuwa na Kai masa abinci falo. Na zuba omo na sab'e masa kayan na shanya masa. Ya fito ya ga ina shanya. Ya murmusa ya ce "Ni ina ce Asiya Toro ce ta ce Aji dawun ta yiwa k'ato wanki?" Kunya ta kama ni domin na sani tsokana ta ya yi, tare da tuna mini sababin da nake yiwa Nasiba idan tana yi masa wanki. Na dara na ce "Ai har yanzu ma ba zan yi ba, kawai na yi maka ne a matsayinka na mijina kuma bebina". Ya shiga falon yana ce wa "zo mu yi maganar a zaune". Yana cin abinci ina masa fifita. Ya ce "Da wayo da wayo dai so kike ki dinga ce mini Bebi ko?" Na yi gajeriyar dariya na ce "A a ai sunan ka yana zuciyata lokacin kawai nake jira. Amma kai kanka ai kasan bebi ne. Domin abin da kake yi mini ai bebis ne suke yin hakan. Ba dama ka kwanta sai ina kusa da kai. Ko juyi zan yi sai dai mu juya kwanciyar gaba'daya, saboda kana.." sai na kasa fa'da. Ya zuba mini ido ya ce "Fadi mana marar kunya. Me nake yi? Na daure na ce zuke wa bebis din da zan haifa mana abinsu." Ya murmusa ya ce "Ai ba nasu ba ne, nawa ne, idan sun zo dai zan dinga sammu su, idan lokacin shansu ya k'are za'a cire su, su bar mini kayana. Ni ai ba zaki taba yaye ni ba". Na yi dariya na kawar da maganar da ce wa "Wai da kanka ka je yago lallen ne?" Ya ce "Eh. Baban Marina na tambaya ko ina zan dinga samun lalle ina sara. Sai ya kwatanta mini yankin da Ubangiji ya azurta da lalle. D'an na goro ake bawa digacin yankin sai ka je ka yi ta yanka. Shine ma ya bani dubu guda duk da shima fama yake da kansa. Da naki karba kin ga b'acin ran da ya yi? Wai raina shi na yi, shi yasa nake ganin ba zai iya bani abu na kar'ba ba. Nasa hannu biyu na kar'ba ina ba shi ha'kuri, shi kuma yana ta yi mini fararen addu'oin da suka k'arfafa mini guiwa.". Na rausayar da kai na ce "Allah ya bada sa'a, yasa a fara a sa'a". Ya amsa da "Ameen Little". Kwanaki ka'dan lallensa ya bushe. Da kansa ya zauna ya gyara abinsa tsab. Ya ha'de su a buhu biyu. Ya fita da su, ni dai bansan inda ya kai ba sai gani na yi ya dawo da shi ya zama gari mai laushi ainun, kuma ya yi auki domin ba k'aramin yawa ne da shi ba. Ya kusa yin buhu guda. Ganin hakan sai na auni kwano biyu na zauna na k'ulle shi tas. D'aurin hamsin, da d'ari. Duk wanda suka zo k'unshi sai na yi musu tallan ina sayar da lalle, ina k'wabawa mutum yasa a gidansa. Nan ma sai Ubangiji ya sanya albarka domin duk sati sai na k'ulla kwano biyu, nima kuma a satin ina k'arar da fin kwano uku ma. Kafin ka ce miye wannan sai jarin Tijjani ya kafu ya samu na siyo mahallabiya da kwalin salatip. Duk sati kuwa zai je ya yago domin ya gamsu ba k'aramin rufin asiri hakan ya yi masa ba. Tunda duk sati zan ha'da masa ku'dinsa a kalla dubu goma. Idan ya kar'ba kuwa zai siyo kayan abinci da k'ananun abubuwa. Maganar ku'din cefane kuwa da ku'din pure water muke yi. Duk da hakan nawa yana shiga amma ba mai yawa ba ne. A hakan kuma bai fasa fita ya yi sana'a ba idan ya samu. Hankalinmu a kwance yake, mun samu rufin asiri. Tunda ya samu ya biya ku'din gidan amma na watanni shida, rabin shekara. Duk nacin ya kar'ba ya biya na shekarar sai ya biya ni a hankali bai yarda ba. Da na matsa ma sai ce mini ya yi "Allah ya karbi ransa kafin ya ga ranar da zan biya masa ku'din hayar gidan da zai kwana." Daga haka na ja bakina na tsuke. Muna cikin wannan rayuwar mai da'di domin dukkanmu mun gamsu da kokarin junanmu. Na yarda ina amfani da duk abin da ya ba ni, ina iyakacin kokarina ban nuna masa ina bu'katar abu sama da k'arfinsa ba, na kuma ajiye dukkan burikana na son na dinga yin suturu masu tsada. Maimakon haka sai na tattara na sayi dan kunnen gold wanda shi da kansa na bawa ku'di ya siyo mini a Jos. Ko zan yi abu a gidan sai cikin dabara ko kuma na kara masa ku'din lallensa idan sati ya zagayo. Shi kuma tunda ya fahimci burina soyayya irin ta indiyawa sai yake ajiye komai ya yi ta kashe ni da kalolin soyayyar da ko indiyawa ma sai a shiri, tunda suma ai shirin fim ne. Shiri kuwa kowa yasan shirya shi ake yi. Amma a hakan yake lalace mini. Ya zama tamkar mai irin shekaruna. Ko a littafai ba kasafai ake samun irin Bulkachuwa ba. Domin ya iya shiririta kala kala da mata suke son ayi musu. Idan yana gida barin komai yake ya tarairaye ni. Cinyarsa ita ce wajen zama na. Goyo kuwa zai iya goya ni, ya yi shara. Har k'aton baho ya siyo irin tafkeke na masu wankan jego. Ya cika shi da ruwa ya dauke ni ya tsunduma. Ya wanke ni tas. A shimfida kuwa irin murza ni da yake yi, da da'din da yake jiyar da ni dole ma na so shi na rikice a kansa. Domin har cikin zuciyata na fara tunanin da ba shi na aura ba dan ban more ba. Har jin haushin son da na yiwa Yaya J na fara yi. Gaba'daya na gama mutuwa a kansa, ba abin da nake so irin na gan shi a gida idan yamma ta yi. Yanzu da baya fita lahadi a gida yake yini. Da kaina na soke yin lalle da kitso. Komin girman mace bana yi a wannan ranar zan fa'da mata maigidan ya hana yi a wannan ranar. Dan na fahimci ba a daina zuwa ana katse mana jin da'dinmu ba sai nake yawan rubutawa a status d'ina cewar babu lalle ranar lahadi haka ma kitso. Mun yi kyau, mun shak'u da juna, komai yana tafiya dai-dai mussaman da na daina yi masa rikicin bai yi mini ciki ba. Da kansa ya dauke ni muka je asibiti da muka cika shekara guda da aure. Dukkanmu aka auna mu aka tabbatar mana lafiyarmu k'alau cikin ko wanne lokaci zamu iya haihuwa. Shike nan sai na daina damuwa illah iyaka ban daina addu'ar ma samu ciki na haihu ba. Muna cikin wannan yanayin mai da'di Rafi'a ta kammala karatunta na jamaia ta dawo gida gaba'daya. Kusan kullum sai ta shigo mini. A zuciyata bana so amma tunda uwarta ba k'aramin kirki take yi mini ba. Sai nake share wa mussaman ita din ma mai kirki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161