Chapter 133
Chapter 133
*Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Idonta ya ciko sosai amma ta sanya jarumta ta hadiye. Ta ce "To Alhaji ban da abin ka, duk wanda ka damkasu gare shi ai shima zai mace wata rana. Kawai yi dabarar damkasu a hannun Ubangiji domin shi ne rayayye wanzazze. Ina kuma son ka yiwa Hauwa adalci. Al'amarin ne yafi k'arfinta. Shi kansa Tijjani ai ba'a hayyacinsa yake ba. Idan muka daure muka yi hakuri. Muka taushi Yabi ta yi hak'uri komai zai wuce. Duk abin da aka gina shi da son zuciya baya k'arko". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ya ce "Kina nufin na sake tirsasa Yabi ta zauna da Tijjani ko da bata son hakan?" Da sauri ta ce "Eh. Domin babu abin da hak'uri ba zai bayar ba idan aka nutsu." Ido cikin ido ya ce "To a yau kam bazan d'auki shawarar ki ba. Sassauci d'aya zan yi, idan ta ga zata zauna shi ke nan sai na bita da addu'a. Idan kuwa ta ga ba zata zauna ba, to kuwa ko menene zai faru sai dai ya faru amma zan fanshi y'ata." Ta kasa ce wa komai domin ta san da dukkan zuciyarsa yake magana. *Bauchi*. Ina falo kan sallaya na idar da la'asar ina jan tasbaha. Hawaye kuma sai sintiri suke yi. Yayin da Tijjani yake zaune babu sukuni a tare da shi. Yara kuma suna islamiya. Na daga hannuwana sama a fili na ce "Allah kai ne mai sarrafa zuciya, Ubangiji ka sarrafa mini ita ta zama mai hak'uri, Allah ka mini baiwa da juriyar shanye ko wacce irin damuwa ba tare da hakan ya tab'a imanina da lafiyata ba. Ina rokon a cire mini damuwa akan wannan al'amarin domin na zama cikin masu imani da abin da ka hukunta. Allah ka warware mini dukkan abin da zai tunkare ni na sharri. Allah ka bawa Mijina lafiya, ka k'ara masa arziki, ka kare shi daga dukkan mummunar kaddara. Ina rokon a shirya zuriata, a tsare mini su, a kuma sanya su a cikin bayi na gari. Allah ka jik'an iyayena ka musu tukuici da aljanna." Na sake yin salatai da istigifati sannan na shafa. Na jingina da bango ina ta sakin ajiyar zuciya domin gabad'aya ji nake tamkar na ciro ta, ko na huta da azababben ciwon da nake ji. Ya sassauta murya ya ce "Asiya na gode miki. Ki cigaba da yi mini addu'a dan Allah. Ina ji a jikina bani da lafiya. Na kasa gane kaina, ki yi hakuri da ikon Ubangiji komai zai faru bazan bar ki ba Asiya". Cikin kuka na ce "Bari na nawa Tijjani? Sau nawa zaka ga ina kuka ka banzantar da ni, sau nawa kake sanadin sa ni kuka? A da na dauka duk lalacewar giwa ta fi k'arfin kiyashi ya ja ta. Ashe sannu a hankali idan suka yi taron dangi sai su jata su kacaccalata. Amma babu komai na barwa Allah ya zame mini garkuwa." Ya tsugunna a gabana ya ruko hannuna a tausashe ya ce "Ba dan ki gamsu ba, ina rantse miki da Ubangijin Al-arshi bana jin so ko wacce mace da sunan soyayya ko sha'awa a zuciyata sai ke Asiya. Amma bansan me yasa nake jin zuciyata na tafarfasa a dalilin Nasiba ba. Ina jin idan ban aure ta ba bazan samu nutsuwa ba har abada. Ki yi hak'uri kada ki juya mini baya a cikin wannan halin da nake ciki. Masifu sun dabaibaye ni, ikon Allah kad'ai yake rik'e da tunanina. Amma gabadaya bani da sukuni. A gida babu nutsuwa a tsakaninmu, a wajen sana'a ta jifana ake yi. Ga shi an kulle mini zuciya da tunanina. Babban tashin hankalina yadda Baban Marina ya shirya kwace mini ke. Dan Allah little kada ki barmu ni da twins. Ya ya ake son mu yi, k'arfin hali kawai nake yi, amma ni yanzu har na fara fatan mutuwa ta dauke ni na huta da wannan dambarwar". Na kasa kwace hannuna. Wani irin abu ya dinga taso mini. Na gasgata ina son Tijjani k'warai da gaske. Domin saukowar da ya yi, ya mini magana ta rarrashi da tausayawa sai na ji k'ullin zuciyata ya fara kunce wa. Na fara kuka na ce "Ta ya ya zan yarda kana sona Tijjani alhalin kullum sai ka mini abin da zai sa ni kuka? Yaushe rabon da ka zauna ka ji damuwata, hatta yaran nan sun san ka canja mini. A gabansu kake rufe ido ka tsigale ni haka siddan. Kullum a cikin yi musu karyar baka da lafiya na ke dan kada su kullace ka. Yaushe rabon ka da nemi wani abu a tare da ni, me kake so na fahimta tunda nasan baka da hak'uri a wannan fagen?". Ya tsananta rikon da ya yi mini ya ce Na gode da kike rufa mini asiri a idon y'aya'na. Allah ya yi miki albarka. Sannan Allah ne shaidar furucin Baban Marina da yake nuni zai k'wace mini ke ya sanya na rasa k'arfi a tare da ni. Wallahi bana aikata komai na b'arna Asiya". Ban ce komai ba ya sake sassauta murya ya ce "Kin tab'a mini alkawarin ba zaki sake fita daga gidan nan ba sai da izinina, ina son ki samar mini da nutsuwa ta hanyar tabbatar mini har yanzu ma ba zaki fita babu yardata ba. Wallahi Asiya ke ce Tijjani. Ke ce nutsuwata, ke ce rufin asirina idan har kika bar ni, ina tabbatar miki komai zai kwace mini. Masu son nawa ma sai sun guje ni, saboda zan rasa abin da suke so a tare da ni." Na kalle shi hawaye na sintiri akan fuskarsa. Ya jani jikinsa ya rungume yana fad'in "Dan Allah ki yafe mini, ki fahimce ni, ki mini uzziri, ki tsananta yi mini addu'a ". Muka dinga kuka babu mai rarrashin wani. Dukkan jarumtar Tijjani ta k'are gabad'aya. Na kuma gasgata ba a haiyacinsa yake yi mini wani wulakancin ba. A haka yaran suka dawo suka tarar da mu. Hamim ya zuba mana ido. A hankali Tijjani ya sake ni tare da dabarar dauke hawayen sa. Yayin da nawa ya kasa tsayuwa. Hanif ya ce "Ammi Baban 2 yau ma ba shi da lafiyar ne, ya sake yi miki wani abu ne?" Kafin mu amsa masa Hamim ya ce "Lafiyarsa k'alau fa. Ammi ce take ce mana ba shi da lafiya, marar lafiya yana yin fad'a ne?" ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi!
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161