Chapter 27
Chapter 27
ne. Mutumin kirki ne, kin ga abin da ya ba ni". Ya nuna mini rafar dubu guda. Na zaro ido na ce "Billahillazi dan yankan kai ne Tijjani! Ban da hakan daga haduwa ya baka dubu dari?" Ya yi dariya ya ce "Kin san istigifari nawa na yi yau kuwa? Na yi yafi dubu goma, Ubangiji kuwa ya yi al'kawarin warware mana komai matu'kar muka dimanci istigifari har da bude kofofin arziki. Bana haufi Ubangiji ne ya turo mini arziki ta hannunsa. Ki yiwa kanki fa'da Asiya kin ga dai ba shiri muke yi da ke ba, amma na fi jin ciwon abin da aka yi miki sama da wanda aka yi mini. Ki saurare shi, ki yi addu'ar zabin Allah. Idan kin samu nutsuwa ki ba shi dama azo a yi auren ki ko kya samu sau'kin masifar gidan nan. Nima kin ga wannan ku'din ajiye wa zan yi wani satin zan bayar akai mini ku'din aure, ko wannan yar'uwar ta ki zata shafa mini lafiya". Na sauya fuska na ce "Nasiba fa bata da laifi Tijjani". Ya kwabe fuska ya ce "To ai ni kuma ko ita ce ka'dai ta rage a duniyar nan na haramta wa kaina ita. Bulkachuwa bai yi wannan arahar ba, ba za'a ci mutuncinsa, a tozarta shi kuma ya lik'e ba". Ya mik'o mini dalleliyar waya a kwalinta ya ce "Da caji da kuma layi a ciki ki kunna zai kira ki." Ya hade hannu alamun rarrashi ya ce pls ki saurare shi ko za'a dace". Na ce "Baba fa ya hana ni rike waya, yanzu haka akwai sabbin wayoyina a ajiye, da wacce Yaya J ya siyo mini, da ta wajen Abdulrashid har biyu. Wai sai na kammala makaranta, ko idan na yi aure na ri'ke". Ya ce "Wannan dai kin ga Babban mutum ne Yabi, ga shi kowa ya yi masa shaidar nagarta. Ki boye ta ba sai an ga ni ba, bana son ya kubuce miki. Bauchi zai kai ki, ba zai ajiye ki anan ba, ko ma Abuja. Babbar waya ce ki yiwa Allah kada ki bari ta salwanta". Ya juya na bi shi da ido ina raya ina ma yadda ake zuba masa kyakkawar sura kuma cikakkiya haka yake da kyakkawar dabi'a da nagarta. Inda a ce shine yake da dabiun Yaya J da ya zama komai an hada masa. Mafi yawan lokacin ina yawan ayyana da Yaya J ne yake ingarma kaman Bulkachuwa da an yi namiji tsayayye mai kyakkawar manufa. Amma halayyar Bulkachuwa shine nak'asunsa, mussaman na yadda yake iya keta alfarmar shari'a yana aikata kaba'ira, ga rashin ta ido, ga shigar iyashege, yau har barima na ga ni makale a kunnensa, gashin kai ya sha tiri (dying) gashinsa mai kyau ne irin na fulanin Bulkachuwa amma ya mayar da shi cibiri cibiri tsabar fitina da son yaudare y'anmatan da ba susan ciwon kansu ba, ga kafiya akan ra'ayinsa, ko k'uda ya shafa masa lafiya wajen naci. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Amma akwai tausayi mussaman idan ya ga kina kuka, to kin karya masa lagonsa, sannan yanzu ya fara sanin kishin kansa har yana taya wani ciwon abin da aka yi masa. Ashe da ya fita wajen Baban Marina ya raka wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba, ya nemi a bashi izinin fara magana da ni. Baba ya ce "Ya bashi damar neman yardata, amma idan ban amince ba, ba zai mini dole ba. Shi kenan sai Alhaji Mustapha Zaki yake zuwa, ni da kaina kunyar yadda nake yar mitsil a gabansa nake yi. Dogo ne sosai yana kuma da jiki, ga tumbi sai dai tumbin bai yi muni da yawa ba, ustazu ne sosai domin ya tsayar da gemun sunnah. Ku'di yake sakar mini da suturu na alfarma, ga kuma mutunta ahalin gidanmu. Dada kanta sonsa take yi a dalilin idan zai zo sai ya kawo mata rafar sabbin ku'di, y'an 100, da na 50, da na 20. Yana cewa gashi ta ajiye canji a hannunta, duk zuwa kuwa. Ga ledar tufa da kilishi. Nawa kuwa y'an 500 da 200 ne. Bulkachuwa ya zama magayak'insa. Kullum sai ya masa kamfen, fa'di yake "Gidan ki daban zai baki Asiya, idan kika yi sa'a ma Umrar bana da ke za'a yi, aikin hajji kuwa tabbas ne. Ba ruwanki da tsufansa, lallaba ki zai yi. Ni kaina alherin da nake samu a jikinsa ba ka'dan ba ne. Kin ga "Na kalli hannunsa da yake karkada wa. Mukulli na ga ni ya ce "Mashin ya ba ni sabo dal, gwamnatin jahar Bauchi take raba wa matasa, shine ya saka sunana. Dan Allah Asiya ki so mutumin nan, oh wani hanin ga Allah baiwa. Yarinya kin tako arziki, na tabbatar Gwaggo data haife ki da akwai wutar Nepa a time din Wallahi. Na miki murna ma da wannan dan tsurut din bai same ki ba. Ai ke babbar mace ce, sai manyan maza, amma yana tafiya tamkar iska ta hure, kirjinsa duk bai fi allona na makarantar tsangaya ba". Na b'ata rai na ce "Yaya J din kake yiwa haka akan bare? Sannan nima ai y'ar tsurut ce ta ina na zama babbar mace?" Ya murmusa ya ce "Ba sai na bu'de maganar ba, ke ma kinsan yadda ake miki layi ai akwai sirri na mussaman a tare da ke. Na'kasunki biyu ne tsayayyiyar zuciya, kuma taurarriya, da fitsara, dole handle dinki sai tsayyayen namiji k'arfaffa ba lusari irinsa ba". Na sake b'ata rai na ce "To yadda kake ganin zuciyata, tasa har tafi tawa tsayuwa da jarumta". "Ke tafi can, me kika sani? Wai har yau son Jabir kike yi? Tabdi jam lallai so ba k'arya ba ne. Jiya fa na gan shi goye da Maijidda a mashin ina ga d'an yawon shan iska suka fito". Nan da nan idona ya k'ada sosai hawaye ya cika su, ya mike yana fa'din "So sorry Asiya Toro. Ki gode Allah da ya kawo miki Honarable Zaki. Domin da ki yi kuka a inda kike so, gara ki yi a inda ake son ki, da ki yi kuka a gidan cin abinci gara ki yi kuka a gidan daula sosai, domin mu maza da kika ganmu so baya hanamu murza kanku". Na girgiza kai na ce "Zan amince ne idan kai ma ka yarda zaka shirya da Nasiba, ni shaida ce akan ba wanda take kula wa saboda kai". Ya bata fuska ya ce "Kin san Allah? Zan ci mutuncinki Asiya Toro! Kada ki saurare shi mana, shawara na baki saboda ina nufin ki da alheri, idan baki so ba, ki sallame shi, ki jira wanda zaki dinga kuka a gaban murhun gawayi, da kishiya. Ga kuma ba'kin cikin da zaki kunsa a wajen ahalinsa, shasha da bata san me ya dace ba". *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161