Chapter 109
Chapter 109
A hankali kuma Tijjani yana samun rufin asiri a zamansa a baucy. Tunda abinci dai baya yanke mana. Iyakar kokarin jarfinsa yana yi. Duk sati zai taho musu da Pampers. Ni kuwa kayan shayi duk sati ne. Idan na ce "Basu kare ba". Ya dinga fa'da akan me bazan dinga shan shayi mai kauri ba, alhalin ina shayar da yara har biyu. Ga su nan su sun yi girma ni kuma na sake zuke wa. Watarana Baba lami ta ce masa ba rashin cin abinci ba ne, wasu matan idan suna shayarwa hakan suke yi. Sai sun ya ye sannan su yi kumari. Baba Lami bata tafi ba sai da muka kwashe watanni kusan biyar a tare. Lokacin su Hanif na da watanni shida. Muka ha'da mata alheri sosai. Sannan suka tafi da Gwaggo da Yaya Ummi bikin da za'a yi a can Kangire. Na so zuwa, amma ya yi mirsisi ya hana. Sannu a hankali muke rayuwa, bamu cika samun matsala ba, tunda kwanakin da yake yi a Bauchi sun fi wanda yake yi a Toro. Kullum idan ya dawo sai ya ce "ki tsananta yimini addu'a little. Mahassada sun kewaye ni a kasuwar nan. Ga shi an rasa gane inda matsalar take kullum Alhajin da muke wajensa sai karayar arziki ya ke samu. Ina jin tsoro k'warai da gaske. Cikin tausayi na ke kwantar masa da hankali da kalamai masu taushi. Wani zuwa da ya yi, ya ce "mu shirya zai kai mu Bulkachuwa mu yi sati. Na dinga murna domin rabona da zuwa tun kafin na haihu. Ga shi yazu watannin su tara har sun fara tsayawa. A yanzu kam na gasgata kama suke yi da Bulkachuwa. Domin suma haka suke dogaye, masu gaba manya. Ba wanda zai ce ni ce uwarsu. Domin manya ne sosai, sannan ni yar tsurut ce sosai. Kawai faratuna suka diba, da kuma yan k'ananun kamanni. Amma kammanin ubansu yafi yawa a tare da su. Tun yanzun kuma halayyarsu ta banbanta. Haneef mai sanyi da hakuri ne. Sai ya yini baka ji kukansa ba. Kafin ya nemi nono sau daya Hamim ya nema sau uku. Zai yi wahalar gaske ya damuki d'anuwansa yasa shi kuka. Amma Hamim kullum cikin nukurkusrsa yake. Ga shi da shegiyar kiwa. Ko wajen Babansu sai ya akan dole yake zuwa. Ko idan ya ga ya dauki Hanif zasu fita. Shi dai kullum yana jikina. Ko k'unshi zan yi, sai dai na ha'da masa kayan wasa a kusa da ni. Ko ya ce ",sai na goye shi. Sabanin Hanif da ba ya yin kiwa. Kowa ya mika masa hannu zuwa yake yi. Shiyasa ma na fi kai shi gidan Yaya Ummi ya yini tunda yanzu ba ni da nisa da ita. Kullum Bulkachuwa sai ya ce halina ya kwaso. Domin mafad'aci ne na gaske, ga kuka. Idan ina mita akan halinsa Gwaggo ma ce wa take yi hakan na yi mata. Haka ta sha fama a goyona. Bana yarda a dauke ni. Ko band'aki zata shiga sai an yi artabu da ni. Da yammaci muka isa Bulkachuwa. Babah sai ina ka saka take yi da ni da yara. Komai ta mika hannu a kai sai ta dauko ta ajiye a gabana. Yara kuwa kayan wasa sabbi sun fi kala uku tamkar dama a wajenta suke. Na kasa ha'kuri na ce "Babah wadanda kayan wasan fa?". Domin ihisan ba a garin take ba. A cikin Bauchi take bari na yi zaton na yaranta ne. Da walwala ta ce "Tunda ya ce zaku zo na siya musu, tunda na ga mai sunan yayan nawa rigimamme ne. Shi dai bai kwaso halin mai sunansa ba. Hanif ne ya kwaso halin mai sunansa." Nasir da yake gefe ya ce "Su Babah ana yabon sunan masoyi". Ya bani dariya na rufe fuskata na dinga yinta. Ta mike sabe da Hanif tana fa'din ja'iran yara bari na baku waje. Shi dai Tijjani bai ce komai ba. Asalima matse wa ya yi ko dariyar bai yi ba. Kwana biyu ya yi, ya barmu ya wuce Bauchi. Bayan dakina da na Gwaggo ba inda nake samun natsuwa irin a dakin Babah. Domin wata irin mua'amala take yi da ni mai dadi da tattali. Bata taba nuna surukunta a tsakaninmu ba. Sai ni ce ma nake jin kunyar yin wasu abubuwan a gabanta. Ita kuwa da taga hakan zata balbale ni da fa'da tana fa'din bata son rashin kunya. Har yaushe na zama matar tasa da zan ture ta a uwa na mata kallon suruka. Na sake na yi komai yadda nake so kamar yadda nake yi tuntuni. Da kanta ta dafa mini kazar da na tabbatar ta mata ce. Kunya ta kama ni. Ita kuwa fadi take ci ki sha romon. Tun lokacin haihuwar na siya na dauka zaku zo yawon arba'in. Tunda baku zo ba. Na ajiye nasan a can ma za'a gyara ki." Na rasa yadda zan yi, ita kuwa ko a jikinta. Ranar da Bulkachuwa ya dawo. Da daddare an hadu a falonta ana ta hira cikin walwala ya kutso da maganar yana son mu koma Bauchi gaba'daya. Ta ce "ka dai kafe. Yanzu kam tunda yaranta sun yi k'wari ba zan hana ba. Allah ya bada sa'a. Dama har da tunanin yadda sana'ar ta zata durk'ushe ne. Amma In sha Allah a can din ma sannu a hankali za'a santa." Ni kuma sai kawo masa abinci abubuwa nake yi. Gaba'daya na kasa sukuni. Babah da kanta ta gane yanzu kam sonsa nake yi da dukkan zuciyata. Washagari ana zaune bayan mun karya. Sai kawai ya kalle ni ya ce "A irin wannan ranar ta shekaru uku baya kika zo har nan kika ce ba kya sona Asiya". Nan da nan na ji tamkar k'asa ta tsage na shige. Kunya ta rufar mini. Na rasa yadda zan yi. Sai kawai na fara kuka ina ce wa "Idan juninka tashin tashina ne, da son sai ka kunyata ni, to ni ba damuwa zan yi ba, kai ne zaka ji kunya Wallahi". Nasiru ma cikin dariya ya ce "Ai kuwa nima na tuna yawun da kika kwalbana masa a fuskarsa. Yau kuwa sai faman girmama lamarinsa kike yi". Na sake rushe wa da kuka ina ce wa "Ai kai dama baka fa'din gaskiya". Babah ta ce "Yo ni ke kika fi ba ni haushi, to kukan na mene ne? Ware wa zaki yi ai ku yaga, suma ki nutsu ki fadi irin nasu al'amarin da baza su so a taso musu shi ba." "Nasiru ya ce "Ni dai babu abin da zata fa'da a kaina, sai dai ko akan mijinta". Tijjani dai tunda ya kunyata ni bai sake ce wa ba. Jimawa ka'dan Babah ta mike ta shiga cikin gida. Nasiru ma ya mike yana ce wa "Hajiya Yabi bari na fece tun Babah bata zo ta fa'da miki wani abu a kaina ba." Ko kula shi ban yi ba. Yana fita na kalli Tijjani na ce "Na gode sosai Baban 2" Ya yi murmushi ya ce "wannan godiyar fa! Ta mece ce?" Na matso hawaye na ce ",Na gode da kunyata ni da ka yi, na gode da wannan sakayyar". Ya dara ka'dan ya ce ",Kin san na fa'da miki lokaci zai zo da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161