Skip to content

Chapter 53

Chapter 53

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

sha Allah ba zan wuce la'asar ba. Za'a kawo miki abinci da rana. Ki shirya gobe zaki fara yin girki". Sai lokacin na fashe takaicinsa da cewa "Ba zan yi ba. Har abada ba zan dora tukunya saboda kai ba". Babu damuwa a tare da shi ya ce "Babu laifi. Lokaci zai fayyace komai ai". Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba. Har shad'aya ina daki ban fita falon ba. Sai da cikina ya tsananta yi mini kartan yunwa. A dole na fita. Na tarar da waina a karamin flask. Sai kunu a jug. Daga dukkan alamu siyowa ya yi. Kan dole na zauna na karya. Ina zaune har aka fara kiran sallar azahar. Na idar kenan sai ga almajiri yana kwankwaso kofar shigowa wajena. Da yake ni ce a farko su kuma su Mama na can ciki. Bamu ha'da komai ba, sai kofar shigowa gidan. Da sauri na fita na bu'de masa. Ya mik'o mini flask din abinci babba mai kyau. Wai wani ne ya bashi ya kawo wannan kofar. Na kar'ba ba tare da na ce komai ba. Na sani abincin da ya ce za'a kawo mini ne. Sai da na zauna a falo na bude na ga alalan gwangwani ya ji manja. Da alamun kifi a ciki. Na ji wani iri a dalilin yunwa nake ji ba ka'dan ba. Ni kuma bana iya cin alala na koshi. Tabbas an gyara shi ne dan a burge ni. Na rufe, ina sake jin yunwa na taso mini gadan gadan. Na yi shiru ina nazari. Sai na ji wayata na k'ara. Ina dubawa na ga Tijjani ne domin ina da lambarsa tun lokacin kwamshina da muka fara dan gaisawa. Na ki amsawa har ta katse. Ya sake kira ban dauka ba. Bai fasa ba, sai a karo na hudu na dauka a fusace na kan ga a kunnena, bayan na danna alamar amsa wa. "Yaro ya kawo miki abinci?" "Eh". Na fa'da a gajarce. Ya ce "kin ci na safen kuwa?" "Wai ni kam jinjira ce ne da zaka dinga mini tambaya tamkar kankanuwar yarinya? Idan ma ban ci ba ai cikina ne ko? Tunda baka shawarce ni akan abinda zan ci ba, ka ajiye mini wanda ya yi maka". Ya nisa ya ce "Asiya Toro kenan! Cikin kuka na ce "Komai zaka ce Allah na ganinka ai". A sanyaye ya ce "Kukan na menene Asiya?" Na sake tsananta kukan na ce "Akan me za'a kawo mini alala? Ni bana ci". Ya tausasa murya ya ce"Alalan gwangwani ne, saboda ke har kwai da kifi aka saka a ciki. Daga gidan abokina Abdul aka kawo miki fa, kema kuma kinsan matarsa mai tsabta ce". Da kukan na ce "To ni ina ruwana, ni dai ba zan ci ba, kuma yunwa nake ji tunda kunun ma ban iya sha ba, ya riga ya yi sanyi k'arara." Ya diririce ya ce "Ki yi ha'kuri bari na sa a kai wa Ummi macaroni da kayan miya sai ta daho miki yanzu. Hakan ya yi miki?" Na yi shiru. Ina harara tamkar yana wajen. Ya sassauta ya ce "Please mana Asiya ki ce to". A shak'e na ce "Yanzu d'aya da rabi. Idan ya wuce uku da rabi bazan ci ba, gara yunwar ta kashe ni". Ya dinga fa'din"Na gode sosai, bari na saka a kai mata yanzu. In sha Allah ba zai wuce hakan ba." Ya katse wayar. Na ri'ke wayar, haka kawai sai na tsinci kaina da mamakin yadda Tijjani yake rawar jiki a kaina. Gashi tunda na zo ban ta'ba yi masa wani alheri ko da ta magana mai da'di ba ce. Yadda ya lank'awasa harshe yana rarrashi tabbas yana yi ne tunda ga kasan zuciyarsa. Na fara gasgata sona yake yi ba sha'awa ba. Mintina biyar a tsakani ya sake kira. Na dauka bayan ta kusa tsinkewa. Da sauri ya ce "An tafi kai mata. Na ja mata kunne, na ce ta bar komai ta girka miki, tunda Nina sanya ta. Biyu da rabi zan aika a karbo mini. Dan haka zuwa uku za'a kawo miki in Allah ya yarda". Na yi shiru. Ya numfasa ya ce "Asiya ba ki ce komai ba". "A hankali na ce "Ina ji ai" Ya yi kasa da murya ya ce "Me zan taho miki da shi?" "Bana bu'katar komai na ka". A sanyaye ya ce "Shikenan, amma na siyo miki abin da nasan zaki yi murna". Na kyabe baki tare da fa'din "Hmm to ya yi". "Baki ce na dawo lafiya". A gajiye na ce "Tijjani ni na aike ka ne? Ka dame ni, in ta nine ma kada ka dawo". Kada na dawo Asiya? Saboda ke na yi tafiyar fa! Amma idan na dawo zaki ga ni". Ban bashi amsa ba na kashe wayata. Na ajiye ina jin wani irin abu da bansan menene ba yana mamayata. Uku saura na ji ana buga k'ofar. Na zari hijabi na nufi k'ofar. Yaro ne ri'ke da madaidaicin flash. "Gashi in ji wani a waje". Ya fa'da a hanzarce da alamu sauri yake kada ya yi latti tunda kayan Islamiya ne da jikinsa. Na kar'ba na tura kofar. Kicin ma fara shiga na dauko plate. Sai lokacin na lura da kwalin taliya, macaroni da galan din mai dana manja. Sai wani katon bokiti sosai mai murfi. Na bu'de na ga garin masara ne a tankade. Daga kantar kuwa an jere robobi masu dauke da kuka, kubewa daddawa da yaji. Sai kunshin bakar leda mai dauke da Maggi da onga da kuma gishiri. Na yi tsam da raina. Ina jinjina wannan kokarin. Na sani Kuma Babanmu baya irin wannan al'adar domin shima baya bari a dorawa ango hidima mai yawa. Na tabbatar a kaina aka fara irin wannan hidimar ni din ma saboda Tijjani ya yi. Daga can gefe na sake hango buhun gishiri a cike amma kuma d'aure bakin aka yi. Na saka hannu na ta'ba na ji don na tabbatar ba gishiri ba ne. Ina tabawa kuwa na gane shinkafa ce a ciki. Na girgiza kai ba tare da na furta komai ba. Na dauki abin da zan dauka, na fice. Na zauna ina cin abincin da ya yi mini da'di ya ji kifi da albasa. Na bu'de fridge ga mamakina sai n ganshi cike da pure water da lemon fanta da coke da kowanne zai yi shida. Take na fahimci katon daya ya siya aka hada masa kaloli. Na dauki ruwa da lemo na rufe. Ina ci ina nazarin yadda Tijjani yake ta rawar jiki a kaina. Wayata ta hau kuwwa. Kamar ba zan dauka ba sai kuma na dauka din. Da sauri ya ce "Network dina ne ya dauke. An kawo miki abincin, kin ci?" A shak'e na ce "Ni ban ci ba, yaji ya yi yawa, ga shi salam babu gishiri ko maggi ne oho". Ya diririce ya hau fa'din "haka Ummi zata yi mini? To a kawo miki yoghurt. Kafin na dawo na miki girkin da kaina". Na yi shiru. Cikin rarrashi ya ce "Pls Asiya Toro". Na tunzura na ce "Ai da zaka bar Toron baka tuna da cikina ba. Saboda bani da daraja. Akan me yanzu zaka fitine ni da buge bugen waya da tambayar na ci

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161