Skip to content

Chapter 81

Chapter 81

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

haka ka ce? Ai shikenan next time zaka gane ashe dazu ba karamin jarumtar na yi ba". Ya jani jikinsa ya ce "Kin san bana wasa a wannan fannin tsokanar ki nake yi, idan akwai abin da yafi jarumta kin yi dazun". Na kalle shi cikin nauyi nauyi, kunya kunya na ce "ka ji tsoro?" Da sauri ya ce "Na ji". Bai fita ba sai da ya dawo daga sallar azahar. Muka ci abincin da tare muka yi da shi. Sannan ya fita zuwa gidan Alh Ado Naira zai yi musu gyaran satellite tunda aka kawo wuta suke ta yi masa waya. Kamar ana jiran ya fita aka fara zuwa lalle da kitso. Shike nan muka shirya da Tijjani. Wata irin soyayya yake gwada mini mai wuyar samu. Da ya ga na canja fuska zai fara susuce wa, ya dinga jaye jaye magana, ko fita ya yo sai ya dawo. Matu'kar ban ware masa ba, ba zai samu nutsuwa ba. Ni da kaina na sani an jarrabe shi a kaina. Domin gaba'dayana a tsaye ban fi iya ruwan cikinsa ba. Duk zafin ransa baya son mu yi fa'da. Cikin rarrashi yake tafiyar da ni. Komai da rawar jiki yake yi mini. Kullum safiya ya wajaba kansa share duka gidan. Ya sa tsintsiya ya wanke band'akin, sannan ya tashe ni na yi wanka. Mafi yawa da safe da burodi muke karyawa. Dan haka shayin ma sai dai na gan shi a filas ya riga ya dafa. Da nutsu sai na ga ne tunda na daina gudunsa a shimfida shike nan ya tattara dukkan hankalinsa a kaina da lamarina. Baya taba yin dare a waje. Ana idar da sallar isha zai dawo ya rufe gidan shike nan sai gobe. Idan kuwa uzziri ya yanko masa sai ya bugo waya ya sanar mini yana waje kaza. Na ce to tare da addu'ar ya dawo lafiya. Ranar da yan rikicin suke kusa kuwa, na botsare masa idan ya dawo. Ya yi ta barin jiki wajen rarrashi na. Tuni muka fara jarrabawa har mun kusa kammalawa. Da kansa yake kai ni. Idan mun gama sai na yi masa waya ya zo ya dauke ni. Muna tsaka da jarrabawa Nazira ta haifo d'anta lafiyayye. Dan haka zarya nake yi tsakanin makaranta da gidanta. Har aka yi suna yaro ya ci sunan wan mahaifin mijinta Ahamd. Ni da kaina na lank'aya masa Abid. Sosai na yi mata hidima ita da yaronta. Ranar suna wanda a lokacin watan Maijidda biyu da haihuwa, y'arta Sajida ta yi gubibi da ita. Tana hannuna ina kare mata kallo. Na rasa gane da wa take kama a tsakanin itayenta Jabir da Maijidda. Saratu da Firdausi suka shigo. Ita Firdausi ta haihu. Saratu ce ta ke ja itama yau ko gobe. *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Na kallesu da murmushi na ce "Ni kam da wa Sajida take kama ne?" Kafin na rufe baki Maijidda ta ce "Da Abbanta mana. Yo ko makaho ya shafa ai yasan kama take da Honey. Shiyasa yake kara sonta domin kullum ya dauke ta sai ya ce mata "Ta zabo uwarta da kanta". Gaba'daya jikinmu ya yi sanyi domin kuwa kowa yasan neman magana kawai take yi. Dan haka sai na mikawa Firdausi yarinya na shiga hidimar raba abinci. Amma k'asan zuciyata ya yi nauyi akan lamarin Maijidda. Har aka watse ban sake yarda na zauna a cikinsu ba. Har dare duk mana gidan Nazira. Muna zaune sai ga yaro ya zo ya yi sallamah ya ce "Wai Asiya ta fito su tafi". Na kasa boye masa abin da Maijidda ta yi. Tun a hanya na hau rattaba masa abin da ta yi mini. Maimakon ya bi bayana ya fa'da mini maganganun da zan ji da'di. Sai ce wa ya yi "To mene ne na bacin rai a ciki? Ke ma Ubangiji ya za'ba miki wanda yafi mijinta son ki, to sai me kuma? Ki bar maganar nan inba so kike na ga ne kishinta kike yi har yau ba". Takaici ya kama ni goma da ashirin. Na kame bakina na yi dif. Amma na riga da na harzuka k'warai da gaske. Ga mamakina sai kawai shi ma ya share ni. Muna isa gida ya gama uzzirinsa ya yi kwanciyarsa ya rabu da ni. Ba'kin cikin hakan ya sanya na dinga kukan sharbe. Bai ko motsa ba, bare ya nuna ya ga ne halin da nake ciki. Da kaina na kwanta. Da asuba bayan ya dawo nan ma kwnaciya ya yi bai nemi ni ba kamar yadda ya sabar mini. Ai sai kawai na fashe masa da kuka mai sauti. Ya janyo ni jikinsa ya ce "Yi shiru, na baki hakuri kin ga". Cikin kuka na ce "Akan me zaka yi fatali da ni?" Da rauni a muryarsa ya ce "Akan me har yau baza ki bar kishin Jabir ba? Kina tunanin zan ji dadi idan na ga ne har yau ban yi nasarar shafe shi a ranki ba?" Na yi shiru sai shesshekar kukana ne yake tashi. Haka ya ajiye fishin nasa ya dinga rarrashi tare da shafata cikin nutsuwa. Daga hakan kuma ya shiga yin abin da baya gundara da yinsa. Sannu a hankali muke rayuwa. Duk yadda Bulkachuwa yake tarairaya ta, akwai abin da yake mini wanda yake ci mini tuwo a k'warya. Duk yadda na so na dinga saka mana kifi ko nama a cikin girkinmu ya k'i yarda. Idan kuwa har na bayar aka siyo na girka to zai ci iya abincin ne ya bar mini nama ko kifina. Rannan da na nuna b'acin raina. A zafafe ya nuna mini yatsa. Ya ce "Iya abin da nake da shi zan ba ki, ba kuma zan zauna ki shiga cikin lamarin rik'on gidana ba. Ke dai tunda kina samun ku'di fiye da ni, komai kike so ci akan abin da nake da ikon ba ki, ba zan hana ki ba. Amma ni kada ki ajiye, ko ki ba ni, bana so". Ganin da gaske baya so din, sai na daina. Iya abin da ya siyo shi zamu ci. Da na bi yadda yake so, sai muka samu dai-daito. Domin duk ranar da ya ga kifi ko nama alhalin ba shi ya siyo ba. To fa yini zai yi babu sukini da walwala. Sai dai wani zubin na kan auni mangyada ko manja na zuba a galan din namu, ko na sayi ledar maggi. Wannan bai cika fahimta ba. Tunda wani lokacin zai siyo gwangwani biyu a leda ya juye a ciki. Dan haka a duk lokacin da ya samu sararin siyo kwalba, kwanaki ka'dan nima zan sake siya na zuba. To baya ankarewa da hakan. Abin da na lura bai dauki maganar da

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161