Skip to content

Chapter 74

Chapter 74

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

"suna da kyau a wajen wata baiwar nake siyansa, ita ce ta zaba mini su, yayarku Sajida nake siyawa. Shekaranjiya na siya, jiya ta Sako mini a mota. FASEELAT da cika alkawari take, ga shi zata baka kaya masu kyau. Ga lambarta Dan nasan watarana zaki so ki sake siyansu" *07039269802* Na dai ce na gode, amma ba wani abu da zan yi akan Tijjani. Ta tafi babu jimawa ya dawo da leda a hannunsa. Ya zauna kusa da ni. Ya bude kamshin hadadden tsiren da ya yi shura a garin Toro ya bugi hancina. Yawun bakina ya tsinke. Amma na maze tamkar bai bani sha'awa ba. Sai da ya dinga ro'kona sannan na yarda na ci. Da daddare muka kwanta, bai nemi komai ba sai rungume ni da ya yi. Washagari da zai fita sallah ya ce zai wuce wajen aiki sai ya dawo. Na amsa da adawo lafiya. Na bi shi na sanya sakata. Sai wajen tara ya dawo. Shi ne ya tashe ni tunda k'arar kiran wayata da ya yi ne ya tashe ni. Yau bayan madara da milo har da k'wai guda hudu a ledar. Sai da ya yi wanka ya shirya cikin shudiyar shadda da ta sha guga, ga k'amshin turaren da ya fara sanyawa mai da'din kamshi ya baibaiye hancina. Yauma shi ya shiga kicin. Ya soyo kwan. Ya hado shayin da burodi ya kawo gabana. Muka karya. Sannan na yi nawa wankan. Da yake tsamin da jikina ya yi da sau'ki, kwalliya na yi mai sauki. Na kalli fuskata na ga ta d'anyace. Na sake yin fari. Shi kuma baya gajiya wajen kawo hannunsa jikina. Tun lokacin na gane jarabarsa ba k'arama ba ce. Washa gari ya yi sammmako ya fita. Duk tunanina gidan burodi ya tafi. Amma bai dawo ba sai gaf da maghariba. Kayan jikinsa ya tabbatar mini ba a wajen aiki yake ba. Ya mik'o mini ledar hannunsa tare da ce wa "Ga shi in ji Babarki." Ina jin hakan na fasa masa kuka har da dirowa daga kan kujerar. Ya tarairayo ni a gigice. "Saboda Allah fa kin girma Asiya. Yanzu ai kin wuce irin wannan kukan." Da kuka na ce "Amma na ce maka za ni, shine ka tafi babu sallama?" Ya sake rungume ni sosai. Ya sanya kansa a kan wuyana. Cikin rad'a ya ce "Sorry Asiyata. Daga yau bazan sake ba. Takanas ma zan shirya mana zuwa Bulkachuwa. Kwana nawa zaki yi?" A hankali na ce "Sati biyu". Ya lank'awasa harshe yana ce wa "Sati d'aya dai Sweetie". Daga hakan ya dinga kissing dina, har sai da na ji jikina ya amsa sosai, na zame na koma kan kujera. A hakan muka kwashe kwanaki hudu ban yarda an sake ba. A wannan ranar kuma ya rikice akan ya yi iya ha'kurin da zai iya. Kusan k'arfi ma ya sanya mini. Sai me? Gaba'daya sai na ji babu banbanci da na farkon wajen zafi da radadi, na rasa yadda zan yi. Na tattaro dukkan k'arfina wai akan na ingije shi, amma abu ya faskara. A wannan ranar kam har cizo na yi ta gasa masa. Amma bai sanya ya k'yale ni ba, sai da ya yi yadda yake so ya gama. Kukan da na yi a wannan dare ya zarta na ha'duwarmu ta farko. Hankalinsa ya yi mugun tashi. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya gaji da rarrashi ya zuba mini ido. Can ya nisa cikin rauni sosai ya ce "Asiya irin wannan bacin rai kamar wanda na yi miki fyade. Kin san k'uncin da nake ji kuwa. Kin san yadda kika tayar mini da hankali. Me zan yi miki kin rangwanta mini k'iyayyar da kike yi mini?" Jikina ya yi sanyi. Amma rad'ad'in da nake ji ya hana ni na daina kukan. Ya numfasa ya ce "Ki yi hakuri ko wacce mace da hakan ta girma." Da rawar murya na ce "Billahillazi bazan yi hakuri ka sabauta ni a banza ba. An yi na farko, an yi na biyu to kuwa ba za'a yi na uku da ni ba. Na riga na sani, baka iya yi da y'an k'ananun mata irina ba. Ka saba danne tima tima masu manyan halittu shi yasa nima kake gwada mini rashin imani kana ganin tamkar babbar mace ka samu". Jin ya yi shiru ya sanya na d'ago na kalle shi. Zuciyata ta tsinke a halin da na gan shi. Gaba'daya idanuwansa sun yi jawur tabbacin zuciyarsa ta b'aci ainun da kalaamina. Bai ce komai ba. Ya tashi ya bar dakin. Wanka ya yi, ya dawo dakin ya shimfida abin sallah ya tayar. Yanayinsa ya saka kukan ya tsaya cak. Na rasa gane tausayi yake bani ko kuwa mene ne? Washagari bayan ya dawo daga gidan burodi ya gama duk abin da zai yi mana. Ya kawo mini abin karyawar har d'aki. Fuskarsa babu walwala ya ce "Sai na dawo". Ban amsa ba. A dalilin kuttun da ya shak'e ni. Don me zai fita? Ba zai zauna ya kula da lafiyata ba. Ya tafi bai jira amsawa ta ba. Na dinga kuka. Zuciyata tana kissima mini ai ya samu abin da yake so shi yasa bai damu da ya tsaya na yi wanka ko na karya ba . Da rana ya dawo, ya zauna ya kalle ni. Yayin da ni kuma na d'aure fuska sosai. Ganin hakan ya mik'e shima fursakarsa a d'aure ainun ya ce " Ban samu ku'di na siyo abin da zaki ci ba. Me kike son ci na dafa miki?" Cikin son na wahalar da shi na ce "Faten doya da wake. Sannan da alaihu da kifi a ciki." Ya nisa ya ce "Ba ni da kudin da zan sayi kifi yau. Zan dai je na siyo alaiyahun. Ya fara tafiya da nufin fita. Na bu'de baki na ce "Zo ka kar'ba. Ni ina da kudin". A zafafe ya juyo "Cikin kaushin harshe ya ce "Asiya Toro baki da kudin da zaki yi mini cefane matu'kar ina da lafiya, ina kuma kan k'afafuna. Ba zaki yi ku'din da zaki aike ni, na siyo abu sannan na zo na girka miki ba, har abada kuwa". Ganin yadda ya rikice ya koma Bulkachuwan sa sai na yi maza na kame, domin na sani yana iya dauke ni da mari. Na laluba na kasa gane fishin me yake yi tun dare. To me na yi masa? Ni da ya ganawa azaba ma ban yi masa zafin kai ba sai shi zai dinga yi mini muzurai da hargagi?. Ya yi k'wafa ya fice bayan ya jira na tanka, amma na yi muk'us. Ina ta jin b'ab'atunsa a kicin. Ga mamakina sai ga shi ya kawo mini lafiyayen faten doya da wake a ciki. Ya ji alaiyahu da albasa mai lawashi. Nabi bayansa da kallo. A dalilin bai zauna ba fice wa ya yi. Ina jinsa a kan baranda ya zauna yake cin nasa. Haka kawai sai na ji guiltiness na kama ni to me na yi masa?. Da ya gama bai lek'o ba. Daga inda yake ya ce "Sai anjima". Na rasa gane manufar wannan abin da yake yi. Da daddare ma da ya dawo bayan ya yi wanka. Ya dube ni ya ce "Zaki ci donot da tea ne,

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161