Skip to content

Chapter 142

Chapter 142

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

inkarin hujjojin lauyoyin gwamnati tunda tabbas Tijjani bai yi bincike ba ya karbi kaya. Bai kuma bude ya duba ba. An ba shi abu a d'aure cikin buhu kawai ya danna a mota. Sannan bai san mutum ba. Kawai ance idan ya je Kano za'a karba a biya shi. Sannan lauyan gwamnati ya k'ara kafa hujja da ce wa "saboda Tijjani yasan ba shi da gaskiya ya dauko wiwi da koken mai nauyin tam goma shi yasa ya ki tsayawa da jami'an tsaro suka tsayar da shi wanda hakan rashin da'a ne da raina jami'an tsaron da k'asa ta wakilta su duba shige da ficen al'umma." Na zuba wa Tijjani ido da yana tsaye jikin kantar da ake tsayar da wadanda ake tuhuma. Ya zube aiun, ya sake yin duhu. Zuciyata ta karaya, na hangi rashin sassauci a shari'ar. Ta zo fiye da yadda muka tsammace ta. Domin maganarsa d'aya ce ba shi kayan aka yi, bai san kuma san mutanan ba. Lambar wayar da ya gabatar a matsayin wacce aka kira shi da ita bata yi. Jikin kowa ya yi sanyi. Bayan dogon rubutu da alkalin ya yi. Ya yi gyaran murya ya ce "Duba da hujjojin da lauyan gwamnati da kuna jami'an tsaro suka gabatar kotu ta yanke wa Tijjani hukuncin shekaru biyar a gidan yari babu tara. Bisa kama shi da safarar kwaya wanda hakan ya saba kashi na goma sha takwas b cikin baka. Bayan haka kotu ta sake d'aure shi shekara d'aya bisa cin zarafim jami'an tsaro da ya yi ta hanyar yi musu gaddama. Har ila yau kotu ta daure Tijjani na watanni uku ko tarar dubu ashirin saboda rashin kiyaye kaidojin kasuwanci. Ba zai yiwu mutum yana hulda da jama'a ba amma babu taka tsantsan da sanin me mutum ya dauko ko mai zai kai. Yana cikin dab'iun d'an kasa na gari ya zama yana duba komai yana kuma kiyaye dukkan doka." Ya rattaba hannu akan takardun tare da buga stamfi. Gabadaya ahalinmu hankaliinmu ya yi mummunan tashi. Ni kam kuka na ke yi mai gunza. An daure shi shekaru bakwai babu tara? Wacce irin bak'ar kaddara ce wannan? A harabar kotun muka tsaya da shi tunda Yaya Ammar na cikin ma'aikatam gidan yarin. Na kalle shi sai kawai na fashe da kuka a dalilin raunin da na ga ni ya bayyana masa a dukkan jikinsa da zuciyarsa. Muka zubawa juna ido ba tare da mun tuna daruruwan mutanen da suke wajen ba . A sanyaye ya ce "Asiya shekaru bakwai da yawa. Tashin hankalina bai wuce ke ba. Ba zaki iya ba. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun " Sai kawai hawaye ya ya k'wace masa shabe shabe". Na rik'e hannunsa na ce "Ko shekaru sha bakwai ne zan jira ka Baban 2. Idan har rayuwarmu ta kai zaka fito ka tarar da ni a dakin ka. Zan kiyaye maka amana, zan yi aiki tuk'uru na kular maka da y'aya'n ka. Jarumtar nan da ka ke fad'in na dinga yi, zan nin ka ta daga yau". Baban Marina ya dauke idonsa amma bai iya tsayar da hawayensa ba. Tijjani ya matsa kusa da shi ya ce "Wallahi ban aikata laifin da aka jingina mini ba, rami aka haka mini na fad'a. Ka taimake ni, ba zullimin hukuncin ne ya zautar da ni ba. Fargabar yadda zan iya rasa Asiya ne. Shekaru hudu ne gejin da shari'a ta dibawa mace akan dakon mijinta. Ni kuwa shekaru bakwai aka zarge ni". Hawaye ya cigaba da tsere babu kakkautawa. Baba ya kasa ce wa komai. Su Yaya Salisu kowa hawaye. Cikin k'arfin zuciya na ce "Idan ni ce matsalar ka, to ka kaddara baka da damuwa. Zan jira ka. Ba ka ce ko ka mutu na zama jaruma dan na tallafi y'aya'n ka ba? Zan kiyaye mutuncin ka, zan kuma maye wa y'aya'n ka gurbin ka har zuwa lokacin da zaka dawo ka cigaba da kulawa da mu gabadaya. Ka sa a ranka ban yi kokwanto akan ka ba Tijjani. Na gasgata ka, na yarda da kai." Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah ya k'ara lafiya Baba. A sanya ni cikin addu'a. Ni kuma ya mini murmushi kad'an ya ce "Na gode". Daga haka suka tafi da shi. Fir na k'i yarda na koma Toro. Domin idan ina gida tashin hankalina yafi yawa a dalilin ina ganin tamkar Tijjani ya rasu ko mun rabu. Bayan haka karatun yara ya dakata. Baban Marina bai matsa mini ba, jikinsa ya yi laushi ya kamu da mugun tausayinmu. Yaya Indo ta zauna da ni na kwanaki biyu. Komai ita take yi, ta ji da hidimar yara ta kuma yi girki da kwantar mini da hankali. Tun sanadin auren Nasiba muka hade da su. Gabadaya yan k'ofarmu muka dinke, muka dunkule, duk wani tsegmi ya yi s'auki tunda dama manyan namu ne karkatattu. Sai da Babah ta Bulkachuwa ta zo sannan ta tafi. Dada ce ta zartar da umarnin Babah ta zo ta zauna da ni. Cikin alhinin rashin Tijjani da kuma tausayi da kyautatawa muke zaune. Nasirun ta wanda shi Ihisan take bi a kai a kai yake zuwa mana domin dalibi ne a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da take cikjn Bauchi. *Toro*. Anas da yake bin Yabi. Yana bandakin k'ofar Dada yana simince shi a dalilin wanda aka yi mata da ta rubza ya farfashe, ba'a yi aikin aminci ba. Gabadaya Baba Maryo ta shafa'a shaf yana k'ofar, kuma kusa da kicin din da take zaune ne. Ta hau tonon murhun tana ce wa "Allah suturi buk'i da auren mazinaci kuma mai dilar k'waya. Wane mutum na had'a iri da shi cikin sanina?" Kalaman ta suka ja hankalinsa ya ajiye abin aikin ya leko tunda bayin ba me k'yaure ne ba. Ganin da ya yi tana tono ya sake jan hankalinsa k'warai da gaske, ya matso sosai. Yana kallonta k'yar. Ya jima yana zargin Yaya Bulkachuwa ba a bar shi haka siddan akan al'amarin Nasiba ba. Ashe kuwa hakane. Ya sandare cikin tu'aajjibi a lokacin da ya ga ta fito da laya a k'asan murhun ta kyasta mata ashana ta k'one. Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Allah na gode da baka k'addara mini ganin auren ta da mai arzikin bogi ba. Ban da ma dai batan basira me za'a yi ne da wanda aka yiwa bulalar zina a bainar nasi? Lallai na yi mantuwa mai yawa. To na tone ramin da na hak'a tun ban rufta ba. Dama Yabi ce ta dace da shi a wannan duniyar." Daidai lokacin Anas ya kasa jure wa ya yi gyaran murya. Ta waiwaya a ankare. Idanuwansu suka hadu, ta yi wura wura. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Shi kuwa sai ya ce "A dinga yin sara ana duban bakin gatari Baba! Da Yaya Bulkachuwa, da Adda Yabi, da kuma Adda Nasiba kamata ya yi ki dauke su abu guda. Ba wai ki nemi rugurguza zaman lafiyarsu dan bukatar kan ki ba. Kin cutar da su duka. Ita kanta Adda Nasibar ai dan ba yadda zata yi ne, akan dole ta bi ra'ayin ki domin tana da darhamin imani a zuciyarta. Ya fara hawaye ya ce "Duk duniya ki rasa wanda zaki yiwa kulunboto ya

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161