Skip to content

Chapter 143

Chapter 143

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

so diyar ki sai mijin d'iyar Baban Marina! Kaico da Bakar hassada, kaico da mutanan da suke da son zuciya, wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka? Asiri kika yi wa Yaya Bulkachuwa! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun " Sai kawai ya fito daga bayin a gigice ya zunduma ihu da dukkan muryarsa tamkar mace ba jarumin namiji ba. Domin ya riga ya gigita da abin da ya ga ni k'warai da gaske. Ta hau tafa hannu tana ce wa "Ashe a maza ma akwai makirai majununai? Zaka ga tsiya da tuggu kuwa! Zan nuna maka uban ka ma ya wuce ya tozarta ni, ya kwaye mini asirina. Zaka gasgata makircin mace aziman ne yau din nan". Sai kawai ta takarkare ta zunduma ihu mai tsananin gaske. Da yake Dada barci take, a firgice ta farka tana fad'in "Waye ya mutu Maryamu? Jin shiru sai kukan Anas da na autarta ya cika mata kunnawan, ita ma sai kawai ta fashe da kukan daga dakinta. Tana fad'in "Allah kasa basu harbe mini "Mai sunan manya ba. Lah ha ilah ha ilallahu! Mintina kalilan jama'a suka taru a k'ofar ta da Dada. Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gidan yayin da Baban Marina baya nan. Dan haka a sukwane suka bu sahun ahalin gidan da suke ta shigowa a gigice. Kowa sai tambayar ba'asin kukansu yake yi. Anas sai hadiyar zuciya yake yi ya kasa bude baki ya yi magana. Jikin kowa ya yi sanyi tare da sake shiga rudani mai yawa. Domin kowa yasan Anas ba mai hayaniya ba ne sannan yaro ne mai juriya da hak'uri na gaske. Sun tabbatar ba zai yi kuka irin haka ba tare da ya ga wata masifar, domin a lokacin da yake yaro ma ba mai fitina ko koke koken banza ba ne, bare kuma yanzu da yake da shekara ashirin da biyu, ya zama saurayi na sosai. Baban Kasuwa ya ce "Maryo mene ne haka? Me ya faru ya tambaya zuciyarsa na rawa irin ta zullimi. Ta kuwa karkace ta kara k'arfin kukanta ta ce "Ban san yana makewayi ba. Sai na afka bayin ba tare da na tambaya ko akwai mutum a ciki ba. Babu zato na ga Anas ya gogawa al'aurarsa sabulu yana wasa da ita! Na zauce na fito a sukwane ina hirji. Kunya tasa ya kasa fitowa. Sai yanzu ya yi jihadi ya fito, wai dan na yi masa matashiya akan haramcin hakan shine ya fasa mini ihu yana neman k'ulla mini sharri tunda dama dukkansu y'aya'n Alhaji sun tsananta mini akan Tijjani, mussaman y'aya'n Asma'u da ko gaisuwa sun yanke yi mini dan su nuna mini Yabi ta fini a wajensu. Amma ni ban ga laifinsu ba. Ubansu ne ya yarda ta ni irin haka." Sai ta zarce da sabo n kuka. Su Baban Kasuwa suka d'auki salati tare da ce wa "Muminin kare ne ashe kai. Kullum da kai ake kwatance a gidan nan da ma unguwar baki daya saboda nutsuwar ka da hamlnkalin ka ashe BAK'AR TA'ADAR da kake tafi ta yaranmu da ake yi musu kallon fitinannu ne! Duk yadda aka yi kai ne ka yiwa y'ar wajen Malam Kabiru fyade satin da ya wuce. Yarinya karama da ko magana bata iya ba, aka kasa gano mugun da ya aikata mata aika aikar ashe kai ne". Kuka ya tsayawa Anas cak. Ya Kalli Baba Maryo ya kalli Baban Kasuwa. Yana ta kissima sune k'ananu a cikin iyayensu amma sune suke kan gaba wajen ruguza gidan Marina. Bai gama nazarinsu ba sai ya jiyo Baban Tsakiya ya ce "A a tunda ba mu ga ya haike mata ba, bai kamata mu jingina masa ba, shaidar zina babban al'amari ne. Sannan idan aka ji maganar a bakinmu ai muma mun kunyata domin baza mu ce ba daga gidan nan ya fito ba. Kawai shata masa layi zamu yi da y'aya'nmu kada ya dinga b'ata manaa su bamu ankare ba tunda ya jefa kansa a wannan BAK'AR TA'ADAR ta istimina'i". Yara da manya kowa yabi Anas da kallon tsana da tuhuma. Duk Mama da kanta ta ce "Anas ba lallatacce ba ne. Na tabbatar bai aikata hakan ba Maryo". Sai lokacin ya samu kuzarin Budeibaki ya ce "A a Mama kada ki ce mata komai. Na riga na kai alkalanci gaban Ubangiji. Idan ya tabbata na yi abin d at fada to ku nema mini gafarar Allah. Na kuma yafe mata tozarta ni da ta yi, tunda ai ba hakan ya kamata ta yi mini ba. Idan kuwa ban aikata ba ta mini hakan to da ikon Allah ba zaki mutu da ido ba Baba Maryo ". Ta zunduma ihu tana d'ura masa ashariya. Bai rufe baki ba ya ce "Ganinta na yi ta tono mugun k'ullin da ta yiwa Yaya Bulkachuwa akan ya rikice akan Adda Nasiba. Tana fad'in ta fasa auren tunda dan k'waya ne kuma mazinaci. Ganin na ganta ta k'ona layar shine ta mini hakan. Ba zan zage ki ba, ko a lahira wani kan ci arzikin wani. Ban ci arzikin ubana a wajenki ba. Nima ba zaki ci nasa ba. Kin ci arzikin kasancewar ki uwar Yaya Ammar. Ba dan shi ba, ina rantse miki da girman Ubangiji sai na miki dukan da ko Dada sai ta yi gaske da ta shaida ki. Amma babu komai na barwa Allah komai." Ya mik'e yana tangadi yayin da kowa ya yi tsit. Ya kalli Baban Kasuwa ya ce "D'a na kowa ne Baba". Baban Kasuwa ya ce "Ni kad'ai zaka fad'awa hakan, shima Baban Tsakiya ai ya tofa nasa" Anas ya ce "Ko ya tofa dai bai mini k'azafi ba, gaskiyar fahimtarsa ya fad'a. Dada tana bakin k'ofarta tana kurshegen kuka tana fad'in "Dambarwa ta tsananta a cikin ahalina. Ubangiji na ci albarkacin sallah da salati, ka sassauta, yafe mini, ka shirya mini zuria gabadaya". Har aka gama wannan cecekucen Baban Marina da Gwaggo basu tofa ba. Mama ce ta shiga lamarin ta yi kane kane tunda yanzu yar tsama ce mai tsananin gaske a tsakaninta da Maryo. Baya ga hakan kowa yasan Anas ba zai yi abin da ta fad'a ba. An kuma gasgata shi,asirin da yaga ta tone.ne ya ya sanya ta yi wannan dibar albarkar. Nasiba kuka ba wanda bata yi shi ba. Ammar da yake BAUCHI da ya ji labarin bai dauke shi da muhimmanci ba. Murnar yadda ta kunce k'ullin da ta yi yake yi. Domin yana matukar tausayin yadda Bulkachuwa yake damunsa ya kawo masa Nasiba ya ganta. Yanzu kuwa tunda an warware zai daina, zai samu nutsuwa, tunda wani lokacin har susuce wa yake zufa na karyo masa. Da labari ya zo mana Babah ta ce mini "Tare ta hada ta mana ai, ni tun kwanaki na kubuta. Nawa a kasan randa aka yi mini ta yadda zan zama mai sanyi akan sha'anin. Sannan aka danne mini zuciyata. Shi kuwa a k'asan murhun. Matukar aka hura wuta a murhun ba shi ba sukuni idan bai ganta ba. Kai wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka? Ta fara hawaye. Na taya ta muka yi kukanmu sosai domin ta ba ni tausayi. Da ciwo kwarai ace d'an-uwanka ne zai musguna maka irin haka. A raina kuwa na yafe dukkan musgunawar da Tijjani

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161