Chapter 57
Chapter 57
fork guda biyu. Ya zauna ya ja plate daya gabansa ya bu'de murya ya ce "Bismillah Amarya". Na bata rai na ce " Asiya Toro dai. Ina na kai darajar amarya bayan ni din yarinya ce kwaila kuma kankanuwa". Ya murmusa ya ce "Oh wai maganar ciwo ta yi miki ne? Tsakani da Allah ba gaskiya na fa'da ba? " Na girgiza kai ba tare da na kula shi ba. Na sauko na ja abincin da yake jirana. Na kai bakina duk kushena ban isa na ce ga inda girkin yake da tasgado ba. Na dinga zura loma. Sai da ya ga na kusa cinyewa ya kaikaice ya ce "Asiya Toro iyashegen ki yawa gare shi. Jibi yadda kike zabga loma kina zare ido. Me ya janye tunanin zan zuba miki wani abu a ciki Kuma? Kunya ta kamani ka'dan. Amma na daure na yi kamar ban ji komai ba. Na share shi. Sai da na gama na yi gyatsa, na kalle shi na ce "Na tabbatar da Yaya J ne ya dafa abincin nan, zubowa zai yi a waje daya. Sannan ya manta cikinsa har sai ya tabbatar nawa cikin ya cika." Na saci kallonsa na ga har wata zufa ce ta karyo masa. Zuciyata ta fara harbawa da tunanin hukuncin da zai yi a dalilin yadda yanayinsa ya nuna maganar ta buge shi. Ga mamakina sai kawai ya yi yak'e ya ce "Ba ki yi karya ba Asiya! Domin jiya mun je gidansa ni da Salisu a dalilin an sace mashin dinsa. A gabanmu ni da Salisu yake tarairayar Maijidda akan ta daure ta ci ayaba. Kinsan cikinta ya tsufa ba komai take iya ci ba. Ai Jabir kam yana mutuntunta maganar tsohonsa akan Maijidda. Sosai yake sonta yake tattalinta. Har mamaki na dinga yi tare da shakkun idan har ya taba son wata mace kafin ita. Ita ma bata jin kunyar mu din yayunta ba ne sai tabara take yi masa son ranta. Take na gano mata irinsu ba zasu ta'ba barin mijinsu ya yi tunanin wata macen ba. Wanda duk ya samu irinsu ya gama morewa, ga cikar halitta ga shagaba ga kuma biyayyar iyaye da aure. Wanda bai samu irinsu ba ai zai dauwama cikin cizon yatsa ne. Sannan tagomashin biyayyar da suka yiwa iyayensu ya sanya gidansu ya zama gidan farin ciki." Maimakon na b'ata masa rai, sai ya zamana nawa ran ne yafi b'aci. Bayan kod'a Maijidda da ya dinga yi, tare da kwarzanta ta, sai na fahimci yarfe yake yi mini akan ban yiwa nawa tsohon biyayya na mutuntata aurena ba. Na yi shiru na kasa cewa uffan. Ya gaji da jiran kalamina, ya tokara ya tashi. Bai dauke kwanon da ya ci ba, bare ya ha'da da nawa. Ya bar gidan ba tare da ya yi mini sallama kamar yadda ya saba ba. Tun da ya fita bai dawo ba, sai bayan sallar isha. Ga mamakina sai na ji haushin hakan. Rashin dawowar tasa ta mintsinin zuciyata sai dai ban bari ta bayyana akan fuskata ba. Ya leko ni, ina zaune a daki. Bai shigo sosai ba. Ya ajiye mini leda ya juya bayan ya ce "Sai da safe". Bansan ya aka yi ba kuka ya k'wace mini. Ni da kaina ban san dalilin kukan ba. Amma so na yi ya shigo yana lallaba ni, da ro'kon na ci abin da ya siyo, ina botsare masa. Ko duba ledar ban yi ba, na yi kwanciyata bayan na rufe k'ofar dakin. Cikin dare na tashi da wata azababbiyar yunwa. A gigice na janyo ledar na hau cin awara irin manyan nan ga kabeji. Da k'yar na iya janyo leda a lungun gado. Maman kawata Shafa'atu ce ta je Kano ta siyo yajin Annur food mai dan karen dad'i. Shine ta ba ni roba d'aya. *Annur food Delicious* *Ba iya yaji ba har da garin danwake da man Shani, da yajin daddawa* *Tuntube su a wannan lambar dan k'arin bayani 08039183880*. Na sani sadda ya kawo da zafinta. Sai da na cinye tas, sannan jikina ya daina rawar yunwa. Take na tuno ashe jiya iya taliyar nan kawai na sanya a bakina. Na jima barci bai dauke ni ba. Sai kawai na yanke shawarar na doro alwallah na yi nafilah. Na mike ina da tabbacin Gwaggo na kan sallayarta a irin wannan lokacin da bayi suke barci. A hankali na zare sakatar na fita. Abin mamaki sai na ga Tijjani akan barandar yana sallah. Yana sujjada. Na dakata ya idar tunda ba zai yiwu na wuce ta gabansa ba. Na jingina da kyauren kofar dakin nawa. Ina kallon yadda ya kyautata sujjadar. Tsawon lokaci bai dago ba. Wani abu ya sake tsirga mini a kansa. Na tuna a duk sadda Gwaggo ta tashe ni cikin dare dan mu yi nafila. Cewa take yi daure ki tashi ki nemi yardar Ubangiji Yabi. Irin wanna lokacin sai zababbun bayi ne suke rabauta da yin ibada. Duk kuma abin da mai yin ibadar dare yasa a gaba sai ya ga sau'kinsa. Allah da kansa yake saukowa sararin subhana yana shelar ina mai bu'kata na biya masa?" Zuciyata ta sake harbawa domin ni kaina da bana son Tijjani. Kallonsa yana sujjadar nan sai da na ji wani irin abu, to ina kuma Ubangijin da ya kyautata sujjadar saboda shi. Har lokacin kuma bai dago ba. Na sake tuna jawabin Gwaggo da take fadin kada ki ce sai kina cikin damuwa ko bu'kata zaki yi sallar dare. Domin idan ta zame miki dabi'a, to lah shakka duk wata bak'ar k'addara da zata zo miki, sai ta zo da sau'ki, sannan komai kika roka zaki ga biyan bu'kata duk nisan jinkiri. Ban da ma dai dan adam mai shagala ne, ai ya kamata ace yana yawan yin godiya ga Ubangiji bisa dinbin niimomin da ya masa. An yika musulmi, an baka lafiya, an kuma hore maka abin da zaka ci komin kankantar sa. Ashe kuwa ba sai da damuwa za'a yi ibada ba. Na nisa ina jin na fara gajiya da dakonsa. Har zan koma daki sai kuma ya d'ago. Na dinka fatan ace sujjadar karshe ce ba zai koma wata ba. Ai kuwa sai na ga ya zauna, alamun attahiyatu yake yi. Ina ganin ya sallame na yi maza na wuce a dalilin fitsari ya kama ni ba ka'dan ba. Yana zaune har na fito na shige shi. Sai dai Ina wuce wa ya sake mikewa tabbacin dama ya jinkirta mini ne na wuce. Raka'a biyu na yi mai dauke da gajerun surori. Na yi yan adduoina. Ban san me yasa na kasa addu'ar da nake nacin yi ba. Na Ubangiji ya tarwatsa aurenmu. Na tsinci bakina da fa'din Àllah ka mini zabin da zai fi mini alheri. Karon farko da na yi addu'ar da dukkan zuciyata. Na yi addu'oi, na yiwa mahaifana addu'a, na ha'da da al'ummar ma'aiki. Na koma na kwanta ina fa'din "da wanda yayi doguwar sujjada, da wacce ta yi gajeriya, Allah dai ake yiwa, to Ubangiji ka karba mana gaba'daya". *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161