Skip to content

Chapter 79

Chapter 79

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

amma idan kika cije ni, ko kika yi mini fallashasshen kuka. Ki tabbatar kina cikin komar mala'iku". Na yi shiru. Amma zuciyata sai harbawa take yi. Domin har zuciyata nake jin tsoron al'amarin. Ina ji ina ga ni, ya shiga yin yadda ya ga dama da ni. A farkon tafiyar gaba'daya na kankame jikina ina sauraron jin matsanancin zafi. Amma ga mamakina sai ban ji ba. Har na sakankace na saki jikina. Wanda hakan ba k'aramin dadi ya yi masa ba. Ya k'ara haifar masa da kuzari mai yawa. Dan haka lokacin da ya shafe yana abu daya, bai dame ni ba. Bayan ya nutsu. Ya rungume ni yana ta faman sakin kalaman yabo da soyayya. "Asiya da hakan kike yi mini, to me zai sa ma na yi fishi da ke? Bare har na yi tunanin k'arin aure. Na gode sosai, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwar ki gaba'daya." Na yi shiru. Amma zuciyata sai kai kawo take yi akan abin da nake son amayar wa. Na kasa jarumtar ha'diyewar murya babu amo na ce "Yo ni ai tunda wula'kanci ka shiryo mini daga yin aure za'a ka fara neman wani dan kawai ka nuna wa duniya bani da wata kima a idonka. Wallahi ba zama zan yi ba. Zaka wayi gari ne ka ga na bace maka." A diririce ya sake ru'ko ni sosai tare da ce wa "Kar ki tayar mini da hankali dan Allah. Na fasa, dama dan na rasa yadda zan yi ne. Amma yanzu indai kin daina yi mini abubuwan da kike yi. Wallahi bazan sake tayar da maganar ba. Ke ko hanyar da ta bi, bazan sake bi ba". Cikin kuka na ce "Daga baya ke nan. Wadanda suka ganka kana zuwa tadi ai tuni sun san baka son Yabi. Dan haka kuwa ba yarda zan yi ba. Ka je ka cigaba da abin da kake yi, ni ma zan samu mafita Wallahi". A raunane ya ce "Bana son kukan ki Asiya! Amma sai ki ta yi mini, dan kawai ki gigita ni. Ban iya yaudara ba. Na ce miki, na fasa, na janye, to ba shikenan ba?" A zabure na ce "Ba shike nan ba". "Da azama ya ce "To fa'da mini yadda za'a yi, me kike so na yi dan ki gamsu?" Na dinga gunjin kuka da na tabbatar yana jijjiga shi. Ya dinga shafa kaina, yana fa'din " Sorry Asiyata! Na ce bazan sake ba, ki yi ha'kuri da gaske na fasa. Dan Allah mu rufe maganar nan haka. Me kike son ci na dafa miki?" Na fara kokarin fizgewa daga rugumar da ya yi mini, amma na kasa. Cikin tab'ara na ce "Bazan ci ba. Yau kwana nawa rabon ma da ka tsaya ka saurare ni akan maganar abinci. Ko na ci, ko kada na ci ai babu ruwan ka". Ya sake sassauta murya ya ce "Wula'kanta ni fa kike yi. Ta ya ya zuciyata zata ji da'din kyautata miki? Yanzu kuwa ai komai yi miki zan yi da kaina". Na cuna baki na ce "Abar maganar abinci. Ka tashi tunda ruwan ya tsaya, ka kwaso kayanka da ka kai mini wanccan d'akin dan kawai kana nema na da jidali". Ya zabura ya tashi. Ya lalubo jallabiyarsa ya d'ora akan gajeran wandon bai ce komai ba ya fice. Ya kwaso su tsab. Ya mayar dasu inda suke. Ya juyo ya ce "Na kwaso, shike nan?" Na bata rai na ce "Ba shike nan ba. Kada mu samu sabani ka sake yi mini hakan. Tijjani ba ruwanka da d'akin can. Nan ne dakinka. Idan kuma zaka dinga fitina ta akan dakin to ka sani zan tattara kayan gadon na mayar maka can din. Tunda nan d'akina ne da shari'a ta ce ka bani shi tilas. Idan anan nake sana'ata ban shiga cikin dakin ba, ai na tsira ko?" Ya yi wani irin murmushin da na fahimci mai harshen damo ne. Ya numfasa ya ce "Namiji ai ba yi masa shamaki a gidansa. Dan haka mu zauna lafiya mu mutuntata juna shine kawai. Amma bazan yarda ina tattala ki, ke kuma ki ce zaki dinga wula'kanta ni, sannan kuma na yi miki yadda kike so." Ya girgiza kai ya ce "Ba haka Tijjani yake ba. Ba kuma zai zama hakan ba". Na kura masa ido na tabbatar iyakacin gaskiyar sa ya fa'da. Na rasa me zance masa domin na tabbatar duk bala'ina. Idan ya kunsa mini ba'kin ciki daya tak kwana zan yi na yini cikin ba'kin ciki mai tsanani. Dan haka sai kawai na buge da sake fashe wa da kukan. Daga inda yake tsaye, ya ce "Allah dai ya taimake ni ki hau ko na samu sau'kin wannan rikicewar da gangan. Idan kina ganin baby a hannunki wata'kila kya daina yi irin wannan sakalcin." Yana rufe baki na fara nuna kaina cikin kuka ina ce wa "Tijjani ni ce sakaliya?" Kafin ya amsa mini na rausayar da kai na ce shike nan na gode da wannan tukuicin". Ya taho da sauri yana kuma dariya. Ya rike k'afafuna ya ce "Ina nufin sakaliyata fa". Na yi tsuka na juya. A sanyaye ya ce "Bana son tsuka Asiya. Amma na yafe miki, ban yi fishi ba". Daga hakan ya koma ya fita. Na tabbatar kuma kicin zai shiga. Ni dai daga nan barci ya sure ni. Sai bu'de ido na yi na ganshi ya yi wanka ya shiraya tsab. D'akin ma ya cika da kamshin turaren nasa. Yana daga jikin sif din yana saka links ya ce "Yanzu dama zan tashe ki, na kai miki ruwan wanka". Ban ce komai ba, na tashi, na daura zani a kirji sannan na saki zanin gadon na sauko. Ya kalle ni babu riga a jikina. Ya ce "Asiya Toro a gabana babu riga. Sai na sake ganin ki wata yar kwaila, a hakan tamkar ba zaki iya komai ba. Nan kuwa al'amarin da yake tare da ke azimin ne". Na cuna baki na ce "Ai ni na gode Allah ma da aka baka yar mitsil din. Kai da rusa rusan mata sai kallo daga nesa. In juninka cusawa mutum takaici ne. Har abada kai da zunduma zunduman mata". Ya murmusa duk da dai yana kokarin shanye dariyarsa. Ya ce "Wato baki ji da'din yabon da na yi ba, sai kika dauki abin da bai yi miki da'di ba, kika yi raddi?" Na share, na dauki tawul na fice abina. Na dawo na tarar da shi ya gyara gadon tsab. Ya share dakin. Na kasa hakuri na ce "Tijjani wai a ina ka iya gyaran gado ne, tunda kullum dakinka na gida a hargitse yake, sai asarrariyar can ta gyara maka shi yake yin fasali". Ya dauko mai yana murmushi ya tarar da ni a bakin gadon. Na yi kamar na hana shi shafa mini mai din sai na fasa kuma. Domin a dan zamanmu na fahimci yana matu'kar son ya shafa mini mai, kafin na sanya komai a jikina. Ina ji ina ga ni ya dinga shafe ni da sunan shafar mai wanda ni kaina ina matu'kar jin sakon nasa a dukkan jikina. Yana cikin murzar tafin kafata. Wanda kafin ya zo kafar ya shafe mintina sha biyar. Murya dakushe tabbacin so yake ya

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161