Skip to content

Chapter 76

Chapter 76

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

"Ni a siffofin munafiki ai har da sab'a al'kawari ko?" Da budaddiyar murya ya ce "Eh" , sai kawai ya shammace ni ya dauke ni da mari". Na zunduma ihu ina ce wa "Manzallazi ya saka mini akan wannan zaluncin da kake yi mini". Ya ce "Idan zaki zage ni sau dubu. Ni kuwa zan d'aga miki hannu sau dubu. Shege ka fasa a tsakaninmu. Kuma idan kin cika marar kunya ce ke, to ki shiga mini d'aki da nufin yin k'unshi, ki ga kalar tawa rashin kunyar". Na kasa ce wa komai illah kuka sosai da nake yi. Bai damu da kukan ba, ya saka kai ya fice. Asarar da na yi, a yinin wannan ranar ba ka'dan ba ce. Domin kuwa mutane sun fi goma da suka zo k'unshi ina sallamarsu. Gara ma na yiwa yara uku kitso a falo. Sau uku yana kewayo wa ko zai tarar na shiga, ya wula'kanta ni. Sai kuma ya ga duk zuwan da zai yi bai ga kowa a ciki ba. Kwana biyu muna wannan takun sak'ar. Ga shi na ji a bakin Rafi'a ana ta tumfirint din Neco. Kwana na uku na same shi a d'akinsa da daddare na zauna na sassauta murya na ce "Tijjani ka ce "Zan yi Neco ga shi ana fa'din an kusa rufe yin rigista da tumfirint din". Kai-tsaye ya ce "Na fasa fas. Dama ai ba wai karatun ya dame ki ba ne. Ni ne a kokarin na sanya farin ciki a zuciyar ki ya sanya na ce zaki yi. Ina kuma da sha'awar mace mai ilimi. Yanzu kuma na fasa tunda baki da abin wula'kantawa, sai ni". A sanyaye na ce "Dan Allah Tijjani tunda ka saka mini rai ka bar ni." Ya ja tsaki ya juya ya cigaba da kwanciyarsa. Na tsura masa ido ina jin zuciyata tamkar ta fa'do. Wato ko wanne namiji ya iya tsiyataku masu k'ona rai. Na dinga mamakin me zai sa wula'kancinsa ya yi mini ciwo ne?". Na tashi na bar shi, zuciyata tamkar ta fa'do k'asa. Kullum fishin nasa gaba yake yi ba baya ba. Gaba'daya ya fitittike ya koma wanccan Bulkachuwan da yake dauke kai ga mace in ta nemi yaga shi. Magana ma da k'yar yake yi mini. Tsakaninmu ya shigo mini da cefane. Idan ya samu sararin siyo kayan masarufi kuwa, sai dai na ga yawansu ya k'aru. Ya daina sauraron abincina. Ya kuma daina tambayar me zan ci. Da ya gama uzzirinsa zai sa kai ya fice, nasan dai bai ta'ba fashin kawo mini cefane ba. Sannan bai damu sai na ba shi idan na girka ba. Ranar da babu gidan burodi kuma bai samu aikin da zai yi ba. Zai dawo ya ce mini ki yi wake da shinkafa ko ki dafa taliya da manja. Shi kuwa sai ya jika garin rogonsa ya sha, ya sake fice wa. Wani lokacin tausayinsa ya hana ni sukuni. Na rasa yadda zan yi da shi, ya k'ulla gaba mai yawa a tsakaninmu. Rannan ya ce mini "Ya tafi Bauchi. Da'di ya ratsa ni, domin zan samu na dan yi k'unshi kafin ya dawo garin. K'warai na takura a halin da nake ciki. Ai kuwa mutum uku suka zo, na kai su dakin bayan na kintsa masa kayansa gefe guda. Na dauko bedsheet na rufesu. Na gama yiwa mutum biyu, ina cikin sakawa ta uku. Tamkar jifa sai buga k'ofa na ji. Ban kawo shine ba. Tunda ya ce ya tafi Bauchi. Nasan kuma sai wajen dare zan gan shi. Na fita da sauri ina zaton ko Anas ne. Ina bu'de kofa kawai na ga mutum a tsaye. A gigice na ce "Tijjani ba ka tafi Bauchin ba?" Fuska a daure ya ce "Allah bai yi ba". Na tare hanyar shigowar. Ya ce "menene haka, ba ni hanya band'aki zan shiga". Na diririce. Baki na rawa na ce "Dan Allah, dan darajar Annabi Tijjani ka rufa mini asiri, ka yi hakuri kada ka shiga d'akin lalle. Ya galla mini harara ya ce "Yau munafurci ya tabbata a kan ki, kuma zaki ga k'arshen rashin mutunci Wallahi". Na zabura na ri'ke shi sosai. Murya na rawa na ce "Ka yiwa Àllah da Manzonsa kada ka yi mini haka. Na yarda komai ka ke so zan yi, amma kada ka sake tozarta ni Tijjani". Ya zuba mini ido yana kallon yadda hawaye yake tsere akan fuskata. Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan". Sanin bai iya yaudara ba, ya sanya na sake shi ya shiga, ina bin sa a baya. Domin da zai shiga d'akin, ba zai nuna mini ba zai shiga ba. Kai-tsaye falo ya dosa. Na samu nutsuwa a zuciyata. Tsabar nutsuwar da na samu har ruwa na dauko masa. Na kawo masa abincin da na dafa zan ci. Ya hakince tamkar wani basarake. Yana cin magani, komai isa isa yake yinsa. Haka dai na lallaba shi, ya koma harkokinsa. Yana fita na saki gauron numfashi. A fili na ce "Oh Allah. Menene damuwata ne akan abin da zai yi a d'akin da nake shiga zullumi idan zai shiga din?" Na kasa bawa kaina amsa. Na kalli mashin dinsa da yake gefe wanda bai fita da shi ba. Yana fita wasu zugar suka zo. Dan haka har kusan magariba sannan na gama saka musu. A gurguje na yi wanka. An fara kiran isha wacce na saka wa a karshe ta cire ta tafi. Na dinga jin da'din ku'din da na tara. Da na nutsu sai na gane, idan ban dauki matakin dai-dai to a tsakanina da Bulkachuwa ba. Asarar da zan dinga yi a kullum ba ka'dan ba ce. Ba'kin cikin rashin bishiya ko rumfa yana cina. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Ga shi yanzu yanayin damina ne. Idan ruwa bai zuba ba rana ake yi, idan kuma an yi ruwan ba damar zama a waje. Ya shigo na ha'diye haushinsa na yi masa sannu. Na kawo donot da flask din shayi. Sai da muka kammala. Na dauko dukkan cinikin da na yi a ranar. Na tura gabansa. Na sassauta murya na ce "Tijjani ka ga cinikin da na yi yau ka'dai. Na ro'ke ka daina hana ni. Na yarda kullum kana da kaso a cikin ku'din da zan samu". Ya fusata irin sosai din nan. Ya nuna ni da hannu. Ya ce "Ke ce kike mutunta ku'di irin haka. Na kuma sha fa'da miki ce wa baki da kudin da zan sa ido akansu bare har ki yi mini iyashege saboda su. Ya jijjiga kai ya mike tsaye bayan ya dangwarar da kofin shayin.

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161