Skip to content

Chapter 94

Chapter 94

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

matsanancin mamaki. Sai kuma dariyar da bai shirya ba ta sake k'wace masa. Ya dinga yi, ni kuwa na ce "Yi dariyar ka son ranka. Allah ne ya ara maka dama. Ka zuba ruwa a k'asa ka sha. Ka same ni da yawa". Ai kuwa ya jima yana yi, sai ya yi shiru sai ya kalle ni ya ce "Ah aha". Ko ya ce ",Na k'i yi miki ciki ko Asiya?" Sai ya sake kyalkyale wa da dariya. Sai da ya nutsu ya ce "Little ki daina yi mini wuta wuta kin ji. Idan kina son ki damke ni, kawai ki kiyaye abin da bana so. Ki kuma dage wajen yin abubuwan da nake so. Ciki kuwa zan miki, ki k'ara hak'uri lokaci ne kin ji". Na ce "To! Amma kai ma kada ka sake ce wa na tafi gida. Ai kasan Baban Marina ba dad'i zai ji ba. Ni kuma magauta su tisa ni a gaba da habaici da gori." Ya kankame ni ya ce "Har abada ba zan sake ce wa ki tafi ba Asiya. Duk laifin da zaki yi mini kuwa. Matukar kin yarda na haramta miki zuwa gidajen mutane da sunan sana'a. Bana so, ba kuma zan dauka ba". Da azama na ce "Bazan sake yi ba har abada". Dad'i ya kama shi ya dinga kissing d'in kunne na, yana fad'in "I cherish you dear " *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* *Watanni shida a gaba*. Zuwa lokacin duk kaucen kaucen Tijjani na kada na shiga harkar ri'ke masa gida ta ci tura. Duk yadda baya son ya karbi ku'dina abin ya faskara domin samun ku'di ba k'aramin wahala yake ga talaka a wannan lokacin da aka janye tallafin mai a Nijeriya ba. Mafi yawa masu kananun sana'u sun shiga halin ni y'asu bare kuma wanda sana'ar sa hab'o ce ma'ana sai an samu za'a yi. Duk da k'arancin shekaruna na fahimci matu'kar Tijjani zai fita ya dawo gida ba tare da ya ru'ko wani abu komai kankantar sa ba, to kuwa a wannan ranar ba zan gane kansa ba. Duk yadda zan yi masa rawar jiki da haba haba dan na samar masa da nutsuwlar bai gaza ba, ba kuma laifi ba ne dan ya fita ya dawo bai samo wani abu ya kawo mini ba. Kullum sai na fa'da masa cinikin da nake yi da nake samun makudan k'udade na yi imani mafita Ubangiji ya kawo mana, domin ba ni ka'dai ba ce wacce ta iya lallai a garin Toro. Amma duk macen da ta tunbatsa, duk macen da ta isa ko ta kai ta kawo to kuwa wajena take yin k'unshi da kitso. Sannan mafi yawa basa ba ni adadin ku'dina sai sun yi mini k'ari. Idan ya bu'de baki sai ya ce "Ko ke ce Zainab Shamsuna ai ba'a ce na zauna na nad'e k'afar wando ki yi mini komai ba. Ubangiji ya ce na ciyar da ke, na tufatar da ke gwargwadon k'arfina." Na nisa na ce "Haka ne! To a maimakon ka dinga tayar da hankalinka, nima kana tayar mini da nawa. Mu yi wata ka'ida mana". Ya zuba mini ido yana saurarona. Na ce "Ka dinga siyar da lalle da mahallabiya da salatip. Ni kuma sai na dinga siya a wajen ka. Pure water ma da nake siyar wa sai ya koma naka ne zan dinga siyar maka". Ya ce na yarda zan siyar da lalle amma ba zan siyar da ruwa ba tunda ai fridge din ba nawa ba ne". Na ri'ke hannunsa na ce "Ashe kayana ba naka ba ne? Rannan a kunne na wata cikin y'anuwana take ta fa'din matu'kar mace da namiji igiyar aure ta zarge su ai komai da suke da shi ya zama mallakin junansu. Ta kalli idona ta ce mussaman idan ta haifa masa y'ay'a to ba wani sauran iyaka a tsakanin abubuwan da suka mallaka." Na nisa na ce "Kana nufin wannan yarfen da aka yi mini, ni da kai ba kamar sauran ma'aurata ba ne? Abuna ba naka ba ne. Kai ma abin ka ba nawa ba ne saboda ni ban haihu ba?" Na fa'da da rawar murya. Jikinsa ya yi sanyi ya janyo ni jikinsa ya ce "Kina dai son ki yi mini rikici ne little ban da haka menene abin kuka? Duka ma shekarar ki nawa ne? Ni fa a halin da nake ciki ma ban shirya karban bebi ba. Hidimar ki ka'dai tana gagarata ina kuma da jariririn da bai san babu ba. Amma idan haihuwar ta zo ina so, kawai dai zan so ace bebinmu sun zo a lokacin da komai ya dai-daita mini ta yadda zan musu hidima sosai". Na yi shiru na ce "Ka sare da yawa ne. Amma da sannu Allah zai kawo mafita." Ya saki gauron numfashi ya ce "Ai al'amuran k'asar ne ya lalace komai sai da hanya, hanyar ma sai ka biya makudan k'udade kafin ka samu aikin gwamnati." Na ce "Idan Allah ya k'addara abu rabon bawa ne komin tsanani sai ya same shi". Da haka na lallaba shi na samu kwanciyar hankali, domin ni rashin ku'dinsa baya damuna irin idan ya takure ya k'i sukuni. Nafi son soyayya, nafi son walwala. Bana kuma samun hakan sai idan yana kawo wani abu, domin ya riga ya k'yamaci ace ni ce nake ciyar da mu. Washagari da wuri ya fita. Bai dawo ba sai yamma lis. Wani abun mamaki da buhun sabon lalle irin mai L din nan ya dawo har buhu uku amma d'anye ne. Na kalle shi na ga ya yi laga laga. Tabbacin da kansa ya shiga jeji ya samo. Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni. Hawaye ya cika mini ido, a zuciyata sai addu'a nake yi masa akan Ubangiji ya hore masa hanyar da zai ri'ke gidansa cikin sau'ki. Da k'yar na ha'diye kukan nawa na dinga yi masa sannu. Ya zauna akan baranda ya ce "Asiya na gaji sosai ga k'aya ta yi ta suka na." Da tausayi na ce "Sannu, Ubangiji ya baka lada, ya kuma sanya wa neman ka albarka." Na dauko masa ruwa ya sha. Na kalle shi ya yi kaca kaca da shi.

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161