Skip to content

Chapter 135

Chapter 135

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

biyu tak a duniya Malam ya siyo mini ita tare da katangar wankan jegon ki. Amma yau kika fasa mini da gangan?". Ita kuwa tunda ta fasa gumi yake yanko mata. Wani irin abu tamkar kiyashi take jin yana sauka daga kanta. Bakinta ya yi nauyi ainun. Daidai lokacin da Innarsu Ubaida ta shigo yiwa Dada sallama zata gidan suna. Tana ganin ruwa ya jik'a tsakar gidan ga fasasshiyar randa ta hau jaje tana ce wa "Yanzu randar nan mai kafirin sanyi yau ta hadu da ajalinta?" Da kuka Dada ta ce "Eh kuma kisan wulakanci da rainin wayo a hadu da shi. Ta ajiye ledar kayanta, ta shiga kwashe rugurguzun randar. A nan ta ga k'atuwar laya. A tsorace ta ce "Dada a 'kona wannan ko ta tsari ce?" Murya babu amo ta ce "Jefa ta a wuta bansan ko ta mece ce ba. Gidan nan kam ai tuni Malam ya kafe shi. Ba dai mugu ya ga kofar shigowa ba. Ai kuwa ana kona layar Baba ta ji nauyin da zuciyarta ta yi ta ware. Sanyin da yake ratsa ta na tsoro da zullimin yin jayayaya ta ji duk ya gudu. Ta dinga Hamdala. A zuciyarta kuwa sai gasgata surkulle a ka yi mata ita kanta. A haka Tijjani suka shigo tare da Nasiba asibiti suka je yin gwaji. Bin su kawai take yi da ido. Bak'inta sai ambaton "Hasbunallahu wa ni'imal wakil yake yi. Zufa kuma bata fasa feso mata ba. Gabadaya ta shiga alhinin BAK'AR TA'ADAR da y'ar uwarta shakikiya ta aikata a dalilin son kai da na zuciya. Ta zuba ido tana nazarin Tijjani. Gabadaya ya kasa sukuni. Idonsa ya kad'a tamkar gauta. Shima sai zufar yake yi. Ya gaishe ta a sanyaye. Ta amsa masa murya babu amo domin gabad'aya ta duniyata ta yi mata tsanani. Jira take ta ji ya yi sallama ko ta fita. Amma yana zaune, duk da bai sake Bude baki ya yi magana ba. Duk takalarsa da magana da Dada take yi. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Ya dai gaishe ta a gajarce. Tsawon lokaci yana zaune. Rigarsa ta jike ta gaba saboda yadda zurlfa take keto masa tamkar mai hadiyar kunama. Fiye da shudewar mintina talatin yana zaune ba ya um ba ya um um. Gabadaya Babah ta shafa'a da miyar da take yi wa Dada. Sai tashin kauri suka ji a hancinansu. Da azama ta yunkura ta sauke. Sannan ta janye wutar ta kashe. A tausashe ta ce "Dada me za'a d'ora kuma?" Cikin bagararwa Dadan ta ce "Kashe kawai." Domin bata sakar mata fuska a dalilin tana taya autarta Maryo fishin cin mutuncin da suke k'irarin ta yi mata da ta je wajenta takanas. Ta fito da garwashin. Ta kashe sannan ta yayyafa ruwa a murhun ta kashe shi gabad'aya. Ta dawo ta zauna. Sannu a hankali Tijjani ya fara dawowa cikin nutsuwarsa. Gumin da yake yi, ya fara tsane wa. Mintina kad'an ya mik'e ya ce "Zan tafi. Babah yaushe zaki koma?" Da mamaki ta ce "Tukunna." Da hanzari ta fice yana fad'in ",Na tafi Dada". Bai ko bi takan Nasiba ba, bare ya yi mata sallama. Babah ta kasa gane al'amarin domin tamkar mai jinnu haka yake canjawa. Ta hakura ta kudiri aniyar tsananta addu'a domin ta yi imanin Ubangiji ba zai juyar da addu'ar ta ba. Sannu a hankali kwanaki suna ta shude wa har ya zama saura kwanaki goma auren da ake ta cece kuce a kansa. Lefe ne kawai ba a kai ba, an yanke shawarar idan ta je gidansa ya bata domin zuciyoyi sun kai kololuwa wajen fusata. * Da safe bayan ya tafi da yara makaranta, shi kuma ya wuce Dass. Ina zaune a falo ni kad'ai, kuka kawai nake yi, irin kukan nan da yake zuwa ko da baka so ba. Gabad'aya duniyar ta mini zafi. Idan na tuna saura kwanaki 'kalilan na fara raba Bulkachuwa da Nasiba sai na ji ina fatan mutuwa ta dauke ni kawai. Na kifa kai a hannun kujera ina kuka tamkar mai wake, domin bilhakki na Bude baki nake yi. Ba zato waya ta hau kuwwa. Na mika hannu a dalilin Gwaggo kawai na saka taken da yake tashi. Sai da na yi jarumtar shanye kukan sannan na dauka. Murya ta kawai ta ji. Ta tausasa harshe ta ce "Kuka kike yi ne Yabi?" Haka kawai ta fad'a na rushe da kuka mai tsananin gaske. Cikin kuka sosai na ce "Gwoggo ba zan iya ba, zuciyata na mini ciwo, tana zafi mai radadi." Ta numfasa ta ce ",Zaki iya mana. Ai ba a kanki aka fara yin kishiya ba, ba kuma za'a kare a kanki ba". Da rawar murya na ce "Amma dai kishiya irin tawa Gwaggo zan zama cikin mutane kad'an da aka yiwa irin ta. Mena yiwa Tijjani da zai mini irin wannan cin mutuncin a rayuwata?" Da taushi sosai ta ce "Nutsu ki ji ni! Shawara zan ba ki, ba umarni ba, kinsan umarni wajibi ne ki mini biyayya. Ita kuwa shawara sai kin so za ki bi. Amma idan kika bi zai fi miki alheri fiye da barin." Ta nisa tare da ce wa "Duk runtsi kada ki ce mijinki ya sake ki matukar bai keta haddi da alfarmar shari'a ko ta aure ba. Sannan ki yi dukkan iyawar ki, kada ki nuna damuwa ko gazawarki a gaban mahaifin ki Yabi. Ya damu da halin da kike ciki. Ki daure, ba abin da ba zai wuce ba, sai ikon Allah". Na yi shiru illah kukan da nake yi mata tamkar zan shid'e. Cikin jarumta ainun ta ce "Allah ya sassauta miki, ba komai kin ji. To ban da ma kin saka damuwa a ranki ai bai kamata al'amarin duniya ya susuta ki irin haka ba Yabi. Kinsan kalubalen da yake gaban ki kuwa? Kwanciyar kabari kad'ai da muna saka ta a gabanmu da bamu bari kalubalen duniya ya kidima mu ya shagaltar da mu yiwa kanmu tanadin kwanciyar da Ubangiji kad'ai yasan adadin tsayin ta ba. Me yasa kishi ya ke sawa mu manta Annabi ya ce mu yawaita sadaka, sallah da istigifari. Domin ya hango mataye da yawa yan'wuta ne. Kuma tsananta kishi alamu ne, na mace ta barranta kanta daga ayar da Ubangiji ya saukar. Wacce kuwa ta barranta daga imani da ayar Allah. La budda tana cikin hatsarin kafirta matukar bata gaggauta tuba tare da yin hak'uri cikin hukuncin da Ubangiji ya halasta ba." Tsikar jikina ta zuba k'warai da gaske. Na sassauta kukan da nake yi. Ta sake sassauta wa ta ce "Ki yawaita karatun kura'ani domin karanta shi kad'ai yana wanke tsatsar zuciya. Ki yawaita sallah. Ki rungumi y'aya'nki da sana'ar ki. Miji kuwa kada ki zalunce shi, kada ki tauye shi, kada ki hana shi samun nutsuwa da ke ko a gidansa. Illah iyaka ki sassauta zazzafar soyayyar da zata saka ki halaka, ki

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161