Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ku, mussaman ke Yabi da tun shekarar da kika iso duniya ya shiga cikin tala jaurar duniya". Ta fa'da kuka na subuce mata. Jikina ya mutu murus a dalilin kalamanta, tunanina ya shiga canke canken akwai al'amarin da zai biyo bayan wannan jirwayen na Dada. Muna tafe da Nasiba duk uban maganar da take yi mini akan Bulkachuwa na kasa ce mata uffan. A dalilin zuciyata ta riga ta baci da yadda Dada ta ce wai tunda na iso duniya ubana ya fa'da cikin ibtila'i. Na sani ba yau ake fa'da ba, Mama ta sha fa'da mini ni din tauraruwa mai wutsiya ce, haka ma ya'yanta su Yaya Indo. Tun ina damuwa har na zo abin ya daina damuna, domin Baban Marina bai ta'ba yi mini wannan izgilancin ba. Amma a yau sai na tsinci kaina da jin ciwon furucin Dada kwarai da aniya. Na dinga hasashen me ya janye mini alfarmar da na a samu y'an watannin nan a idonta? A daren ranar Babanmu ya zaunar da ni da matansa ya fa'da mana aurena da Alhaji ba zai yiwu ba, bisa wani dalili da bai bayyana mana shi ba. Ya je shi da Alhaji Tanimu sun bashi ha'kuri. Ya gamsu sun yi masalaha, duk da ya shiga rud'ani sosai. Ya kuma ce ya yafe duk hidimar da ya yi. Jikina ya mutu, zuciyata ta tsinke. Na kasa bu'de baki na yi magana. Ya sallami matansa suka bar ni da shi. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S* Ya tausasa harshe har ya bani tausayi. Ya ce "Yabi kinsan Nura dan wajen Babanku Tanimu?" Na daga kai tabbacin eh. Ya numfasa ya ce "Madallah! To zai zo ku gaisa, shi na za'ba miki ya zame miki miji. Ubansa tuni yake ro'kon na ba shi ke ya bawa Nura, tunda ya samu labarin abin da y'anuwana suka yi mini, ina ta bagarar da maganar. Saboda ganin Alhaji ya shigo da k'arfinsa. Amma a yau din nan na amince masa. Ina ro'kon arziki Yabi, kada ki kunyata ni. Kinga shi namiji ma ubansa yana fa'da masa ya amince da farin-ciki da walwala. Ki kwantar da hankalinki irin k'alubalen da kike fuskanta da kananun shekarunki na alamta cewa zaki samu kyakkawar rayuwa a gaba". Hawaye taf a idona na ce "Na amince Baba! Allah ya sa hakan shine mafi alheri". Ya amsa da ameen ikin farin-ciki mai yawa, tare da sanya mini albarka. Ya sallame ni bakinsa dauke da addu'a a kaina da lamarina. Ina shiga d'akin Gwaggo na fashe da kuka. Ta ru'ko ni sosai ta dinga bani ha'kuri. Wannan rarrashi da Gwaggo ta yi mini ya sanyayya mini zugin da nake ji a zuciyata. Da na nutsu sai na fahimci ba kukan rabuwa da Kwamshina nake yi ba. Domin ba wani sonsa nake ba, dama na yarda zan aure shi ne, dan na gaji da zaman Gidanmu. Sannan Bulkachuwa ya kitsa mini cewar da na yi kukan takaici a gidan babu, gara na yi a gidan wadata. Amma sam babu soyayyar da zan yi ba'kin ciki irin haka. Kawai ina kukan yadda al'amarina ya banbanta da na kowacce y'a a gidanmu ne. Maganganun Gwaggo sun sake fahimtar da ni ita dama ba son aurena da Alhaji take yi ba, ta yi shiru ne dan gara aurensa akan na Jabir. Amma ta ce bata fasa addu'a ba, bata fasa nema mini zabin Allah ba. Dan hakan kuma ya kasance sai ta gamsu Ubangiji ne ya amsa mata. Kwanki biyu na warware tamkar komai bai faru ba, na cigaba da harkokina. A yammacin wannan rana ta litinin mun taso daga Islamiya sai ga aike wai ana sallamah da Yabi in ji Nuru Tanim. Na dan diririce na kasa magana a dalilin yadda ya zamanantar da sunan na shi. Na dinga canki canki wane ne Nura a y'ay'an, Baba Tanimu? Domin y'ay'an gidan yawa ne da su, matasa sun kai bakwai ko wanne ya isa aure. Na kasa cankar wane ne shi a cikin jerin matasan gidan. Inna da kanta ta cewa yaron ya je ya ce "ina zuwa". Hijabina har kasa na sanya, bayan Gwaggo ta matsa mini na shafa hoda. Na fita cikin zullumin yadda zan gan shi. Tunda bani da sauran za'bi akan lamarin. A babban zauren na hango shi sanye cikin shudiyar shadda sosai, kansa sanye da hular da ta dace da kwalliyarsa. Ko ka'dan ba shi da makusa, ya fi Yaya J cika, tsayi ne dai zasu yi taya. Batki ne sosai, amma ma'abocin tsabta ne daga ga ni. Take na ji abin da ya d'aure mini kirji ya fa'da mini domin ban ganshi a cikin mummunan yanayi ba. Baya aikin gwamnati, amma yana koyar wa a wata firame mai zaman kanta, boobies a sannan yana da shagon caji da turin wakoki ko finafinai a wayar hannu. Muka gaisa cikin yanayi na babu yabo, babu fallasa. Muka yi shiru. Tsawon lokaci kafin ya katse shirun ya ce "Asiya! Zuciyata ta harba domin har cikin raina nafi son a ha'da mini da Yabi. Na amsa a hankali da "Na'am". Ya tausasa murya ya ce "Na da'de ina son ki, na sha fa'da wa Babanmu ya taimake ni ya nema mini auren ki, sai ya bada hanzarin dan-uwanki ne yake son ki, ba zai yiwu ya gabatar da maganata ba, tunda akwai nauyi a tsakaninsa da Baban nan gidan. Dan haka ko da kika gan ni anan ba turo ni aka yi akan dole ko biyayya ba, dama ina son ki tun ina zuwa makarantarku". Na yi kasa da kaina ina sake samun nutsuwa mai yawa. Ya sake sassauta wa ya ce "Idan har kina da matsala ko kina ganin ban yi dai-dai da ra'ayinki ba, zan san yadda zan yi na zulle wa maganar ba tare da an ga laifinki ba, domin al'amarin aure ba k'aramar tafiya ba ce da za'a yi ha'kurin dole a cikinsa." Na tsinci kaina da cewa "Babu damuwa Allah ya tabbatar mana da alheri". Dadi ya kama shi, ya ce" kenan Asiya ta aminta da ni?" Murya babu amo na ce "Yabi bata da burin yin fatali da burin iyayenta ko da ya ci karo da nata ra'ayin." Farin ciki ya sake lullube shi. Ya dinga fa'din ma sha Allah! Madallah da Yabi". Na taya shi murmushi. Ya ce "da alama kina son Yabi, ni kuma sai nake ganin karamci ne na kira ki da Asiya." Na cuna baki na ce "Tunda na riga na sami wannan falalar ta zuwa gabas, kawai ka kira ni Yabi domin ina son sunan da dukkan zuciyata". Ya murmusa ya ce

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161